Aikin NGOs: An Buɗe Shafin Daukar Ma’aikata a Haske Humanitarian Aid Initiative (HHAI)
Aikin NGOs: An Buɗe Shafin Daukar Ma’aikata a Haske Humanitarian Aid Initiative (HHAI)
HASKE HUMANITARIAN AID INITIATIVE (HHAI) wata kungiya ce mai karfafa matasa da mata, da aka kafa a shekarar 2022. Kungiyar tana aiki tukuru don tallafa wa al’umma wajen magance matsalolin bangaren kiwon lafiya, inganta abinci mai gina jiki, da karfafa hakkin mata da matasa a matakin karkara. Manufofin kungiyar sun hada da samar da yanayi mai kyau da inganta lafiyar al’umma, tare da tabbatar da ci gaban al’umma mai dorewa.
HHAI tana mai da hankali kan kawo sauyi mai kyau a yadda al’umma ke kallon kiwon lafiya da walwalar zamantakewa na mata, matasa, da yara ƙasa da shekaru biyar. Ta hanyar haka, kungiyar na kokarin kawo sauyi mai ɗorewa a rayuwar wadannan mutane.
Yadda Zaku Cike
Domin cike wannan damar latsa shafin yanar gizo dake a kasa
https://forms.gle/7doKoHJuFuhcWy2P9
Allah Yasa mu dace baki daya
0 Response to "Aikin NGOs: An Buɗe Shafin Daukar Ma’aikata a Haske Humanitarian Aid Initiative (HHAI)"
Post a Comment