-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tallafin Noma: Kungiyar Barau Initiative for Agricultural Revolution in Northwest, Nigeria (BIARN) tare da Hadin Gwiwar Bank of Agriculture Sun Buɗe Shafin Cike Tallafin Noma

Kungiyar Barau Initiative for Agricultural Revolution in Northwest, Nigeria (BIARN) tare da hadin gwiwar Bank of Agriculture, karkashin Sen. Barau Jibrin Foundation, suna bayar da dama ga matasa da manoma masu matsakaicin shekaru su nemi tallafin har zuwa Naira miliyan 5. Wannan shiri yana tallafawa manoma 558 da ke jihohin Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto, da Zamfara ta hanyar samar da kuɗi, shawarwari, da jagoranci a kowanne mataki.  

 Sharuɗɗan Nema  

Domin samun wannan tallafi, dole ne mai nema ya cika waɗannan sharuɗɗa:  

📌 Ya kasance ɗan Najeriya daga ɗaya daga cikin jihohin da aka ambata.  

📌 Ya kai aƙalla shekaru 20 da haihuwa.  

📌 Ya mallaki fili na noma mai girman hekta 1 zuwa 5.  

📌 Ya kammala hidimar NYSC tare da shaidar sallama.  

 Takardun da ake Bukata  

Masu nema za su aika da waɗannan takardu:  

📌 CV (Tarihin Aiki da Karatu)  

📌 Takardar Haihuwa ko Rantsuwar Haihuwa  

📌 Takardun Karatu  

📌 Shaidar Kammala ko Watsi da NYSC  

📌 Takardar Shaida ta Indigene na Ƙaramar Hukuma  

📌 Katin Shaida na Kasa (National ID)  

📌 Takardar Alkawari da hannu mai nema  

Yadda Zaku Cike 

Domin cike wannan damar latsa shafin yanar gizo gizo dake a kasa 

Latsa: https://biarn.com.ng/register

Masu sha’awa su gaggauta nema domin cin moriyar wannan dama!

0 Response to "Tallafin Noma: Kungiyar Barau Initiative for Agricultural Revolution in Northwest, Nigeria (BIARN) tare da Hadin Gwiwar Bank of Agriculture Sun Buɗe Shafin Cike Tallafin Noma "

Post a Comment