-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Daure ka Karanta Wannan - Yadda Zaka Nemi Aikin Nigerian Custom Service 2024/2025

Daure ka Karanta Wannan - Yadda Zaka Nemi Aikin Nigerian Custom Service 2024/2025

Daure ka Karanta Wannan - Yadda Zaka Nemi Aikin Nigerian Custom Service 2024/2025  

Hukumar hana fasakwauri ta Nigerian Customs Service (NCS) ta fitar da sanarwa game da daukar sabbin ma'aikata na shekarar 2024/2025. Sanarwar ta fito a ranar 27 ga watan Disamba, 2024, wanda kuma ranar ne aka bude portal don masu sha’awar neman aikin su fara cike fom.  


Matakan da ake dauka a aikin sun hada da:  

1. Custom Superintendent Cadre (ASC - Consol 08):  

   Wannan matakin ya shafi wadanda suka kammala digiri (degree) ko HND. Idan ba ka da daya daga cikin wadannan takardun, ba za ka iya neman wannan matsayin ba.  


2. Customs Inspector Cadre (Consol 06):  

   Wannan matakin yana da damar cikewa ga wadanda suka yi NCE ko Diploma. Idan ka kammala NCE ko Diploma, za ka iya neman wannan aikin.  


3. Customs Assistant Cadre II, III (Consol 03, 04):  

   Wannan matakin yana da sauki saboda duk wanda yake da takardar Junior Secondary Certificate (JSC) ko SSCE (Senior Secondary Certificate) zai iya cikewa.  


Bangarorin da ake dauka suna kunshe da:  

- ICT  

- Injiniyan Kera Kaya (Mechanical Engineering)  

- Kiwon Lafiya (Nursing)  

- Da sauransu.  


Yadda Zaka Nemi Aikin Nigerian Custom Service 2024/2025  


1. Ka ziyarci wannan link: https://recruitment.customs.gov.ng/

2. Za ka ga shafi da aka rubuta “Apply Now.” Ka danna shi domin fara cike fom din.  

3. Ka zabi matakin aikin da ka cancanta kuma ka tabbatar da cewa ka cika dukkan sharuddan da ake bukata.  

4. Ka shigar da bayanan da ake nema, ciki har da hoton passport photo naka mai karamin nauyi.  

5. Bayan ka gama cikewa, ka danna submit domin a aika da fom din ka.  


Muhimmin Bayani:  

Za a rufe portal din ranar 2 ga watan Janairu, 2025. Wannan yana nufin cewa za a ba da mako guda kacal domin cike fom din.  


Allah ya bada sa’a!  


Tambaya ko Karin Bayani:  

Idan kana da tambaya, ka rubuta a sashin comment ko ka shiga Telegram Channel din su domin karin bayani.  

0 Response to "Daure ka Karanta Wannan - Yadda Zaka Nemi Aikin Nigerian Custom Service 2024/2025 "

Post a Comment