-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman Soyayya Sahihai

Kalaman Soyayya Sahihai

Kalaman Soyayya Sahihai 



To bari kiji farkon zancena da karshensa duk akan soyayyarki lalle a kanki nasan wuyar so na san dalinsa duk akan soyayya. Lalle yau da gobe gonar Allah ba mai iyata sai shi kadai. Sabida haka ina bukatar kulawarki koda yaushe na tuna dake sai inji dadi kuma komai kikace nayi zuwa gareki kamin duk ki furta na riga na aikatashi babu babban abinda nake a wurinki face kibani zuciyarki gabaki daya domin kaunarki na cikin raina kuma bazan taba dainawa ba domin har abada mu kasance masu son juna da zama a jini daya lalle ni na san wuyar so kuma na san dadinsa ko taya zai juyamin. Lalle na gode Allah makagi na da yabani yar auta mai sharemin hawayena mai cikar muradina mai son ta mutuntani sannan tayimin alkawalin kasancewa tare. Kada kiyi tunanin akwai lokacin da zaizo in sauya miki domin kece cikon duk wasu mafalkaina sabida haka ga zuciyata nima zan karbi taki domin mu kasance a tare. Banida wani buri da tunani a koda yaushe face inga na kasance tare dake ya ke gimbiyata babu ranar da babu tunaninki kuma da mararinki acikin zuciyata sannan koyaushe sai zuba nake a zucci kuma a bayyane kuma duk akan soyayyar ki. Kinji kaunata lalle kaunar da nake miki acikin zuciyata har abada bazanyi tunanin zai iya dainawa ba domin duk yadda so yake da dadi to kauna ta wuce shi abinda zuciyata ta riko na soyayyar ki bakeson ki karba domin mu haskaka. Lalle idan babu ke na tabbatar da hanyar hallaka ta ce ta riga tazo ya sahibata aminiyar rayuwata cikon samun nutsuwa ta. Lalle nayo Sa'ar samunki a fannin soyayya domin kuwa samun macce mai irin dirinki zai yi wuya a sameshi sannan bakiyimin banna domin ke kadai nasan kina iya boye sirrina. Lalle ki kula dani idan har kina son in kasance acikin wannan duniyar kuma rashin kukawarki ba karamin kalubale bane acikin rayuwata. Lalle Na san nayi nisa a soyayyarki sabida kasancewar yadda nake magana ni kadai sannan tunanin nawa yazo ya canza ina ta abubuwa tamkar na dabbobi duk ta dalilin irin yadda soyayyar ki ta bugamin kai. Birni da karkara mazan gari sai yokuwa sukeyi a wajenki domin samun lokacinki koda na minti biyu ne Don su jaddada soyayyar su zuwa gareki akan haka nabi diddigin abin har naga cewa babu wani namiji yanzu mai iya tubkaroki da maganar so domin na riga na sanki ke gwanata ce koda a mafarki ban tunanin zaki iya cutar da soyayya ta da nike tsakanina dake sabida ke tauraruwa ce kuma tantabara uwar alkawari a fannin soyayyar dake tsakaninmu dake.


Lalle Wata ta yaudareni kuma ta rudeni ta zomin da wata fuska ta soyayya daga baya bayan na aminta da ita sai ta gujeni amma yanzu dani dake ban san akwai abinda zai iya zowa shi rabamu ba duk da rana ta gayamin akwai ranar rabuwa tsakaninmu dake amma hakan baisa na karaya ba sabida na san kawai yaudarar kaina zanyi idan har na biyema wannan yaye yayen shedan domin kullum sai kinzo a wajena domin mu gaisa kibani zuman so mai bala'in zaki kuma tun kina karama nake da tabbacin ke wacece a harkar so sabida nayi ta jarabaki kuma kinacin moriyar jarabawar shiyasa dani dake banyo zaton akwai rabuwa ba duk da so makahone bansan lokacin da ya shigoni kuma akwai mutanen dake gayamin wata rana zaki juya min amma na tabbatar da hakan ba gaskiya bane domin ke yar amana ce samunki shi yasa a koda yaushe sai nishadi nake ina ta samun nishadi. Farin cikina kece haske idaniya na kuma kalamanki a koda yaushe rudani sukeyi musamman idan kika kusantoni lalle ke kadai ke iya daurewa tare da jure halayyata. Gaskiya soyayya ta gaskiya akwai kwanciyar hankali gareta sai gashi gabaki daya na riga na danka miki duk yarda ta kuma banison ki juyamin a rayuwa idan kika juyamin ina mai tabbatar miki kin riga kin gama dani domin na tabbbatar da duk ranar da kika juyamin rayuwata batada sauran Muhimmanci sabida na tabbatar da rayuwar da zan shiga cikinta banda wani banbanci da mahaukaci wanda ke yawo a kasuwa ana tsokanar shi. Kin riga kin zame min wani bango acikin jikina wanda duk ranar da ya fadi na tabbatar da asirina ya tonu. Ke kadaice diya mace wacce zan iya kwashe jikinta in dorata akaina inje duk inda kike bukatar in kaiki ba tare da naji gajiya ba. Ke kadaice wadda zan iya kwashe jikinta domin in isa dake babbar birnin da masoya na gaskiya da amana ke gudanar da soyayyar su acikin nishadi tare da samun sukuni, Banji akwai wata diya mace dake iya jinginawa a jinana tun daga shidda na safe har zuwa shidda na yamma ba tare da na nuna gajiya ba amma idan kece koda kwana goma ne kike a jingine gareni babu yadda za'ayi in takura koda kuwa babu ci babu sha zan iya jure dukkan tsanani domin faranta miki rai yake masoyita.


