
Kalaman soyayya masu zaka kwalla
Kalaman soyayya masu zaka kwalla
Na tare kowane Gurbin dake dauke da soyayyar ki acikin awanni Guda Domin Samun kwanciyar Hankali na sabida zubewar koda kwarar azarar soyayyar ki acikin zuciyata ba karamar hasara bace a wurina. Babu kalar macen da ban ganiba amma Har yanzu na kasa Samun mace Guda acikin matan sararin duniya wadda keda annurin jiki Hadi da haiba irinki sannan duk inda za'a je kasa da kasa gari wa gari lungu da sako na kowane kasa a nahiyar majalisar dokokin duniya wadda zatayi launin kyakkyawar fuska irin taki Domin kin wuce ayi misali dake acikin kowane matan na wannan zamani
Zamani ya zo kuma har ya shude amma anyi bincike ba'a samu mace mai nagarta da siffa ta kamala kamarki ba duba da dabiunki masu bayyana kyakkyawan halayenki da tafiyarki da kasaitar ki tare da kaifin tunaninki a duniyar Mata. Ya zama wajibi in kara saka kaimi tare da yin azama inga na kasance lamba ta farko a birnin dake dauke da kasa jaha da karamar hukumar zuciyar ki ya ke budurwar da idan babuta a gari to babu kyawawan mata duk da cewa idan kika fito kowace mace bata son fitowa domin kyakkyawan fuskar ki da surar da Allah ya Bayyana a jikinki zai shude duk wani kyawon dake dauke ga kowace mace a nahiyar duniya.
Kin zama jidda ya zama wajibi in kasance a matsayin jamilu muhada mubada Jamilu jidda, lalle inajinki acikin raina domin ke kika hanani zubar kwalla kece muradina kece kuma zan baiwa kauna dare da rana inason ki kirani da sunan mijinki uban yayanki. Damuwarki tana dakatar da numfashi koda kince mini bakison kiga na fita a gida ya zama wajibi inason ki lura dani dake babu kalma ta rabuwa domin babu kalma a duniya mafi muni irin wadda zaace a rabani dake. Rashinki a gareni bakar kaddara ce da ba kowane musulmi ke iya imani da ita ba. Don Allah idan duk makiya sunyi miki yawa ni ki gabatar dasu zuwa gareni domin Nine ya kamata in jure duk wata adawa da kalubalen da zai tunkaro ki. Kin riga da kinyi rata ga duk wani namiji wanda bai iya taka rawar gani a fannin soyayya na lura kinason duk wani mai sonki amma ni soyyayar da kikemin ta banbanta da kowace soyayya. Zuciyata sai bugawa take a koda yaushe amma wannan dalilin baisa nayi kasa a guiwa wajen jawo soyayyarki in makkale acikin zuciyata ba saboda ke mace ce wadda idan mutum ya kasance a tare da ita babu shakka zai samu sukuni. Tabbas inajinki acikin raina farin cikina sai kara daduwa shike idan ina tunaki a rayuwata. Kece mace guda tilo dake mallake birnin zuciya ta wadda nake tunanin komai ruwa komai iska komai zafi komai sanyi duk runtsi duk wuya ko dadi zan iya mallaka miki amanar rayuwata.
Lalle Soyyarki na tayimin yawo a zuciya kuma a shirye nake da yakar duk wani mai sukar ki, juya ki rausaya ki takamin rawar soyayya domin a kowane lokaci na samu kaina idan na tunaki inji farin ciki. Lalle idan har yau da gobe sai Allah to ya zama wajibi in nemi samun yaddar ubangiji domin samun kasancewa a tare dake domin kece rabin raina yunkurin tunani na. Kada kiji komai ke tawa ce na shirya daukar kowane dafi. Lalle zuciyata ta bani sakon soyayyyar ki inason ki daure ki karba don babu wacce nake dako a kullum dare da rana idan bake ba ya ke masoyiyata na jima ina tara Wasikun kauna ina tura miki amma na kasa samun amsarki sai rana guda na samu wannan sakon da nake daukar shi a matsayin sakon da yafi kowane sako muhimmanci ma'ana sakon amincewar ki a maysayin wadda ta yadda in mallaketa kuma in mallaki zuciyar ta tun daga wannan ranar na shirya jure kowane kalubale akanki yake habibiyata abar soyayyar zuciyata
0 Response to "Kalaman soyayya masu zaka kwalla"
Post a Comment