-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Gajerun kalaman soyayya masu dadi

Gajerun kalaman soyayya masu dadi

Gajerun kalaman soyayya masu dadi



Soyayyarki wata abin alfari ce a gareni don haka a kullum burina inga na kasance tare da soyyayyar ki. Babu wani dare da zai zo mini har safiyar shi ta waye ban samu kaina acikin tunaninki ba hakan yasa a duk lokacin da nasamu kaina acikin jama'a Sai kaga wasu mutane da basu san dalilin shigata yawan tunani ba suna ta korafi akan yawan tunanin da nake yi ba dare ba rana a kullun na samu kaina acikin majalisa.

Ya ke masoyiyata akanki zan iya shiga rijiya mai gaba Dubu dari da hamsin da takwas wadda babu igiyar da za'a zura a kamota ayo zabarina daga ciki. Kin kasance abin mararina muradina wadda ban iya tunani na mintuna biyu ba tare da na ware miki na sakan dari da bakwai ba. Lalle banida laifi irin yadda na zauce da saka soyayyarki acikin Zuciyata banda wani burin da zai hana in samu yaddarki a fannin soyayya sabida rayuwata na cike da shauki tare da alhinin rashinki a kusa dani. Babu shakka ke mace ce wadda idan mutum ya rasata a rayuwar sa zaiyi wuya duk inda zaije shi dawo shi maida madadinki duba da halittar da Allah ya albarkace ki da ita wadda ba kowace mace ta samu irin wannan niimar jiki da sura ba gaki da zazzakar murya kamar zuma farar sakar da aka Saka shi a yanzu.



Lalle saida ido ake ganin hanya kuma kowane kyawon tafiya a nemi guzuri kamin a iso ga sansani shine dalilin da yasa na tilastama kaina samunki kuma duk wanda zaiyi kokarin tabaki a wannan nahiyar duniya dole zai hadu da fushi na domin jirgin soyayyyata baida wani fasinja a soyayya face ke domin a koda yaushe banida wata fada wadda zan iya zama wazirinta face fadar soyayyarki. Lalle girma yayimin amfani a fannin soyayya duk da komai girman soyayya bata kaima kauna domin soyayya ana kai karshen ta amma kauna itace tantagaryar mika wuya ga mutum. Lalle soyayyyar ki zuwa gareni tanada muhimmanci a gareni duk da na riga na zauce amma duk da haka na san ba gareni farau ba zallar farin ciki ba'a fara ba idan har ana magana ta soyayya da kauna to lalle babu tamkar irin yadda zuciyata ta kunnna zazzafar wutar da zata rura soyayyarki acikin zuciyata ya ke abinda nake kwana ina tashi da ita. Shiyasa a kowane majalisa na shiga acikin samari zakaga wasu har hassada suke dani ta dalilin samunki a maysayin budurwata.


Sauko Tsuntsun so sauko wayyo Allah Sauko Tsuntsun so sauko haba mai sona kidawo gareni koda zuciyata zata samu salama a rayuwa lalle duk matan duniya ke nafi so domin ke ta dabance kuma ya kamata ki gane kaunar da nake miki tamkar bishiya ce idan yayanta suka sauko suna son raino. Gashi sai yawan zuba nake tayi akanki Ni inasonki ko ina cikin numfashi na kuma zanci gaba da dakon soyayya ki har sai numfashi na ya tsaya. Soyayyar da nake miki tamkar a hada madaci ne acemin insha ba tare da na bata fuskata ba. Shi rabbana idan ya jarabceka da soyayyar mace to bakada wata makawa wannan dalilin yasa koda yaushe sai inji kamar Soyayyar ki sabuwa ce a gareni

0 Response to "Gajerun kalaman soyayya masu dadi"

Post a Comment