kalaman soyayya masu ratsa jiki da jijiyoyin
kalaman soyayya masu ratsa jiki da jijiyoyin
Ya masoyiyata na shiga kogin kaunar ki Kuma bazan taba tunanin soyayyar ki zata dakatar dani ba ya habibiyata na je na dawo duk inda zan je amma na kasa Samun mace mai kaifin tunani irinki ba, hakika babu inda kafa ta bata kai ba Domin in ganki in saka ki a idona amma kash duk masoya sun zagayo sun cimmiki suna Kokarin hada wata alakar juna dake Kuma na tabbatar Da babu dalilin da zai sa kibi ra'ayin wani saman nawa ra'ayin.
Akan rashin ganinki Har ta kai ga na rame bazan iya cin komai ba murmushin ki tamkar fadama ce a gareni mai dauke da lambun itace kamar Gwaiba, Gwadda, lemo abarba Daidai sauransu wadanda nake sha a bakina ina kara jin dadin rayuwa. Ban cika magana ba idan na fito wajen gari amma a duk lokacin da muka yanke shawarar fita daga garinmu ina mai tabbatar miki tabbas zan yi iya kokarina Domin Inga na dakatar Da duk wani Da na miji daga isowa ta Bangaren ki. Na isa babban birni amma ban Samu biyan bukatar rayuwata ba Domin na shiga wani hali ta dalilin da yasa banganki a kusa dani ba hakan ya sa koda yaushe zan Samu kaina Acikin nishadi ya zama wajibi sai nayi Kokarin gayyato wani mai Kokarin tasuwamin maganar ki a koda yaushe hakan zai sakani farin ciki na rayuwa. Banyi tunanin zan iya tada jijiyar wuya na akan wata bukata tawa ba amma akanki ya zama wajibi in tabbatar Da rashin jin dadina a duk lokacin da na Fahimci wani ya zo wajen ki Domin Neman soyayya ki wannan shi zaisa na dakatar Da wannan kidiri acikin fannin zuciyata ni na Riga na tabbatar da hakan.
Banda wani kuduri a zuciya ta face in isa a gidanku in nemi uzuri daga iyayenki in nemi damar Neman ki haka Kuma in shiga birnin soyayyar ki in kai kudin aurenki in Samu saka ranar aurenki haka Kuma in aurenki. Lafiyata da gangar jikina sun kasance babu wani karfi Wanda zai iya rikemin gangar jiki kasancewar soyayyar ki da kaunar ki ta Riga tayimin dafifi acikin babban birnin kalbin zuciyata. Nayi Nisan da bani jin kira idan ba na soyayyar ki ba na tabbatar da bazan iya sake numfashi ba. Lalle an kawo harshen zamanin da bazan iya cewa komai gameda soyayyar dake tsakanina dakeba sabida banida tushen da yafi soyayyar ki kin Riga da kin zama tamkar sugar ga kunu na na kasa Samun numfashi mai kyau babu yadda zanyi na karasa soyayya a tare dake Domin babu wani wunin da zai zo babu tunanin ki acikin sabgar rayuwata ya ke habibiyata muradinki shine nawa Samun ki shine fata na babu shakka na sameki a kusa dani habibiyata mai son fara'a ta banda ke ya zanyi in sha wuya Domin Babu wata diya mace wadda nakeso idan ba ke ba. Nayi nisa ga soyayyar ki ya habibiyata zinariya ta
0 Response to "kalaman soyayya masu ratsa jiki da jijiyoyin"
Post a Comment