-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

1000+ Sakonnin Soyayya

1000+ Sakonnin Soyayya

1000+ Sakonnin Soyayya 



Ko a fakaice soyayya ke shigar Mutum nidai tawa ta ginu ne akan tsarin Daidai. Babu wani misalin da zan iya badawa gameda yadda nake ji a duk lokacin da aka kiraki A gaban idona sai inji duk wani sarkin dake duniya Na fishi babbar sarauta Domin Samun ki ba karamin girma bane tare da karramawa Duba da irin yadda Al'ummar gari ke yaba miki ba dare ba rana. Lalle kowane Tsuntsu kukan gidansu yake yi amma ni a fannin soyayya ta na kasa Samun koda bagire gudane Acikin zuciyata da zan iya lakube soyayyar ki ba tare da tayimin illah acikin zuciyata ba. Soyayya idan tayimin Yawa wata rana sai inji tamkar zan shagaltu in je in kama babbar hanyar da ba'a ganin karshen ta Kuma ya zamana babu wani gari babu kauye bale Al'ummar da zasu iya Taimakon ka na kan hanya koda kayi gamo da mummunan abu. Lalle kauna wata abu ce mai dauke da sakama Mutum jin dadi amma wani lokacin takan zama barazana ga Mutum yayin da furucinsa yake Bayyana duk wata alakar dake tare da kauna a fayyace ta fannin soyayya wadda ke wanzuwa a tsakanin saurayi da budurwa wannan sai ya zama izina ga kowane Mutum Wanda idan Bai iya soyayya ba tau sai Shiyi Kokarin kamawa da gaskiya Domin kada wata rana azo a Samu matsala Kuma irin matsalar da babu mai iya shiga shi gyara ta sai Allah. Hakika na zama mai laifi Kuma mai laifin da ya wuce wuri Wanda ya kai kimanin girman dutsen uhudu Kuma wannan laifin Yanada alaka da rashin kara maida Hankali dare da rana Domin in Samu in baki kulawa ta musamman wadda idan kika tuna wannan kulawar ko wata rana zaki iya yimim adalci ki daina yankemin hukunci cikin gaggawa Domin kin Riga dak kinsan Muhimmancin ki a gareni Kuma wannan dalilin zaisa duk Wanda ko wadda suka taso wajenki da sunan jefa kalma maras kyau akaina baza kiyi Gaggawar yanke hukunci zuwa gareni ba don kinsan Waye ni mi nakeyi Kuma mi nake iyawa. Babu ranar da zata zo inji zan iya dakatar da kaina daga yabonki Domin kuwa kinsan mai daki shi yassan inda yake masa ruwa Domin ni na Riga da na San kimarki da darajarki a wurina.


