-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yan Arewa mu Farka: Hukumar Fasa Kwari ta Najeriya (Nigeria Customs Service) ta Buɗe Shafin Daukar Sabbin Ma'ikata

Yan Arewa mu Farka: Hukumar Fasa Kwari ta Najeriya (Nigeria Customs Service) ta Buɗe Shafin Daukar Sabbin Ma'ikata

Yan Arewa mu Farka: Hukumar Fasa Kwari ta Najeriya (Nigeria Customs Service) ta Buɗe Shafin Daukar Sabbin Ma'ikata 

Hukumar Fasa Kwari ta Najeriya (Nigeria Customs Service) tana sanar da matasa masu sha’awar shiga aikin hukumar cewa an bude manhajar daukar ma’aikata yau, Juma’a 27 ga Disamba, 2024. Za a rufe neman aikin ranar Talata, 2 ga Janairu, 2025. Wannan dama ce ga matasa ‘yan Najeriya masu sha’awar shiga aikin kwastam don taimaka wa ci gaban kasa.  

Masu sha’awar neman wannan aiki su kasance suna da shaida ta kammala karatu da kuma cancanta bisa ga bukatun hukumar.  


Yadda Za Ku Cike Takardar Neman Aikin

  • 1. Shiga shafin yanar gizo na hukumar a: http://recruitment.customs.gov.ng/apply
  • 2. Cike dukkan bayanai da ake bukata da gaskiya.  
  • 3. Tabbatar kun gabatar da dukkan takardun da ake nema kafin wa’adin rufewa.  


Allah ya albarkaci dukkan mai neman wannan dama, ya kuma bamu nasara wajen samun aikin da zai kawo ci gaba ga rayuwarmu da kasa baki daya. Kada ku yi kasa a gwiwa, ku garzaya ku nemi wannan dama kafin wa’adin ya cika.  


Ku daure ku yada wannan sako ga sauran matasa don su ma su amfana. Allah ya taimaka!

0 Response to "Yan Arewa mu Farka: Hukumar Fasa Kwari ta Najeriya (Nigeria Customs Service) ta Buɗe Shafin Daukar Sabbin Ma'ikata"

Post a Comment