![Zakakan kalaman soyayya Zakakan kalaman soyayya](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgjDE1B2aHAqGqi7JPv6yB3KpFlDkizO8eQ6aWWFZbNcrHOwoD4vCIelorO2m6MDLpthcn8v-ny9HbHdRmiWCkcLsArzNvDz5CjCcLBwzvqFjcBuIbvPgzGoRqXUSzBrtDrfXE8KpG_Jgka3rh2_v2-vbFQIHVN6r_EM7I6JWHSgx5vCgnID-MTWOC5m7A/s16000/1000345591.jpg)
Zakakan kalaman soyayya
Zakakan kalaman soyayya
Ya masoyiyata tabbas na samu tazara ga Dukkan manemanki dake son suga sun kulla alaka dake sannnan inason in sheda miki cewa kaunarki a raina babu irinta a fadin duniya. Lalle Allah sarkin har abada ne tunda ya hadani da mace mai kyawon halayya irinki haka kuma nayi babban dace tare da samun Sa'ar rayuwa yayin da nake tuna cewa akwai soyayyata acikin zuciyar mace mai fara'a irinki. Banda wani motsi da nake acikin jikina bayan motsin tunanin ki. Tabbas banda wata diya mace acikin wannan nahiyar duniya da nake kulawa inba keba kasancewar duk lokacin da mutane ke son susan wacece ainihin wacce ta kama zuciyata da nayi musu bayanin ki zakaga alumma na yabon ki da irin kyawawan halayayenki da kike dasu hakan yasa nake tunanin cewa gabaki daya kaf acikin garin namu babu namijin da yayi dace kamata. Babu karya babu yaudara da maida hankali akan soyayyar ki domin soyayya tare dake ba karamin ci gabane ba domin duk inda zan isa na bayyana ki a matsayin wacce nake tare da ita Kowa zaiyi amanna dake. Banyi gaugawar furta miki kalmar so ba duk da cewa abokaina Sun bani shawarar kada inyi gaggawar nuna miki soyayya ta amma kash sai nayi watsi da shawarar su kasancewar idan ban riga na bayyana miki soyayya ta ba to bazan samu sukuni ba. Na samu kwanciyar hankali tun ranar da na samu kaina acikin sanyi mai launin kore tare da sanyin korama zuwa gareki yake sahibata. Babu komai yayin da nake samun damuwa sabida idan na tuna inada ke acikin zuciyata babu wani bacin rai da nake dashi a rayuwata. Al'umma sai fatan alheri suke min tare da tayani murna irin yadda na samu mace mai kyakkyawan fuska da lafazi mai dadi irinki. Babu wata Sa'ar rayuwa da mutum zai samu kansa aciki irin samun irinki domin na riga nayi matsaya da irin dabi'unki da kike tare dasu. Babu mutumin da bai ganni yayimin murna da samunki ba kuma babbban burina ki aminta dani domin in turo magabata na suyimin maganar aurenki hakan zai sa idan na zauna in samu nutsuwa domin ita nutsuwa itace cikon duk wani hankali da dan adam yake dashi. Lalle na tabbatar da koda kaddara ta samu galaba akaina ko akanki na rabuwar mu ina mai shaida miki cewa lalle wallahi bamu rabu ba tunda soyayyarki ta kamma jinina yabi ta fata ya kwashe dukkan sassan launin jikin ya afka acikin kayan ciki tun daga makogoro zuwa huhu hadi da hanta tare da koda ta hagu da dama sannan ta rikide ta garwaye a tare da jinin jiki kuma suna yimin amfani acikin jiki kinga koda kaddararmu ta riga da ta jira fata dole ni in neme ki Sabida na tabbatar da rayuwata da taki rayuwan tare suke tafiya haka zalika kema duk irin kamun da soyayyar ki da tayimin kema ta kama ki kamar haka har ma mutane na tunanin cewa soyayya ta acikin jikin ki tafi tasiri fiye da tau wannan dalilin yasa ban tunanin ko yaushe kiyi tunanin akwai abinda zai iya rabani dake koda na minti daya sabida na san idan ke yar halak ce kuma jinin jikin naki yana bi ta jikiin dole zaki tadda hankalim ki idan har kika ga an furta kalmar rabani dake. Banyi kasa a guiwa ba lokacin da wani taubashi na ya gayamin cewa gaki can bakida lafiya kuma rai a hannun Allah nan take nayi gaugawar shiga ban daki domin inyi wanka bayan na kammala wanka ina fitowa na saka tawul na goge jikina na shafa ma jikina mai na dauko kaya na irin wadanda suka fi kowane kaya kyau acikin akwati na saka na fesa turare nan take na nufi wajen sayen kayan makulashe domin yin tsaraba ta maras lafiya koda na isa gidanku sai naji kyakkyawan muryarki ta tarbeni tun daga nan na tabbatar da cewa wannan yaron taubashin nawa ya gayamin zance karya kawai yanaso ya latsa ni ne.
