-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Labari Mai Dadi: Sanarwa Zuwa Ga Masu Neman Shiga Aikin 'Yan Sanda

Labari Mai Dadi: Sanarwa Zuwa Ga Masu Neman Shiga Aikin 'Yan Sanda

Labari Mai Dadi: Sanarwa Zuwa Ga Masu Neman Shiga Aikin 'Yan Sanda

Hukumar Kula da Aikin 'Yan Sanda ta Kasa (POLICE SERVICE COMMISSION) karkashin jagorancin DIG Hashimu Argungu (mai ritaya), tare da hadin gwiwar Rundunar 'Yan Sandan Najeriya karkashin jagorancin IGP Kayode, za su dauki sabbin kuratan 'yan sanda.  

Kamar yadda sanarwa ta zo, wannan karon babu batun cike takardun neman shiga aikin 'yan sanda saboda karancin lokaci. Za a dauki sabbin 'yan sanda ne daga cikin wadanda suka taba neman shiga aikin har suka rubuta jarabawar Computer-Based Test (CBT) a ranar 5 da 6 ga watan Maris, shekarar 2024, amma ba su samu nasarar samun aikin ba.  

A yanzu, ana bukatar su shiga cikin wannan gidan yanar gizo da za a bude zuwa nan da karfe 12:00 na ranar yau: https://apply.policerecruitment.gov.ng

Duk wanda ya ga sunansa sai ya buga (print) invitation slip domin halartar gwajin lafiya (medical screening) a asibitocin 'yan sanda (Police Hospitals) da ke hedikwatar runduna (Zonal Headquarters) guda 17 a fadin tarayyar Najeriya.  

Za a fara medical screening daga ranar 26-02-2025 sannan a kammala zuwa ranar 12-03-2025. Duk wanda bai samu damar zuwa ba, to ba zai samu damar shiga aikin ba.  

Ku taimaka wajen isar da wannan sako domin ya isa ga 'yan uwa, musamman mazauna yankunan karkara.  

Allah Ya ba wa mai rabo sa’a.

2 Responses to "Labari Mai Dadi: Sanarwa Zuwa Ga Masu Neman Shiga Aikin 'Yan Sanda"