Kin kwance akalar dake jikin kowa ta soyayyar ki babban burina wannan akalar ta kasance a wuyana Domin in Samu sukuni. Tun ranar da kika Dora kafarki Acikin mafarkina tun daga wannan lokacin na jima ina Jira tare da fattake duk wani karon batta da mundahana da tabarrakin da koda idan anje an dawo wajen da babu wani mahaluki Wanda zaije wajen Mika wuya ba tare da ya kira wajen kurajen dake gurguzu acikin zukatan masoya masu dauke da launi kala kala da zai zama nakasu tare da wanzuwar duk wata damuwa da zata iya cire soyayya acikin zuciyar dake dauke da soyayyar juna wadda idan aka Samu kuskure ko rashin sa'a fahimta bata zamo daya ba zakaga dukkanin wadannan masoyan ba zasu Samu Kansu acikin yanayin Samun sukuni ba Har sai ma kaga yadda wannan yanayin zai zo musu cikin wani kushu'in da su Kansu masoyan bazasu iya jure wannan Abin ba kai koda tambo ne Abin ba za'ayi tunanin warakarshi ba dole sai an nemi kwararrin manyan likitoci na sassa daban daban, dole ma sai an Duba gabas an Duba yamma an Duba kudu an Duba arewa za'a fara tunanin wadanmi kalar manyan likitoci za'a gayyato Domin Duba wannan matsalar Domin idan irin wannan iftilain yana faruwa babu yadda za'ayi karamin likita ko ince likitan cikin gida shi iya bada maganin da zai iya dakatar da wannan Abin sabida shi likita ko a ina yake idan Har ba babbar asibiti da aka yima shaidar kwararrun likitoci ba zaiyi wuya a aminta Dashi wajen gudanar da manyan ayukka na musamman. Na budewa zuciyata kofofin kaunar ki wadanda na tabbatar da koda wannan soyayyar dake cikin zuciyar ki zata yi sallama acikin zuciyata koda kuwa bada sanina ba zai yi wuya wadannan kofofin basu zama babbar Garkuwa a Garesu ba Domin na Riga da nayi shawara tare da yanke hukunci tsakanina da zuciyata idan Har zuciyarki ta shirya yin samame tare da afka sallama kai harma Neman amincewar shigowa acikin wannan zuciyar tawa mai albarka da tayi Gaggawar amsarta cikin Lokaci Domin soyayyaya ta da taki idan suka hadu ba karamin tasiri zasuyi acikin manyan zukatan duniya ba zaka ga duk lokacin da za'ayi misalin soyayyar juna Hadi da amana to ya zama dole ala tilas abada misali da zuciyar Mu babban dalilina shine Soyayya da nake miki tamkar wani haske ne da ake amfani Dashi Wanda Al'ummar gari ko ince Al'ummar duniya kowa zai iya morar sa a kowane Lokaci misali kamar hasken rana ne Wanda kowane Mutum ya kwanta acikin dare baida wani buri face shiga Safiya ta Waye masa shina cikin koshin lafiya. Bayan wannan safiyar ta Waye baida wani buri face idanuwansa su gane masa hasken da zai Bayyana Wanda zai iya ganin koda tafin hannunsa ne Domin gudanar da abubuwan sa na yau da kullun haka ma idan ya Samu haka baida wani buri face hasken rana shi fara sauka a duniya Domin ya fara shiga Acikin ta yana shan hantsi Domin hantsi Yanada Matukar Muhimmanci ga Bawan Allah Domin kowace Safiya bata rasa yin sanyi wannan dalilin yasa kowane Mutum yake da bukatar Samun hasken rana ko don idan yayi Shanya ta bushe yaje zuwa nashi uzuri na gaba sabida duk Wanda keda rai da lafiya kowace rana idan Safiya ta Waye zaka ga Mutum Yanada abinda yake son yaje Shiyi a gabansa na rayuwarsa a kullun baida wani buri face shiga ya aiwatar da abinda ya kwanta da burin aikatashi tun acikin Daren.


Lalle nayi babbar Sa'ar rayuwa tunda na Samu juyowa da akalarki na saito ki acikin dukkanin jikina Kuma na Samu Sa'ar sauke duk wani nauyi dake dauke da soyayya ta a tattare dake idan ma na juya a ko ina banda wani nauyi da nake Dashi tunda na Riga da na tabbatar da cewa dukkanin soyayya dake damuna akanki na Riga nayi mata bugun diyan kade don na Riga da na dauki tutar soyayyar ki na zama gwazon shekara duk garinmu kowa sai kara tsorona shikai Domin karawa dani a Fagen soyayya ba karamin kalubale bane ga duk wani mai son ya ratsa soyayyar dake dauke da zuciyarshi taki zuwa gareki hakan tamkar ka shiga daji ne mai dauke da manyan zakuna Kuma kowane zakin acikin su da abinda yake bashi shawa acikin jikin Mutum Kuma wadannan zakuna kwara Hudu ne. Daya hancin Mutum yake bukata daya Kuma zuciyar Mutum yake son cinyewa dayan kunnuwan Mutum yake bukatar cinyewa shi Kuma dayan na karshen dukan jikin Mutum babu inda baida bukata. To kwatancen soyayyar ki dani tamkar wannan misalin ne kai kamar ma Wanda yaje gulbi ne mai dauke da manyan kadodi acikin ruwan Wanda kada Guda daga cikinsu girmansa ya kai girman kilomita Dari da Hamsin da takwas da digo goma sha bakwai.

0 Response to "1000+ Sakonnin Soyayya"

Post a Comment