Ina Son in shaida miki cewa soyayayr da nake miki tamkar Dankali ne wanda aka dasa acikin fadama wadda tafi kowace Ni'ima ya samu yin yado to komai yawan wannan yadon dankalin bai kai yawan wannan soyayyar da nake miki da yadda ya haifafa acikin birnin zuciyata ba. Babu shakka a kullum banda wata damuwa acikin zuciyata duk na tuna cewa ke kadaice wadda ke tsayi acikin zuciyata a koda yaushe ba lalle bane kowane namiji ya samu karbuwa gareki amma ni da kaina sai gashi rana guda dare guda na samu amincewar ki ta fannin soyayya ta amana dakuma kauna. Duk wani masoyi karyar soyayya yake idan har gani gaki a fannin soyayya na kasa samun lokacin da zan iya baki sabida babu daren da babu tadda hankali na a gareshi. Nayi ta samame in nemi mace wadda koda babu ke zata iya kasancewa a madadinki amma kamar ba nema nikai ba sabida nayi ta yawo tun daga abuja yobe pataskum burkina ghana mali itofiya sokoto kebbi zamfara kalgo mali illele tureta wasagu riba zuru dirin daji tadurga maga mahuta koko besse maiyama yauri jega gwandu dadai sauransu babu inda ban zagaya lungu da sako amma na kasa samu tun daga wannan ranar na kawo miki saffa nake kuma kara mutunta ki a rayuwa domin ba'a samu mace irinki ba tun farkon duniya har yanzu da take batun shudewa kowa ya barta. Labari ya zomin da cewa tun ranar da aka haife ki kina sauka duniya tun daga wannan ranar gidanku suka fara samun karbuwa ga dukkan mutanen duniya kasancewa sun samu mace wadda babu kamarta acikin dangi da yan uwa duba da haka yasa ko kaifi kikayi acikin gidanku babu wanda zaiyi saurin yanke miki hukunci sai ya binciki yadda wannan lamarin yake duba da yadda kika samu kulawa acikin gidanku. Nayi imani da babu wata kaddara wadda zata zo da rana tsaka tayimin awon gaba da soyayya ta dake. Ga baki dayan samarin garinmu nayima kowa ritaya a soyayyar ki ya kamata ki sani murmushinki sakani murmushi yake sannan dariyarki sakani dariya take duk wani gurbi dake cikin zuciyata ya riga da ya garwaye da soyayyar ki acikin jikina da kuma dukkanin ruhina. Lalle soyayyar ki ta riga ta sarkeni banida wani buri face ki tausaya ki agazamin ko na furta so a gareki na tabbata ba mai iya jamin layi sabida kullun a shirye nake da in sameki muyi tattaunawa ta musamman don raya soyayyar mu. Ni a kullum banda wani buri illa in sameki kina rereamin wakar soyayya tunda ina ganin wasu nayi kuma abin yana damuna.
Ya kamata idan ina ciwo koda likita ya kasa gano matsala ta idan aka zo aka kiraki zaki iya magance wannan matsalar. Lalle soyayyar ki ta riga tayimin illa kuma ki gyara zan baki labarin soyayya amma sai nayi gyaran murya sabida ke kadaice mai iya take kaunar kowa ki sakamin taki acikin zuciya babu ranar da zan daina sonki kuma kada kiyi zaton a kiraki asibiti gameda halin da na shiga gameda soyayyar ki ya ke aniniyar raya karkarar zuciyata. Na matsu in samu rana guda in rike soyayyar ki domin kada tayi dameji. Lalle kowane namiji baida wani muradi face yasamu kasancewa da mace irinki acikin jikinai. Na zamo mutum wanda ya kamata a tausaya ma duba da yadda nake ta fadi tashi a kullun game da soyayyar dake damuna kullun acikin jikina kuma babu wacce ta jamin wannan sai irin soyayyar ki da na saka acikin zuciyata. Tabbas a kullum bayan nayi askar banda wani lafazi da ba lafazinki ba ya ke sahibata. Lalle garwashin soyayyar ki na riga na taka shi kuma banda wata maslaha face in kara samun salama ta hanyar kara samun kulawa daga gareki domin kulawar ki da kara amintar da soyayyar mu yana kara tasiri a zuciyata. Fannin soyayya da amana tare da kauna na tabbatar da duk cikin matan dake huldar soyayya acikin wannan nahiyar duniya da wuya asamu kamar ki. Lalle koda ni dake wanin mu ya mutu to tabbas inada tabbaccin soyayyar mu bata kawo karshe ba sabida kin riga kin shiga cikin birnin zuciyata kin cakude da jini na kuma tsokar dake dauke da fata ta riga ta kwashe jinin tayima gangar jiki baraza kuma ko yaushe wanda ke duniya tsakanin ni dake duk wanda ke raye zuciyarsa dole zata fara yimasa sake sake na cewa nan bada jimawa ba lalle masiyinsa zai dawo gareshi domin suci gaba da soyayya tunda tun farkon abin jini da fatarmu sun riga sun garwaye a wuri daya kuma kowane na tasiri acikin jikin junanmu babu shakka na yadda da kukawar da kike bani dare da rana wadda babu irin macen dake iya bani ita shiyasa duk matan da nafara muamala dasu babu wacce nafi son mutuntawa irinki duba da yadda na sameki acikin sauki kuma an tabbatar min da cewa soyayya tsakanina dake babu ranar da zata tsaya don numfashin mu a tare yake tafiya tun daga farkon fitowar rana har ranar ta fadi duhun magariba ya shigo ya bayyana a bainal nasi
0 Response to "Zakakan kalaman soyayya"
Post a Comment