-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

1000+ Kalaman Soyayya

1000+ Kalaman Soyayya

1000+ Kalaman Soyayya 



Sauko tsuntsun so sauko wayyo Allah sauko tsuntsun so sauko ni wancen shi nake so Kuma babu abunda zai iya ciremin shi sauko ko in dakatar da numfashi na Domin rashin ki a kusa dani. Wancen nafi so shi na nufa auren sa nake son inyi lalle so kamar wutsiya ne Domin kauna batason a rabe masa gida gida. Ya ke mai sona kisani inason ki Domin wallahi duk Wanda kika ji ance ana so sai ana ganin yayi duk da cewa shi kwadayi mabudin wahala ne wajen bada kafa sai asha madaci acikin Zuma ba tare da an Ankara. Lalle wajen zuwa sai a Dade ba a zoba idan ana ja daga Baya Domin shi dauke kafa ga Mutum ba karamin ci bayane.. Daga Allah ne soyayarmu ni dake Domin ke farin cikina ce Abin yabona ce dare da rana zan zama malami zuwa gareki Domin inyi lelenki Kuma in kasance ango naki Domin kece hubbi na mai rike kalbina Kuma kin zamemin hurul ainihin na tunda munyi cudanya tare dake dole in kasance mai shagwaba a gaban idonki yake yar fara tubarikallah yar dagwas inason in tabbatar miki da cewa sai na aureki Kuma aure na soyayya tsananina dake Wanda babu yadda za'ayi ayi tunanin rayuwa tsakanin Mu dake sabida kin San ita rayuwa batada wani buri face ta kasance cikin Samun abinda take so a koda yaushe sabida wannan dalilin yasa banda yadda zanyi tun farkon fara soyayyar Mu sai na kara jaddada miki irin kalar soyayyar da nake miki a rayuwa. Nayi zurfin tunani irin yadda na bada dukkanin yadda ta zuwa gareki Duba da yadda kema na Samu sukuni irin yadda kika aminta dani ta Bangaren bani dukkanin soyayyar ki a rana Guda Kuma a Lokaci Guda ba tare da nayi ta yimiki hidima ba. Bukin Mu za'ayi buduri Kuma irin budirin da ba'a taba yin irinsa ba ko a tarihin mutanen da dasu kayi nasu bukuwan aure daban daban.kisani banida laifi don na nuna son kaina a soyayya sabida hausawa na cewa rogo don kainai yake yin saye ba don mai gona ba to minene laifina idan na nuna tsantsar soyayyata zuwa gareki sabida abinda ke baki saniba shine kefa matar manya ce duk Wanda ya ganki baida wani buri face Shiyi duk yadda zai yi ko ta karfin tsiya ne shiga ya mallaki zuciyarki kai Har ma dake din ga baki daya to wannan dalilin yasa kike ganin a koda yaushe ina bada katangar karfe tsakanin ki da Mutane da Har kike ganin kamar son kaina yayi Yawa a Bangaren soyayya. Shin kin manta wani Abu in tuna miki; shin kin manta cewa kamin in shiga cikin jerin masoyanki ga baki daya dangin ki da Yawa sun so su kasance tare dake tun daga yan uwanki, makwaftan