-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Mafaraucin Soyayya

Mafaraucin Soyayya

Mafaraucin Soyayya 



Ba nan labarin mafaraucin soyayyarki ya tsaya wajen surkullen nemanki ba Nan take ya fara Nemanki acikin garin kankara wannan karamar hukumar mulki ta katsina amma bai samu mutum ko daya wanda yacce yanada labarinki ba Haka yaje gidan masarauta domin gabatar da kansa a wajen maigari ya kuma bayyanama maigari dalilin isowarshi acikin garin nashi sai maigarin yayi murmushi yayin da yaga haukar sonki ta bayyana ga wannan bawan Allah nan take dai maigarin ya hadashi da fadawanshi aka shiga cikin gari lungu da sako domin nemanki babbar matsala dake nan shi wannan bawan Allah mai neman soyayyar ki koda Hotonki ne baza a sameshi gareshi ba balle ayi amfani dashi domin a gane ki wannan dalilin ya kara tabbatar ma mutane cewa wannan mutunin ya riga da ya afka cikin rijiya mai gaba dubu ta soyayyar ki. Daga nan dai sarkin garin ya bashi gudumuwar guziri domin ya tashi daga wannan garin zuwa wani garin domin sun fahimci wannan bawan Allah ya zauce da irin soyayyar da yake miki nan take yasamu mota ta daukeshi sai acikin garin sheme daga sheme bai isa ko inaba sai cikin babbar kasuwar wannan garin na sheme wadda ke ci a duk ranar Juma'a a nan dai cikin kasuwar yasamu masauki amma duk da haka bai bar tambayar mutane gameda ke ba. Nan dai wannan bawan Allah yayi ta jira zuwa ranar kasuwa saida ranar kasuwa tazo kawai ya fara bincikar mutane daya bayan daya amma kowa bai bashi gamsassar amsa ba domin kuwa ko hotunanki babu tare dashi haka dai yafara ramma kanshi domin kowa mutane sun fara yimasa kallon mahaukaci a bainar nasi amma duk da haka bai dakata shiga garin lungu da sako domin nemanki ba nan dai magariba ta karasa masa alumma sai fita suke daga kasuwa haka dai ya koma a bakin babban garejin kasuwar duk mutumin da ya fito acikin kasuwa yana tambayar mutane ba'a Ganki ba domin ya riga ya samu tabin hankali ta dalilin saka ki a rayuwarsa da yayi kuma Allah ne kadai zai iya yaye masa wannan lalura.


Ba daga nan na tsaya ba kawai sai wannan masoyin naki yafara tunanin barin wannan garin komai dare, haka ya fito a bakin titi ya tari mota sai garin tsafe Shikenan ya fara shiga acikin garin yana nemanki ya buga nan ya buga can sai bugun daji yake akan soyayyar

 ki

0 Response to "Mafaraucin Soyayya"

Post a Comment