Zafafan Kalaman soyayya masu sanyi
Zafafan Kalaman soyayya masu sanyi
Na shirya tukarar duk wata barazana ta dalilin ki banda wani sukuni ga rayuwata idan Har ban hadu dake ba ya ke masoyiyata. Kin riga kin wuce duk yadda kike tunani a wurina Domin kibiyar ajali ma da ta tunkaro ni ta tsallake kaina Kuma ta soyayyar ki tazo ta soke ni maimakon in juyo inga jini haka naga tuwon so miyar so aka kwasheni aka kaini asibiti soyayya likitan masoya yazo yayimin gwaji ya tabbatar min da cewa soyayyar ki ce ta kamani ta hana ni sukuni Har ta kai ban iya ci sannan Kuma ban iya sha kullun zakaga sutura ta acikin datti kasancewar banda yadda zanyi in rage soyayyar ki acikin zuciya ta koda na sakan guda haka Kuma babban makasudin rike soyayyar ki acikin zuciyata Domin babu yadda za'ayi in Samu sauka da tashun numfashi idan Har babu yaddar zuciyar ki a kusa dani na kasa gane miyasa koda yaushe idan na kwanta bacci bazan iya bacci ba sai na takura Ashe ban farga ba soyayyar kice tayimin illah a zuciya Domin ita zuciya akoda yaushe batada wani buri face taga masoyi a kusa da ita Duba da yadda soyayya ke taka babbar muhimmiya rawar gani ga Al'ummar nihiyar duniya baki daya sannan zuciyar masoya a koda yaushe tana son mai kyautata mata sannan ta kasance a koda yaushe acikin fushi Da mai munana mata a rayuwa shiyasa na dage a koda yaushe inga na Samu kaunar ki da amincewar ki a rayuwa banda burin da yawuce in aure ki a koda yaushe.
Kin zama jinin jikina akan rashin ki a kusa dani yanzu gashi na kasance bani jin duk wani mai kirana ban ganin duk wani Wanda ke gabana bani sauraren komai koda yaushe cikin sauraren muryar ki nike. Bani nesa da fassara miki irin kalmomin da suka cika zuciya ta ta fannin soyayya da kauna amma babu yadda za'ayi a kwana a tashi banyi mafarkin kiba banida yakinin yadda zanyi in janyo hankalin ki, na cire rayuwata ga duk wata diya mace wadda batada kyakkyawar fuska irinki Duba da tunanin Wasu mata a koda yaushe ganin suke sun hadu Kuma kowane mace a kullun tunanin ta babu wata wadda ta kaita kyawun hali kyawun Sifa kyawun halitta koda ka ce bata kai miki kyau ba bazata yadda ba duk da na San Halayyar mata Abasu yafi su Baka. Lalle siyasar soyayyar ki da na fara na tabbatar Da ko takara na fito nine zan Samu galaba na tabbatar da cewa idan ina soyayya dake zan kasance acikin alfarmar ki ya ke masoyiyata aminiyar rayuwata. Lalle da naji kidan jaruma mata irinki ya zama dole inje in taka rawa dama na jima inason in Samu masoyiya irinki wadda akan tsanani sonta zai iya sakani Kuka. Lalle kin shiga raina kinyi girgiza burina kizamo jaruma mata. Albishiri zan miki yake sarauniya ta ki daure ki rike amana ta nidai kaunar ki tana kara sakani damuwa ki daure Kawai ki sakani dariya Domin zamana dake babu abinda ya kara mini face jin dadi da fara'a tabbas ba karamin ci gaba nasamu. Fatana ni dake ni dake Mu zama maaurata muyi aure ni dake muyi auren soyyayay Domin musamu karuwa Mu haifi diyan da zasu kasance a Matsayin hafizai Domin ranar yabo musamu karbuwa muje aljannah muna kara girgiza zuciya. Na tabbatar da cewa kin bani soyayyar da bazan iya dauka ba lalle Karen rashin mutuwa ko ina ana Dashi ruwa lalle kin saka maza Gudummuwa da na tanadat miki ba karamar Gudummuwa bace Domin ba yadda za'ayi in Samu kaina ba tare da na tunkari soyayyar ki ba.
Na shiga duk inda nake sa ran in ganki amma kash na kasa Samun ki na fara yawo tun daga abuja na bincika banganki ba naje cross river ban ganki ba naje Adamawa ban ganki ba na je taraba ban ganki ba naje gombe ban ganki ba a nan na tashi nazo bauchi a nan hanyar alkalere amma na isowa jigawa ban ganki ba haka na kai ki Har yobe wata rana akan haka na tambayi Mutanen yobe Kuma sun tabbatar min Da cewa baa ganki ba haka na hakura na shiga babban birni na jigawa nayi ta yawon nemanki amma ban ganki ba haka na yunkura na shigo babban birni Kano daga Kano na Duba lungu da sako amma ba inda na ganki daga nan na shiga hanya ta ta zuwa katsina na biyo ta hanyar kankara akan Layin gwarzo tsakiyar baifas Domin babu yadda zanyi ban biyu ta wannan Layin ba na zabura take na isa Garin katsina Domin Neman ki ya ke masoyiyata koda na isa Garin Katrina dare ya Riga da yayi a nan na kwana Safiya na Waye wa Kawai na fara binciken ta yadda zanyi in ganki na bi lungu da sako amana ban gankiba daga nan na yanke shawarar zagaye na biyo kan Layin sheme nan hanyar tsafe Domin zuwa Neman ki nan take nigga kaina acikin Zamfara nan take banyi wata wata ba sai na nemi masauki Domin idan na kwana Safiya ta Waye in fara Neman ki Safiya na Waye wa Kawai na fara yawon maaikatar Garin Zamfara nan na gano baki nan daga nan Har na fara fidda rayuwa daga ganinki.
Masoyiyata ban daina bada labarin yadda nayi na ganki ba tun lokacin da na kare yawona cikin Zamfara Kawai sai na tashi na shigo a Garin sokoto daga sokoto na fara yawon anguwanni na fara da guiwa locost da mabera na tashi daga mabera daganan da bangankiba sai na wuce kofar marke na bincika akacemin baki nan Amma ban kariya ba sabida na San sokoto babban Garin Da kike zama na hakika na shiga arkilla Kuma ban ganki ba sannan gani acikin badon Barade bamu haduba Kuma ba yadda zanyi in ganki ba bansan yadda za'ayi in kwana in tashi cikin sokoto ban nemi ina zan gankiba daga kowa bakin daga yin wannan kwanakin na tashi na iso kebbi babban birnin birnin kebbi amma saida nayi kwanki da Yawa banganki ba sai can wata rana Har na tabbatar da bazan ganki ba amma sai gashi mun hadu nan take nayi hamdala da Samun ganin ki a ranar
0 Response to "Zafafan Kalaman soyayya masu sanyi"
Post a Comment