Fitattun Taurarin Kannywood na Shekarar 2024/2025
Fitattun Taurarin Kannywood na Shekarar 2024/2025
Shekarar 2024 ta zo da abubuwa da dama, har da ɓangaren nishaɗi wanda ya zama ɓangare na rayuwar jama'a wajen kawar da damuwa da kuma shaƙatawa. Akwai taurari da dama da suka yi fice sosai a wannan shekara, la'akari da yawan fitowarsu a finafinai da kuma karɓuwar da suka samu wajen masu sha'awar Kannywood da finafinan Hausa. BBC ta zaɓi wasu daga cikin taurarin Kannywood da suka fi tashe a shekarar 2024:
Yakubu Muhammad
Yakubu Muhammad yana daga cikin tsofaffin jarumai a Kannywood, amma har yanzu tauraruwarsa tana haskawa kamar yadda aka gani a shekarar 2024. Yana kuma ɗaya daga cikin jaruman da ba su tsaya a Kannywood kaɗai ba, har sun tsallaka zuwa Nollywood.
Ya taka muhimmiyar rawa a finafinai masu daraja irin su Allura Cikin Ruwa, wanda shi ne darakta, da kuma Gidan Sarauta, Manyan Mata, da Labarina.
Amina Hassan
Amina Hassan, wadda tsohuwar matar Adam Zango ce, ta yi fice a finafinai da dama da suka samu karɓuwa a shekarar 2024.
Daga cikin finafinan da ta fito akwai Labarina, Garwashi, Unraveled Hearts, da Ɗakin Amarya. Ita ce ta fito a matsayin Jamila kuma ƙawar Maryam, wadda Mainasara ya fara so amma ta ƙi amincewa da shi.
Fateema Hussain
Duk da cewa Fateema Hussain ta ɗan jima a harkar Kannywood, a bana ta yi fice sosai. Ta fito a finafinai irin su Labarina, Jamilun Jidda, Na Ladidi, da Manyan Mata.
A fim ɗin Labarina, ta fito a matsayin Maryam, matar Mainasara.
Sai dai, bayan wasu kalamai da ta yi a shafukan sada zumunta da suka jawo cece-kuce, daga bisani ta nemi afuwar mutanen da suka ji ba daɗi.
Saddiq Sani Saddiq
Saddiq Sani Saddiq shi ne babban tauraron fim ɗin Labarina, inda ya fito a matsayin Alhaji Mainasara.
A fim ɗin, yana da mata biyu - Maryam da Dokta Asiya. Ya kuma taka rawa a cikin Manyan Mata da sauran finafinai.
Zahrah Muhammad
An fi saninta da "Diamond Zahrah" a masana'antar Kannywood. Ta yi fice sosai a 2024, musamman a finafinan Labarina.
A cikin fim ɗin, ta fito a matsayin Dokta Asiya, kuma ta zama matar Mainasara, wato kishiyar Maryam.
Maimuna Gombe Abubakar
Maimuna Abubakar, wadda aka fi sani da "Momee Gombe" a Kannywood, ta yi fice sosai a fim ɗin Gidan Sarauta.
Ita ce tauraruwar fim ɗin mai dogon zango wanda yake tashe a shekarar 2024. Ta kuma fito a fim ɗin Manyan Mata, wanda ya tara jarumai da yawa.
Firdausee Yahaya
Bayan fitowarta a fim ɗin Labarina, Firdausee Yahaya ta yi fice a cikin wasu manyan finafinai kamar Manyan Mata, Allura Cikin Ruwa, Garwashi, da Jamilun Jidda, wanda za a fara haskawa a Janairun badi.
Fa'iza Abdullahi
Jaruma Fa'iza Abdullahi ta yi fice sosai a cikin fim ɗin Daɗin Kowa mai dogon zango.
An fi saninta da Bilki mai abinci a fim ɗin, wanda ya haskaka ta a harkar Kannywood duk da cewa ta fito a wasu finafinai.
Kammalawa
Shekarar 2024 ta kasance shekara mai cike da nasarori ga masana'antar Kannywood, tare da ƙarin haskawa ga waɗannan
taurarin da suka yi tashe a shekarar.
0 Response to "Fitattun Taurarin Kannywood na Shekarar 2024/2025"
Post a Comment