
Shirin Youthrive na Access Bank: Tallafin Horo/Kudi Ga Matasa yan Kasuwa na Najeriya
Shirin Youthrive na Access Bank: Tallafin Horo/Kudi Ga Matasa yan Kasuwa na Najeriya
Ana kira ga matasan ‘yan kasuwa da kananan da matsakaitan masana’antu (MSMEs) da su shiga shirin Youthrive na Access Bank, wanda aka tsara domin karfafa gwiwa, bunkasa kasuwanci, da habaka basira. Wannan dama ce ta musamman don samun horo, tallafi na kudi, da kuma damar fitar kasuwanci zuwa ƙasashen waje.
Abubuwan da za ku amfana da su
1. Ƙarfafa basira da horo – Samu koyarwa kan dabarun kasuwanci, kirkire-kirkire, da fuskantar kalubale.
2. Shirin musayar kasuwanci – Manya-manyan ‘yan kasuwa za su sami tallafin tafiya zuwa Netherlands, China ko India don samun gogewa daga ƙasashen waje.
3. Tallafin kudi – Bayan kammala shirin, za a ba da damar samun rancen kudi har Naira biliyan 50 da kuma kyautar tallafi ga wadanda suka fi kokari.
4. Damar samun aiki – Wadanda suka halarci shirin za su sami dama ta samun aiki musamman a bangaren fasaha.
Karin fa’ida
- Jagorar masana a harkar kasuwanci.
- Rajistar kamfani ta CAC.
- Taimako wajen samun rijista da takardun SON da NAFDAC.
- Tallafi ga wadanda ke son fitar da kayayyakinsu kasashen waje.
Yadda Zaku Cike
Domin cike wannan damar latsa shafin yanar gizo gizo dake a kasa: https://youthrive.accessbankplc.com/
0 Response to "Shirin Youthrive na Access Bank: Tallafin Horo/Kudi Ga Matasa yan Kasuwa na Najeriya"
Post a Comment