-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Zafafan Sakonnin Soyayya

Zafafan Sakonnin Soyayya

Zafafan Sakonnin Soyayya 



Assalamu alaiki ya sayyada ta na saka takalman dake dauke da soyayyar ki Kuma na fara Tafiya a kan wadannan takalman masu dauke da soyayyar ki Domin zuwa birnin soyayyar ki. Ke lilo lilo Dan mazarina lilo na Allah lilo na annabi ke yarinya Dan mazarina shin wa kike so shin wa kike jiran aure bayan ni. Shiga birnin zuciyar ki dole ne a gareni Domin bakida tamka ko da misali acikin zuciyata kin shiga cikin jijiyar wuyana tare da afkawa cikin rijiyar zuciyata Kuma kin yashe dukkanin wata cuta tare da Wasu abubuwan dake haka so yaduwa acikin zuciyata. Banda lamarin da na saka a gabana yanzu illa in ganki acikin hali na walwala Domin banida wata fargaba acikin rayuwata kamar in ganki acikin mawuyacin hali. Kin buga jaridun da baza a Samu wani Dan Mutum mai iya karancesu ba acikin labarin soyayyar Mu. Kin zama hako Wanda babu manomin da zai iya shirya saka masa taki Domin ya Nome shi girbi soyayyar ki Kuma shi ci ribar wannan noman soyayya da yayi inaa hakan karya ne bazai taba yuyuwa ba Domin na tabbatar da cewa duk inda Dan riko shike ya Riga ya San kifi nai a kowane gida bazai taba yuyuwa Dan agola shi hi Dan masu gida ba. Na Gina rijiya mai dauke da gaba Dubu Dari da Hamsin da biyar Domin kafa wata gasa ta dalilin soyayyar ki Kuma wannan gasar babu Wanda zai fara gwada shiga wannan rijiyar face ni Kuma inada tabbacin duk Wanda zai iya gwada shiga acikin wannan rijiyar ya zama wajibi shi kwana da shiri ya tabbatar da koda ya isa ciki to bazai iya maida kanshi waje ba Ma'ana idan ya kuskura ya afka acikin wannan rijiyar to fa ya Riga ya tabbata acikin wannan rijiyar kenan saidai ajalinsa ya cimmasa aciki. Ina mai kara tabbatar miki da cewa duk yadda matsalar rayuwa yakai matsala bazan iya dakatar da cin kowace gasa idan Har ta shafe ki ba.


To kinga na daina sonki tun randa kikace bakisona ke kika rurasheni komai zanyi in kare dukkan mutuncina. Ni na Sani Wanda duk yake sonki bazai so ki tamkar yadda na so ki ba gaskiya bazan bari so yakai ni Garin da bazan iya jure zama ba Kuma na tabbatar da cewa ko tanbaya aka yimin miyasa nake sonki babu yadda za'ayi in bada wannan amsar sabida na San soyayya wata Abuce mai dauke da ba zata Wanda Kawaye kai zata iya riskar ka ba tare da ka shirya ba. So wani aljali ne Wanda idan ya tashi shiga jikin ka zai zoma da waibuwa kala kala. Soyayya wata alkali ce wadda idan ta tashi yimaka hukunci bata Tausayin halin da zaka shiga. Ashe Wanda zuciya take so wata rana ba shine takeso ba. Akanki na jure zama cikin zafi na jure sanyi na jure rani Kuma gashi na jure zagi akanki ban taba nuna wata damuwa ba. Kiran wayarki Har sau goma nayi ta kirarki ko daya baki daga ba Kuma ban nuna fushina ba duk da na San cewa soyayya da Kuma rai ajizi ne. Ashe so Yanada dadi idan akwai abokin kauna na kwarai Kuma na hakika Domin yanzu sai gashi kin dawo gareni to kisa a aranki idan Har ni zan baki soyayata bazan kara wannan ganganci ba Domin nayi na farin nayi Dan auta Kuma banji dadi ba wannan dalilin yasa yanzu jinina ya Riga da ya haye. To Ashe Ashe Wanda zuci take so bashi take so ba. Ki Duba dare da rana sai rakiyar so nake miki wata rana ko anason ganinki sai dai inyi ta bulayi acikin gari na sha fada da masoyan hakika akanki Kuma kinsan da komai Allah sarki idan Mutum na son ka bazai taba ganin laifinka koda a Rana Guda ba. Ke kika ce rakiyar son ki na daina ba za kimin uzuri ba kalar Wanda kike so ko hanyar su ban kamo ba. Lalle yanzu kin koya min Hankali Domin naga komai acikin yaudarar soyayya Kuma ta dalilin ki. Hakika na dauki babban darasi irin darasin da Bazan taba mantashi acikin rayuwata ba Har karshen rayuwata. Soyayyar ki ta ratsa jinin jikina tayimin wani kalar siddabaru Wanda idan ka saka idonka Acikin nawa zaka ce ni bama Mutum bane Duba da yadda soyayyar ki ta sakani acikin wani kalar mummunan yanayi Wanda duk Wanda ya kuskura ya afka acikinsa to saidai ayi masa addu'oin waraka don ya Riga ya zautu ya kama wata hanya ta daban wadda ko ya bita bai bullewa acikin rayuwa.

0 Response to "Zafafan Sakonnin Soyayya"

Post a Comment