![Kishin Kalaman Soyayya Kishin Kalaman Soyayya](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiZtTQoPiGBKWL-B0FmtUwpj30xj2MeEbFexBC11NMr4DMzc6sMU81n44vG7f44aMj6ap3VXYHSbJb7SKAf_LuAFGzuPb8b0BB7-UNWFhgAAGRw7lNkGcPdW-KA79otd_pGLgKMeXaIP8VNjlXqkHuC2RDaim9zJyysfajJEHlsDr8d0CHXtWENGP_mSc0/w640-h640/1000345590.jpg)
Kishin Kalaman Soyayya
Kishin Kalaman Soyayya
Na sallama miki da kokon baran soyayyata na riga na shirya baikon ki ya me sarauniyar tawa banda wani da nasani gameda ke nayi nisan da babu waiwaya acikin soyayyar ki. Ranki abin mararina ne akanki ban iya kwana ko ince miki bacci a hausar da kike fahimta yake maaoyiyata banda wani khaufi face khaufin rasaki akusa dani nayi kwaram nayi caraf nayi wagaz nayi cirindo nayi kwas nayi firit nayi madas nayi kushit nayi kakat nayi barat nayi dunayya nayi birimbit nayi kwatalwa nayi biyas nayi hore nayi biris duk akan soyayyar ki na kasa samun wani mataki wanda zan iya kai kaina acikin lokacin da duk soyayya ki ta mamaye zuciyata. Banyi wani tunani wanda nake iya rabuwa dakeba banida wani farce na susa da zan iya takaice soyayyar ki acikin wannan babban birnin zuciyata na kasa rike kaina domin duk yadda nake ganin jikina baida nauyi amma na kasa rike kaina domin ban iya rike soyayyar ki kuma in tauye kaina wajen nayi nauyin naman jikina domin kuwa ke soyayyar ki ta wuce ta kowace diya mace a fadin duniya ba yadda zaayi in hada dakon soyayyar ki da wani rikon gangar jikina domin soyayyar ki tafi mihimmanci fiye da gangar jikina ya kurratul ainin zuciyata. Nayi alwashin fadi tashi don neman yaddar ki ta fannin soyayya banda wani sukuni ko wata igiyar zato gameda soyayyarki zuwa ga wani mutum mahaluki don babu wata yadda da zan baiwa wani ta nuna kusanci tsakaninsa dake hatta na mintuna biyu sabida kishin dake dauke a zuciyata na soyayyar ki sabida kinsan duk wani namiji mai kishi akan abinda yake so hakika wannan shine cikakken namijin duniya mai hankali kuma mai riko da addinin Allah. Nayi ta rigima kuma na jima ina yinta ta dalilin inga na sameki kusa dani a koda yaushe domin hakan na kara sakamin kaimi tare da hazaka a bangaren soyayya ta dake. Bance zanfi kowa sonki acikin duniyar nan ba domin Allah da ya halicci kowace halitta yafi kowa son wannan halittar kuma kowa ya tabbatar da haka banda yakinin yanzu akwai wani mutum da zai hini sonki domin akan sonki na shirya shiga rijiyar da koda an cimma ruwanta babu yadda zakayi kaga waje koda zaka tadda kanka sau dari da tabanin da takwas koda kuma tsayinka zai kai tsawon kilo mita goma shabiyar da digo biyar bazaka cimma nisanta ba haka na tabbatar da cewa babu wani mutum mai iya jure wannan kasadar da nakeyi akanki ya ke masoyita mai raya dukkan kambun gurmamawa da nake samu ta dalilin soyayya ta dake da na jima ina gudanarwa akoda yaushe ya abar yabona.
Lalle nayi shirme tun lokacin da nasamu soyayyar ki ya kamata in shiga in fita domin neman zuma farar saka wanda zan tanadar miki a koda yaushe idan muka hadu in baki ki lasa domin karama soyayyarmu ni dake kwarin guiwa da kuma kara toshe wata hanya wadda za'a samu wani bara gurbi yasami damar isowa shiyi sallama akan ki domin neman yaddar soyayyar ki hakan yasa a koda yaushe nake tunanin nayi kuskure da na kasa daukar wannan babban matakin tun daga wuri domin gujema rashin mace kyakkyawa irinki don kece wacce ta cancanci akoda yaushe asaki acikin gaban mota kyakkyawan da babu kamarta. Na shirya afakama kowane korama komai zurfin ruwanta idan har zan samu soyayyar ki.
0 Response to "Kishin Kalaman Soyayya"
Post a Comment