ki, Yan Ajin ki a matakin karatun da kike yi babu Wanda Bai nuna ra'ayin shi zuwa gareki ba kasancewar ke yarinya ce wadda duk wata halitta da ake so macce ta mallaka a jikinta ke Allah ya Riga da ya baki ita sannan banga wani Mutum na miji Wanda zaiyi ido biyu dake Bai sake maida miki wani kallo ba kai Wasu ma Har tuntube suke yi. Akwai lokuta da dama ina ganin Wasu abubuwan dake baki ganin su a yayin da muka fito yawon bude ido acikin gari a tare dake da Yawa Wasu manyan Mutane mamkin suke irin yadda na Samu mace kyakkyawa irinki Kuma ace kina bani Lokaci da kulawa kai Har ma ace zan iya daukar ki muna zagaya gari cikin so da kauna sannan su Kansu sunada bukata da su sameki amma sun kasa Samun koda lokacinki ne ki basu bale kulawar ki Amma hakan yaci tura hakan Yasa da Yawan Mutane idan muka wuce tare dake muna yawon shakatawar Mu a Matsayin masoya Wasu hadda kallon banza ake min Wasu Kuma harara Wasu ma hadda nuna tsangwama zuwa gareni Domin basuda wani buri face suga sun rabani dake sun mallake ki. Akwai Wasu kalar Mutanen da ni na kasa fahimtarsu a Bangaren soyayyar Mu daga ciki hadda yan uwanki na jini ba ma na nesa ba basuda wani buri ko tunaninsu a duniya face suga na rasaki ma'ana suga kin rabu dani kin kama wani koda ba cikinsu ba sudai babban burinsu Bai wuce suga mun rabe tsakanin ni dake ba shiyasa a koda yaushe rokona zuwa ga Allah Bai wuce In nemi Tsari daga Allah ga sharrin abu biyu da nake fama dasu Masoyi makusanci mai hassada da Kuma mai nuna maka masoyinka Ne Amma bayan idonka Ashe Bai sonka da ci gaba irin wadannan mutanen za'a iya hada kai da baki dasu Domin shiga gonar Mu aga cewa mun Samu sabani Kuma wannan sabanin ya zama Silar rabuwa tsakanina dake na tabbatar da irin wadannan Mutanen basuda wani buri Wanda yakai suga cewa koda wani ne shi malleke ki koda su ba sune zasu mallake ki ba idan ma suka Samu irin wannan Sa'ar babbar bukatar su ta Riga da ta gama biya tunda basu son duniya taga na tare dasu ya fisu yin zabi mai kyau a Bangaren Neman budurwa wannan shine babban bakin cikinsu a rayuwa Kuma insha Allah idan zaki ci gaba da bani hadin kai wannan mummunar bukatar tasu ba zata taba biya ba Har karshen rayuwar su sai dai bakin cikin soyayyar Mu ya kasance shine dalilin zama ajalinsu Kuma idan na gano ina tare da irin wadannan kalar Mutanen Hakika zanyi Gaggawar rabuwa dasu Domin duk abinda zai iya kawomin matsala ta sakan daya tsakanina dake bazan taba son shi a rayuwata ba kema Kuma kin San da haka Domin a ko ina zaki iya tsayawa ki bada shaida akaina ta fannin soyayyar Mu dake.


