Yadda Zaku Cike Shirin Tallafin NDE Na Renewed Hope Domin Samar da Ayyuka 93,731 Ga Matasan Najeriya
Yadda Zaku Cike Shirin Tallafin NDE Na Renewed Hope Domin Samar da Ayyuka 93,731 Ga Matasan Najeriya
Ga cikakkun bayanai dangane da shirin NDE (Hukumar Kula da Ayyukan Yi) da aka kirkira domin tallafa wa matasa ta hanyar koya musu sana'o'i.
Tsarin Shirin Ayyuka na 93,731
A bisa tsarin Renewed Hope Agenda na Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya mayar da hankali kan bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da rage talauci, Hukumar NDE ta kaddamar da shirin koyar da sana’o'i daga watan Oktoba zuwa Disamba 2024 domin samar da ayyuka 93,731. Shirin ya kunshi sana’o'i nau’i-nau’i har guda 30, wanda zai amfani wadanda za su ci gajiyar sa. Manufar wannan shiri ita ce yakar rashin aikin yi a Najeriya tare da samar da yanayin da zai inganta samun kudaden shiga. Don tabbatar da cewa tallafin ya kai ga duk talakawa, shirin yana gudana a matakin mazabu na siyasa.
Lokutan Shirin
- Fara shiri: 14-10-2024
- Kammala shiri: 31-12-2024
Yadda Zaku Cike
Domin cike shirin, zaku latsa shafin yanar gizon dake a kasa: https://nderegistrationportal.ng/signup
Matakan Rijista:
1. Cikakkun Bayanai na Kai (Personal Details):
- Hoto (Ana goyon bayan tsarin JPEG/PNG/JPG, matsakaicin girma: 1MB).
- Lambar NIN.
- Sunan Gida.
- Sunan Tsakiya.
- Sunan Farko.
- Jiha ta zama.
- Karamar Hukuma (LGA).
- Mazabar Siyasa.
- Lambar waya.
- WhatsApp.
- Ranar Haihuwa.
- Jinsi.
- Matsayin Aure.
Allah Ya Sa Mu Dace Baki Daya!
hassanaaudu85@gmail.com
ReplyDelete