![Masoya biyu - Kalaman Soyayya Masoya biyu - Kalaman Soyayya](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjT_nGIpMCSZtctZ8pXcMgsEQZPTmcuIltLaK_b2JC0-52jAcVg7yJVdJSN0l9m8xSK4k6QsEL_B3ipOLUvMJBwc5EdULnV417E0EGhuW7Ph2YvJSZPf2dipH1iy2ehcL7Jv3VmvTV18ASRy5s_Fq64cuPzhAQhzrgeQkGwAtrzWGClpZui6KPdx63zCc8/w640-h640/1000345590.jpg)
Masoya biyu - Kalaman Soyayya
Masoya biyu - Kalaman Soyayya
Assalamu alaiki ya ke hasken da idan ya fito alummar gari zasu haskaka a kowane lokaci na kanso in samu natsuwa domin soyayyarki idan tazoma bawa baida nutsuwa zata iya hadewa ta zame masa firgici kuma ya kasance cikin rashin samun sukuni duba da yadda nake ganin sauran samari da zarar sunyi arba dake sai ka samesu cikin wani yanayi ko hali na rudani tare da zaucewa, A Koda yaushe idan na samu labarin isowarki tun daga tashinki a gida har ki isa wajen da zakije Zaka ga samarin dake zaune acikin gari kowa ya tadda hankalin sa babu mai wani buri face ya Samu ganinki koda baisamu zantawa dakeba. Lalle babu wani mahalukin mutum wanda keda numfashi acikinsa da zai ganki baiji ya shiga wani yanayin tunanin yace ina ma ace ya samu lokacinki koda na minti biyu ne ya samu tsayuwar ki ke dashi a wuri daya koda zai samu sukuni acikin zuciyarsa Lalle Nayi sa'a ta rayuwa tunda na samu amincewar ki da kika aminta kiyi soyayya tare dani duba da irin kyakkyawan dabi'unki da kowane mutum yasamu irinki a matsayin masoyiyar sa tabbas yayi babban dace a rayuwa. Ban fiye son gaddama da musu ba A kullum idan aka tadda labarin mata masu kalar kyau dake rayuwa a fadin duniya zakiga na kawoki a sawun farko hakan yasa kowa zaiyi kokarin gaddama dani akan cewa bazai yuyu ace yanzu kece macce lamba ta farko wacce tafi kowace diya mace kyau ba a wannan nahiyar duniya.
Lalle na samu kaina a cikin kalubale ta dalilin samun mace dilleliya irinki acikin tsarana babu wani wanda ban fishi samun budurwa mai kyakkyawan launin fuska ba. Hakan yasa a koda yaushe kikayi yunkurin fita daga gidanku domin kai wata ziyara a wani wuri hankali na bazai taba kwanciya ba har sai kinje kin dawo inda zakije domin a kullum tunani na wani zaiyi kokarin salamawa acikin kokon zuciyar ki yazo da kokon baranshi zuwa gareki don amincema soyayyarki. Tabbas Duk kalar mata guda ce tun daga Kai idanu hanci baki kunne gashi hannun hagu da dama tare da yatsun su Cibiya hakori hamata kafafu da sauran wasu sassan jiki da mace ke dauke dasu a jikinta Amma kash Ke duk wanda Zai ganki bazai kula kowace diya mace ba duk da cewa duk abinda kike dashi suma sun mallake shi Lalle tabbas soyayya gamon jini ce kuma a kanki na kara tabbatar da haka irin yadda mutane suka zurfafa soyayyar su zuwa gareki har takai ga abin ya riga yaci tura takai ga yanzu idan mutum yanason ya ganki ya furta miki kalmar so to babu shakka wannan mutumin ya kai gwarzo kuma jarumi acikin kowane filin daga sabida furta miki so a bainar Juma'a ba karamin kuskure bane sabida yawan tarin masoyanki dake cikin wannan garin. Babu inda zanje in dawo acikin kowace majalisa banji ana ta yawan surutu akanki ba hakan yasa duk wanda ke son kulla alaka dake yana mugun taka tsantsan gudun kada wani masoyinki acikin tarin masoyanki yayi yunkurin hallaka shi domin kuwa a wannan zamani soyayya ta riga ta canza koda matan da basu kaiki kyau da gata tare da jan aji ba zaki ga mutane na naukar ma wasu mazaje mummunan matakai ta dalilin nuna ra'ayinsu ga matan da suke so ballantana ke dake dauke da siffar da Ko ina Za'a je a dawo baza a sami mace mai irin kyawon fuskar ki ba. An samu wani namiji yayi tattaki tun daga Taraba babban birnin jalingo Zuwa adamawa domin haduwa dake bai ganki a can ba sai ya tashi wani tattaki zuwa yola babbban birnin adamawa haka kuma bai ganki ba sai gashi yayi tattaki sai savanna babban wurin da kamfanin suga shike domin haduwa dake kuma kash bai sameki ba haka ya taso yayi tattaki daga savanna har balanga wata karamar hukuma acikin gombe, ya shiga garin balanga lungu ya sako domin haduwa dake amma hakan baisa ya dace ba haka ya taso ya shigo garin billire bai samu haduwa dake ba sai ga fadan kabilanci yana wakana acikin wannan garin amma bai karaya ba shi burinsa ina zai ganki ya saka ki a idonsa domin samun lokacin ki ya mika sakon soyayyar sa amma duk da haka bai ganki ba ana haka sai ya samu ragiyar hanya har kaltungo acikin wata karamar hukumar mulki ta gombe domin ya samu ganinki sai gashi bai dace ya ganki ba koda safiya ta wanye masa yana cikin babban masallacin Juma'a na garin nan ana tadda sallah ya tashi yabi jam'in sallah ya isa har cikin babbar jami'ar su koda zai dace da ganinki amma bai samu ganinki ba sai gashi yayi tattaki daga babban garin kaltungo har zuwa alkaleri karamar hukumar mulki ta bauchi domin ya samu ya ganki amma bai samu ganinki ba nan take bai jima ba sai ya nufi hanya yana shassheka tun daga alkaleri har garin bauchi koda ya iso garin bauchi ana sallar Juma'a nan take yayi alwala ya shige jam'in wannan sallar Juma'a ana gama sallah sai gashi layin masu waina an saka masa waina mai kyau tare da miya amma ya kasa cinyewa sabida hankalin sa ya riga ya karkata zuwa gareki nan take ya wanke hannunsa yasha ruwa ya nufi hanya sai gashi acikin garin misau amma dare yayi masa ya buga ya buga amma ya kasa samun wajen da zai laba a matsayin masaukin bako ai kuwa dole ya tunkari otel domin yasamu wajen da zai kwanta kuma duk wannan wahalat akan soyayyar ki yake ta yinta. Safiya na wanyewa sai gashi ya shiga gari yana neman ina zai ganki ya shiga lungu hadda sako makarantu da wurin wasa domin yaganki amma kash! Abin yaci tura nan dai ya hakura ya tunkari hanyar garin Jama'are domin neman ina zai ganki sai gashi ya kara yi wani tattaki sai garin kano Ya Kuma shiga yankin kano daban daban domin ya samu ya ganki da idonshi amma abin yaci tura kasancewar baisan indama zai dosa ba sabida ya riga ya zauce a soyayyar ki amma baisa ya karaya ba ya shiga ya fita acikin garin kano sai gashi ya tassuwa ya iso har garin kankara ya cigaba da nemanki
0 Response to "Masoya biyu - Kalaman Soyayya"
Post a Comment