
Kungiyar Yaki da Zazzabin Cizon Sauro (Malaria Consortium Nigeria) Ta Buɗe Shafin Daukar Sabbin Ma’aikatan Technical Assistants
Kungiyar Yaki da Zazzabin Cizon Sauro (Malaria Consortium Nigeria) Ta Buɗe Shafin Daukar Sabbin Ma’aikatan Technical Assistants
Kungiyar Malaria Consortium tana neman Technical Assistants domin tallafawa shirin rarraba ITN a wasu jahohi guda tara, ciki har da Abuja, Bauchi State, Borno State, Kebbi State, Kogi State, Nasarawa State, Oyo State, Plateau State, Sokoto State. Wannan aiki na wucin gadi ne kuma zai kunshi yin micro-planning da tantance ma'aikatan da za su gudanar da aikin SMC a shekarar 2025.
Masu sha’awar neman aikin dole su kasance da ilimi a fannin Kimiyya, Kimiyyar Zamantakewa ko Lafiya, tare da kwarewar aiki na akalla shekaru biyu. Dole ne su iya amfani da Kobo Collect, Survey CTO, da Microsoft Office.
Ana bukatar masu sha’awa su cike takardar neman aiki ta hanyar amfani da hanyoyin da aka bayar kafin 5 ga Maris, 2025. Don cikakken bayani da cike fom, danna:
Danna nan domin cike fom → [Bauchi, Borno & Abuja (FCT)]
Danna nan domin cike fom → [Kebbi, Kogi & Nasarawa]
Danna nan domin cike fom → [Oyo, Plateau & Sokoto]
Allah yasa mu dace baki daya
0 Response to "Kungiyar Yaki da Zazzabin Cizon Sauro (Malaria Consortium Nigeria) Ta Buɗe Shafin Daukar Sabbin Ma’aikatan Technical Assistants"
Post a Comment