Banjin kaina a matsayin mutum wanda keda sukuni matukar ban ganki a kusa daniba. Gangar jikina sai rayawa take yi a kullun sabida yawan tunaninki babu bishiryar dake iya sauke yayanta ba tare da nayi tunanin kece mai wannan yawan adadin diyan da ta zubar a kusa daniba. Duk ruwan dake sama zan iya jure tun farkon damanar ruwan nan har karshenta in tsaya a tsakiyar daji ruwan su kare akaina domin abani ke. Duk tsananin duhun dare zan iya jure tafiyar dake dauke da kilomita dari da hamsin da bakwai ba tare da ina ganin tafin hannuna ba har in isa wajen da zan sameki idan har zan samu amincewar ki don kibani soyayyarki. Zan iya Jure zafin wuta a ko ina take zan iya tunkarar ta domin samunki sannan duk gasar da za'a saka ta wani abu wanda yafi komai wuya ni zan iya tara kai in dauka domin cinye wannan gasar insamu Soyayyar ki ya ke masoyiyata. Ki kulamin ki rufamin in gode miki ki azamin ki rukamin mu tare farmaki sakar sonki ta riga ta sarkeni tausaya don Allah ki tausayamin idan har akwai ki bazan kula kowace diya mace ba domin na riga nayi miki shimfida acikin zuciya ta. Ina rokon Allah yabani jaruma kyakkyawa irinki mai farar zuciya da ba zata iya juyamin baya ba wadda komai cuta dake damuna da na riga da na ganki na warke. Lalle so bai jure rini kamar zanen zabo yake wanda idan ya bayyana dole yaudara ta kama kanta, kin riga kin san launukan sirri na naki kawai ya rage in ji ki rika soyayya ta mu rubanya ta muga yaya ribar zata kasance. Zo ki zauna dani domin ki zamemin magani Son ki shine dutsen fashin tama mai kauri zani furta miki shi kuma duk wuya duk rintsi domin idan na barki bazanyi rayuwa mai kyau ba lalle ke ka sona da gaskiya wadda bazan tadda hankali na akanki ba nidai nace sai ke kuma duk jawabin da za'a kawomin akanki na riga na yanke hukuncin kasancewa tare dake. Soyayyar ki acikin zuciyata tana sukana ya kamata ki dama fura ta soyayya domin ki saka suga na soyayya ki dama ta da luddayin soyayya ki saka acikin kwanon soyayya sai kibani acikin murmushi na soyayya tun ranar da na kalleki tun daga ranar nake sonki da baiko babu yadda zanyi in jure soyayyar ki matukar ina numfashi bazan boye miki ba kaunar ki ta riga ta tabamin hanta kuma ta mamaye dukkanin kayan cikina. Duk wani mutum dan halak ya ganki dole sai ya yaba kyakkyawan halayen ki na riga ni na aminta dake. Na Zaka zauna ki tuna tantabara kike sarkin kauna da alkawali bazan taba dakatar da zuciyata daga soyayyar ki ba koda an halbeni da bindiga babu yadda za'a yi na bari harsashe ya tunkari zuciyar dake dauke da soyayyar ki.

0 Response to "Kalaman Soyayya Sahihai"

Post a Comment