Lalle soyayyar Mu dake ta amana ce wadda babu wani Lokaci da nake tunanin akwai ranar da zata zo ta zama ranar rabuwa tsakanin Mu dake wannan ba karamar barazana ce a zuciyata ba Duba da irin yadda maka Samu shakuwa tare da jittuwa tsakanin Mu dake. Na tabbatar da idan Har sabani zai iya shiga a kowace soyayya Kuma wannan sabanin ya zama dalilin rabuwar masoya sannan Kuma wadannan masoya su jure rabuwar da sukayi ni na tabbatar da irin tamu soyayyar ba wadda wani zai iya jurewa bace Domin tamu soyayya ta daban ce banga akwai wani Mutum mahaluki da zai iya shigowa tsakanin Mu Shiyi koda barazanar raba tsakaninmu ba Domin na tabbatar da ke mai kishina ce Kuma Nima mai kishinki ne wannan dalilin yasa Mutane munafukai koda suna son shiga cikin soyayyar Mu suyi mata illa suna fargabar yadda zamu kaskanta su Domin ko acikin dangin Ku idan zaki iya tinawa akwai Wasu bara gurbi da suka shiga suka fita suga sun raba tsakaninmu amma hakan bata faruba sabida baki basu dama ba haka Nima basu Samu damar a wuri na ba tunda Mu tun farko mun Gina soyayyar Mu da kauna da amana tare da fahimtar juna a tsakanin Mu duk Wanda zai zo ya kawo miki suka ta da ya bar wurin zakiyi Kokarin hada zama tsakanin ni dake Domin Mu Fahimci juna gameda maganar da aka gaya miki akaina Domin kinsan da wuya in aikata abinda aka gaya miki sai Kuma kisamu akasin abinda aka gaya miki haka Nima idan hakan ta faru ba zanyi saurin yanke hukunci tsakanin ni dake ba dole sai na kira ki munyi zama tare da maganganu na kawar da zargi kamin shigar da maganar da aka gayamin game dake sannan daga Baya Kuma Mu Fahimci juannmu daga nan sai Mu zubar musu da Kima a idanun Mutane kowa ya Fahimci cewa ga yadda suke basuda wata rayuwa face Suga masoya biyu sun rabe Kuma su sun kasa Gina tasu soyayya bisa ga amana. Idan na tuna ranar da kika gayamin wata magana game da mahassadan Mu sai inji kamar akwai ranar da zata zo na cimma wannan mummunan burin nasu amma ko ina cikin wannan tunanin sai inji kai ina ma hakan zata faru tunda na tabbatar ke mace ce mai amana kin Samu kyakkyawar tarbiyya mai kyau daga iyayenki Wanda babu yadda za'ayi kiyi alkawali Kuma ki Tadda wannan akkawalin wannan dalilin Yasa koda yaushe nake kara kwantar da Hankali na game dake Domin inada tabbacin Dari bisa Dari ke ba zaki iya yaudarana ba a fannin soyayya Domin nayi ta gwada tunanin ki ina ta jaraba ki daban daban Domin inga abinda zai iya juyowa Baya amma ban Samu kama ki acikin irin wadannan matan ba wadanda da zarar sun fara soyayya dakai idan suka ga canjin ka yayi kasa daga nan zuciyar su zata fara rera musu tunanin da zasuyi su Samu wata mafita sannan wannan mafitar ba kowace mafita bace face suga sun Samu wani sun hada tare da soyayyar ka ya zamana suna hadaka kaida wani suna soyayya daku a tare Kuma kowane matsayinsa daban to irin wannan soyayyar itace soyayyar yaudara mafi girma Wanda matan yanzu ke yi daga karshen ma sai kaga mace tayi biyu babu ta rasaka Kuma ta rasa wancen tunda Galibi irin wadannan mutanen da zasu shiga soyayyar mace daga Baya Kuma bayan sunada tabbacin akwai Wanda suke tare Dashi kamin su Amma sai kaga sun aminta da yin soyayya da macen tunda dama tun farkon basu shigo da soyayyar su ta niyya mai kyau ba daga karshe bayan ainihin saurayin nata mai sonta tsakanin shi da Allah ya gujeta Sai shi Kuma ya kara matsa kaimi Domin kara kashe mata kudin da yake dasu da Yawan nuna mata abubuwan kawa daban daban Domin jawo hankalinta zuwa Gareshi daga karshen idan ya Samu biyan mummunar bukatar sa sai kaga ya kwashe kayansa daga gareta ya tafi abinsa tunda daman Surat jikin da Allah ya baki shi ya kawo shi ba soyayyar gaskiya ba daga karshe ma sai shi yanke duk wata alakar dake tsakaninsa da ita hakan yana faruwa sosai ga mata marasa amana shiyasa ni Kuma a koda yaushe nake rokon Allah Shiyi miki Tsari daga shedan Domin shi shaidan Abin gudu Ne ko yaushe da kalar wasi wasin da yake kawo ma mace bama Ku manta kadai ba hadda Mu maza. Allah dai yasa mudace ya Kuma kara mana zumunci akan wannan soyayyar tamu yakai Har ranar aure Mu gayyaci Mutane yan uwa da abokianin arziki sassa daban daban Domin isowa Mu shafa fatiha ta ranar aurenmu ni dake.

0 Response to "1000+ Kalaman Soyayya"

Post a Comment