-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Zafafan kalaman soyayya

Zafafan kalaman soyayya

Zafafan kalaman soyayya



Soyayyarki a zuciyata tamkar wata fitila ce wadda idan aka haskata babu wani launin da zai gushe haskenta a Sararin nahiyar duniya baki daya. Banda wani buri a rayuwata face inga kaina cikin taurarin dake cike da hasken soyayyar ki acikin kalbin ruhin zuciya Na Kasa samun lokaci isasshe wanda zan iya warewa babu dare babu rana ina bauta miki ta dalilin yadda soyayyar ki tayimin katutu acikin zuciyata na san maza kuma maza sun sanni ta dalilin soyayyar da nake miki garinmu ga baki daya kowa ya ganni zai kirani da majnun na laila sabida irin yadda muke gudanar da soyayyar mu tsakanina dake tamkar laila da majnun, jamila da Jamilu, sadiq da sadiqa, fatuhu da fatihat, romiyo da jiliyat. Naso ace zaki zama sabulu inzo muhadu in zama Soso domin muhada kawunan mu mu wanke duk wani datti mai kawoma soyayyar zuciyar masoya nakasu ta fannnin shiga da ficen yadda jini ke gudana a Zuciyar duk wasu masoya masu rayuwar soyayya a doron kasa.


Na kasa samun nutsuwa da sukuni a fannin yankin tukurin zuciyata kasancewar soyayyar ki tayimin dafifi tare da Rifce duk wani makwallaton makullin dinarin zuciyata mai dauke da soyayyyar ki. Bani ji bani gani idan na samu tashi a kullum idan safiya ta wayemin banda wani buri ko raayi wanda ya wuce insamu dogon lokaci muna hira da tadi na soyayyya tsakanina dake kuma hakan zai kara zama garkuwa tare da danne duk wata cutar soyayya dake mamaye zuciyata. Hakika nayi kewarki har kewar ta zama dalilin da yasa banda sukuni kuma dukkan lamurra na sun tsaya tsaf sun kasa isa ko ina domin zuciyata ta riga da ta dukufa wajen nuna soyayya ta dakuma kauna. Nayi nisa kuma nisan da bani jin kira ta dalilinki ya ke sahibata na kasa runtsawa idan dare yayi ba yadda zaayi insamu sukuni sabida koda yaushe mafarkin ki nake babu ma dare ba rana. Duk safiya ta waye hakika hankali na bazai taba kwanciya ba sai naji kyakkyawan muryarki mai kama da suga ta fannin zaki. Lalle nayi sa'a tunda na riga na sauke farashin duk wasu maza a fannin soyayyar ki. Duk yadda zanyi bayanin yadda soyayyar ki ta cika gurbin zuciyata ba wanda zai fahimci yarena sabida babu wanda yasan illar da soyayya ke yima ruhin mutum sai wanda ya karanci littafin So mai dauke da launin kauna da kulawa. Duk da cewa soyayyya akwai dadi kuma tana rikita tunanin duk wani mai yinta amma soyayyar ki ke ta daban ce mai dauke da makamaahi da kibiyar ajali wannan dalilin da yasa a koda yaushe soyayyyar ki ke tayimin barazana acikin birnin makwallaton zuciyata ya ke sarauniya wadda idan ta shigo fadar ta babu wani bafaden da bai kawo saffa agareta. 


Duk jijiyoyin jikina dake dauke da jinin dake zagayawa acikin jikina idan aka fasa su dole launin soyayyyar ki zai bayyyana acikin wannan jinin. Kizo ki zauna dani kada ki mance dani ki tausayamin don Allah ki tausaya kiyimin uzuri sannan idan har wani kafi kikamin na wani siddabaru na kasa samun sukuni ina rokon arziki a Wurinki Da kiyi gaggawar yin azama ki cire wannna sihirin domin insamu salama acikin zuciyata Duk wata gyada tanada gardi amma kash ba yadda za'ayi wannan gardin ayi misali dashi da irin matukar soyayyar da nake miki, Duk Wata Kofa an tanadar mata Kwado wanda keda ingancin da ba wani barawo da zai iya fasata ya shiga cikin domin daukar wani abu ko fita da wani abu mai Muhimmanci ba amma Kwadon dake Kulle Da Zuciyata yafi na kowace kofa inganci sabida yadda na kulle soyayyar ki acikin zuciyata kamar babban Bankin duniya ne inda kudaden manyan kasashe ke sauka tun daga saudi arabia, Ingila Brazil Australia Birkinafaso Ghana Itopia, mali, Chadi Zimbabwe, turkey brazil Germany, indonissia Da dai sauran kasashe na duniya baki daya.


Babu Wani Ganwo da bazan iya hadawa in dora a saman kaina ba domin dakon soyayyar ki. Soyayyar ki acikin jikina a kullum sai ta shiga jinina ta baiwa kassa su kuma kassan subaiwa tsoka ita kuma tsokar ta baiwa fata sannan ita fatar ta kwashi wannan soyayyar ta garwaye tare da jinin dake yawo acikin jiyojin jiki ya kwashe komi ta iza acikin Sassan jinkina ta zagaye zuciya ta baiwa huhu huhu shi baiwa hanta hanta ta baiwa kodar dama ta dama ta baiwa ta hagu hanji su kwasa su fidda abinda ba'a so a Soyayya sai su kawoshi inda Za'a Sauke shi a matsayin bayan gida Ko hakan lalle lafiyar soyayya zata kasance garau acikin jikina. Hakan kema a bangaren cikin jikin ki akwai wasu sassa da yawa dake amfani da nawa kullum kuma a lokaci daya domin zuciyata da taki tare suke bugawa a duk lokaci sannan huhun dake cikin Zuciyarki Tare Suke Jan iska kuma da sauke iska duk a lokaci guda kasancewar mun riga mun zama daya soyayyar juna ta riga da ta ratsamu sannan kuma hanjina da naki tare suke daukar abinci suna tacewa a tare kuma su assasa ban haya a matsayin bayan gida a tuce shi haka kuma kododin jikina tare Suke tace jinin jikina tare da naki a duk lokaci guda wannan dalilin yasa a koda yaushe tare muke shiga ban haya kuma tare muke shiga fitsari domin gangar jikin mu ta riga da tazama guda a fannin soyayya ta amana dakuma kauna sannann a koda yaushe fatana inga na kasance tare dake har karshen rayuwata daga nan har ranar da mai zuwa ya dawo har ranar juma'ar da batada Assabar, Har Ranar assabar dinda batada lahadi, Har Ranar lahadin da batada litinin, har ranar litinin da batada talata, har ranar talatar da batada larba, har ranar larbar da batada alhamis, har ranar alhamis dinda batada Juma'a to kinga kwatankwacin yadda soyayyar ki tayi tasiri acikin jikina ya ke sahibata aminiyar rayuwata lailatulkadaril kalbi na mai sanyaya zuciyata ta sakani farin ciki yake wadda zamu shige a tirakata a tare da ita.

0 Response to "Zafafan kalaman soyayya"

Post a Comment