![Wasikar Soyayya Mafi Kyau Da Kayatarwa Wasikar Soyayya Mafi Kyau Da Kayatarwa](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjoVnPNrUICWsQllvb9MSBYV1Nw5vf7nUI_dJUfpHi6HNV6-mphK3EbX3_J1Qqcidfh66I8qYfWCixL_PBjLMSZGc3LPiMpuZSxloa5YokpVLbwOLwiETqwSWfhCU6q-rDFVcdr26_y6ivXA9ZJ58lzmS5zZ3tu_PLQ8VkLg1HfgoQ9YlIowu7eZWf0lUc/s16000/1000279459.png)
Wasikar Soyayya Mafi Kyau Da Kayatarwa
Wasikar Soyayya Mafi Kyau Da Kayatarwa
Na sunkuya na bada sari na kuma bada dukkan wata kauna zuwa gareki ya sahibata banda wata hanya wadda zanbi in bulle har zuwa inda zan isa ba tare da na hadu da soyayyar ki ba a koda yaushe. Banda wata bida ko nema da nake dare da rana face neman soyayyar ki ta zama mallakina a koda yaushe. Nayi nuta acikin ruwa kuma nayi nutsewar da ban iya tasowa saida koramar birni da raya karkarar horinton rikon makosar bisakkin daren diron soyayyar ki. Duk baron da zan iya ja koda da kaya shike a cike idan ma kayan sun fi karfin daukata amma idan akwai soyayyar ki ko nauyin kayan nan banji a jikina. Wayyo ni kaunarki da soyayyar ki tayimin zoba kuma irin zobar nan dake shiga cikin kasa da bera ke yi daga wani gefe zuwa wani gefe na daban domin yasamu tsira. Nayi biryima na tusu na harabu na gittu duk kuma a dalilin soyayyar ki. Soyayya hakin cikin ruwa dabara zaman cikin wuta lamarin da ni nake yau ki tuna kullun kinada karbuwa a wurina Allah dai shi bamu lafiya. Soyayya idan da Sani kamar dai tafi karuwa amma tunda yan uwa muke kamar dai sunfi yaduwar jiki. Kin San rashin ganinki fitina ce gareni wadda babu makarar ta sai Lokaci ko ranar da mai zuwa ya dawo. Kin shahara a wajen iya wanka kin iya Kuma takon ki maganarki tamkar wata zinariya ce wadda za ta kasance ba sai an wanketa ba tun lokacin da aka fidda ita acikin ramin hakar zinari. Babu wani yado Wanda yafi yadon da soyayyar ki tayimin acikin zuciya ta Wanda babu yadda zanyi inyima Mutum bayani ko misalin shi saidai idan ka ganshi ya Bayyana a sansanin fuskar ka. Na Dade ina jiran wannan ranar ma'ana ranar da babu wani Mutum Wanda zai iya furta miki so da kauna face ni. Ni kadai ke son inyi ta furta miki Kalmar soyayya Domin idan bani ba babu Wanda zai gayyace ki Acikin zuciyar sa Kuma wannan soyayyar tayi armashi babu wuni bale rana Wanda zai zo ban kira sunanki ba sabida irin kaunar da nake miki babu dare babu rana a kullun yaumin Safiya rana dare hadda ma marece ya ke sahibata.
Duk wata soyayya da wani Mutum na miji zai nuna miki na tabbatar da dodon bango ce babu rikewa jabau acikinta Domin kuwa wannan soyayyar tanada nakasu Wanda koda matsalar soyayya aka Samu baza a iya kai karshen wannan matsalar ba dole sai wannan tsarin ya lalace Kuma babu makawa aciki sai Samun gibi acikin wannan kauna. Dole ne a tanadi likitocin da koda wata matsala ko ciwo ko Kuma miki acikin soyayya ya bayyana suyi sauri su kawo dauki yadda wannan soyayyar bazata Samu matsala ba. Nayi baccin dare koda na falka Kawai sai hazon kyakkyawan fuskarki ake yimin tare da kyalkyalin zinariyar fuskarki a kusa dani, Nayi bacci safe koda na falka sai Kuma hazon kyakkyawan fuskarki Kawai ake min a kusa dani Wanda ban taba ganin irinshi Acikin launin tunanina ba haka Kuma nayi mafalkin kece kika kwashe ni kika biyamin kudi na kujerar makka kika biyamin kudin gwadin da akema Mutum kika biyamin kudin kayan da ake sakawa na maniyyata Aikin hajji kika kwasheni Acikin jirgin sama sai gamu a Garin Jidda sai kika rikemin hannaye na muka isa Garin makka Domin gudanar da Aikin hajji Amma muka dawo masauki aka rabemu sabida wajen mata daban na maza daban wannan ya samo asali Ne ta dalilin yadda soyayya ki tayimin Yawa Acikin zuciyata ya ke habibiyata
0 Response to "Wasikar Soyayya Mafi Kyau Da Kayatarwa"
Post a Comment