-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman soyayya ga budurwa

Kalaman soyayya ga budurwa

Kalaman soyayya ga budurwa



Ya masoyiyata tunani na ya riga da ya bar jikina duk na susuce ta dalilin soyayyar ki idan bacci nake bazan farka ba saida kiran sunanki idan tafiya nake ba zan isa wajen da na nufa ba ba tare da na kira sunanki ba. Ya hayyu ya qayyum ina rokon Allah a Kullum safe da Marece domin samun galaba akan soyayyar ki a koda yaushe. Na zama kurma wanda babu wata magana da nake ji face maganar saukar lafazin rayuwarki domin banda wani tasiri a rayuwa bayan samun gansasshiyar kukawarki a tare dani. Kirji na ya kasance babba sabida tsananin yadda zuciyata ke tafarfasa tana cika tana batsewa a kowane lokaci kuma duk akan soyayyar ki. Na samu kaina cikin wani hali da yanayi na rashin samun sukuni idan har na kwanta na tashi baa taddani acikin sautin muryar ki ba dayake muryarki ko ba gareniba wata abuce wadda idan mutum ya saurare ta ya zama dole yasamu sukuni acikin rayuwatai. Kasancewa ina tare dake a kullum banda wani yanayi dake iya shigoni face farin ciki dake mamaye zuciyata a fannin rayuwa ta. Nayi nisa kuma nisan da babu wani juyowa da zanyi acikin rayuwa sabida banda yadda zanyi a rayuwa idan har ban samu kaina acikin yanayin samunki a koda yaushe ba. Kin zama zuma ni kuma na riga da na samu wani Muhimmanci ga alummar gari tunda ke kika zama zakaran gwadin gwaji a ko ina fadin duniya ta fannin kyawun hali da sura ta jiki mai kyau da kowane namiji yake alfaharin samunta a matsayin mata ko wata makusanciya mai iya share masa kukansa. Nayi kuka nayi murnar farin ciki ta dalilin samunki a matsayin masoyiya. Lalle Da lafiya ake gudanar da komai amma ni ko acikin yanayin da na samu kaina zan kasance acikin soyayyar kowace irin gudummuwa zan iya badawa domin insamu amincewarki ta fannin soyayya duk da cewa na san akwai wuya mace ta mika wuya akan soyayya amma ke inada tabbacin ke yar hakak ce bakida wani buri face kiga kin rike amana koda ba a fannin soyayya ba anyi miki shedun rikon amana ga kowace irin zamantakewa ta rayuwa. Lalle kowace mota tanada malejin gudu da malejin mai wanda idan babu isasshen mai lalle wannan malejin zai nuna amma soyayyar dake tsakaninmu dake babu Maleji a gareta domin batada kasa batada sama babu sauri kuma babu rashin sauri ko da wane lokaci soyayya ta da taki akan farashi guda take bata hawa sannan bata sauka koda yaushe cikin tsari take akan daidai. Na maida hankali na da tunani na akanki babu yadda zanyi inyi tunanin wani na iya gittama soyayyar mu. Akwai abinda ke tasomin shiyi tsaye a zuciyata amma likita ya Tabbatar min da cewa dole soyayyar kice tayimin fintikau acikin wannan zuciyar tawa. Lalle zan taka a hankali domin Nadori gamo da wadda tayi daban acikin mata. Wata rana ina gida sai gashi naga kiran wayar ki kina kirana kika gayamin cewa a koda yaushe bakida abinda kikemin face fatan akheri nikam nayi matukar godiya ga Allah domin samun mace mai kaifin hankali irinki kamar yadda kika zayyana bayaninki zuwa gareni wannan dalilin yasa koda yaushe na tuna da irin jin dadin da kika sakamin acikin zuciya. Tun ranar da muka hadu dake sai ruwan sakon waya nake tayi acikin wayarki wannan sakon soyayyar na sauka wannan kuma yana isowa.


Yanzu gashi bukin su ummi ake sai gashi bakinan kuma ke kadaice yar halak acikin kawayenta da naga dandazon taro har na tuna dake diya ta hakak wacce ba irinta acikin mata. Allah ubangiji shikara tsaya miki shiyi miki babban guzuri rahamar Allah ta zagayeki a koda yaushe. Lalle danginki sunyi babban kamu acikin zuriaarsu na samun mace irinki sabida bayyanar ki acikin dangi ba karamin cigaba ne. Lalle ina ganinki naji na sakaki acikin kololuwar zuciyata nayi nisa da soyayyar ki banida ranar da bazan shiga cikin zuciyata ina tambayar ya akayi inajin tausayinki. Babu wata niima da zan Samu acikin rayuwa face samunki acikin jerin sahun wadanda ke dauke da dakon ayukkan zuciyata. Babu barazana ta rayuwa irin ace gaki gani amma ba yadda zanyi idan har ban nemekiba. Duk inda kikaje rabbana ya kareki sannna ina fatan ki dawomin lafiya cikin nutsuwa bana son maza su kalli fuskar ki ko sauraren lafazinki. Yake yan mata mi ya faru wa ya tabaki don rigimarki a gareni haka take tamkar yaron da bai zama mutumba lalle nayi dace da masoyiya wacce ake yayi wadda ake yayi akoda yaushe lalle musha kauna domin duniya labari ce. Na zama surrikin baba surrikin mama su suka haifamin mata domin mu saita zaman lafiya. Lalle ko mace ta kalleni ba yadda zaayi ingane sunyi min kallon soyayya domin ke kadaice kayimin gizo a soyayya lalle son mai sonka shi ke sa ka gane minene so shiyasa ko yaushe nake ta ririta ki

0 Response to "Kalaman soyayya ga budurwa"

Post a Comment