-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman soyayya Masu Dadi da Ratsa Zuciya da Saka Nishadi 2025

Kalaman soyayya Masu Dadi da Ratsa Zuciya da Saka Nishadi 2025

Kalaman soyayya Masu Dadi da Ratsa Zuciya da Saka Nishadi 2025



Masoyiyata lalle ance shimfidar fuska tahi ta tabarma amma idan nayi fushi ki rarrashe ni Silar sonki na shiga babban karni Domin kinga duk wayon dila a daji sai gashi so ya tafi Dashi ba tare da saninta ba. Mace kike mai iya jure yanayin rayuwa kina iya zama da masoyi ko akwai ko babu shi kina iya jure Zamantakewar aure lalle nayi naam da Hankali ki natsuwa tare da ladabin ki lalle kinada girman daraja a gareni yaddar da Nike miki itace ta sa na baki ajiyar so Domin ga sakonnin soyayya da zan baki yake masoyiyata. Wasu mata na maganin da soyayyar da kake musu Domin ya zama makami Garesu Domin hukunta masoyin su to ni na Riga na bar wannan mugun Layin Domin Wanda ya soka da gaskiya kaima dole na soki.

Kin San na jima inason mace mai haiba irinki Domin Samun mace irinki sai an rike wuta ganin ki na shirya ma Kuma na Riga na taka matakin da babu mai iya dakatar dani akan ki Domin akanki na fara kauna Kai dawo, dawo sarauniya Domin so ya shigo mini banda shiri gashi zuciyata ta Riga ta zautu gani akan soyayya nake shan yawan kira mai budurwa yau gashi ina ta kalon kallo banda yadda zanyi, na Riga na fara kaunar ki tunda so ya Riga yayi kira zuwa gareni sabida haka inason in shaida miki cewa lalle baa fushi da so saidai dangana Jarumi a so Bai yin fargaba. Ko zuciya ta Sheri ba zata ce bata San soyayya ba Domin duk Wanda yake sonta ta sanshi yawan fushi a soyayya janyo fitina ne. Taka sannu sannu in miki tambaya Albishir a so ya Riga ya zama dole in bayyana miki Domin kara miki haske game da soyayya da amana...

Murmushin ki ya sacemin zuciya kwar jinin ki idan ina bayani akanshi acikin Mutane sai kaji Wasu na fadamin cewa wai banida Hankali. Ga Zuma ta kauna ga madara Kuma ki zabi duk Wanda kike so Domin kowane Yanada Muhimmanci agareni Kuma a gareki.

Na tabbatar da ke tantabara ce uwar alkawali wannan dalilin ya sa a koda yaushe banida wani buri face inga na kulla alaka wadda take tabbatacciya tsakanin Mu dake Domin kin Samu shaidu marar misaltuwa daga wurin Mutane hakan Yasa ko bani ba kowa na ta aringizo Domin shiga ya Samu yaddar amincewar soyayyar ki ya ke tauraruwar da ke haskaka fitilar zuciyata


Ya masoyiyar Zuciyata Kin bani so shiyasa na yanke shawarar in baki kauna tare da kulawa Domin itace tabbatacciyar Sakayyar da Ya Kamata Inyi miki a rayuwa Domin Kin cancanci kyauta ko wace iri daga gareni. Hakika kin zama haske Kuma kin zama tauraruwa dake Yaduwa acikin dare ta haskaka Al'ummar duniya masu dauke Da soyayyar juna a tsakanin su. Lalle Tun ranar Da muka hadu dake a ranar na tabbatar da na Samu rabo babba akan babban kamun da niyyi na Samun macce mai ilimin zamani da na addini irinki, mai kyawun hali, mai kyawun haiba mai Matukar Gashi Har kasa sai kace matan larabawa.


Babu wata gada wacce bazan iya tsallakewa ba idan Har na tabbatar da cewa idan na tsallake gadar zan iya isa babban birnin ruhin zuciyar ki mai dauke Da soyayya ta ya ke aminiyar rayuwata, tauraruwa ta wace nake ma Fatan zamowa mata ta. Lalle duk ranar da zata fito Har ta fadi banyi tunaninki ba na tabbatar da wannan ranar itace ranar da rana zata fito a yamma Wanda na San dole wannan ranar itace ranar Da Kowa zai kasance ta kansa yake sabida itace ranar karshe wadda bayi kowa zaiyi ta kansa ranar da babu aboki ba uwa ba Uba babu yaya babu Kane babu Dan uwa bale dangin juna bale wani makwafci.


Lalle Na tabbatar da nayi babban kamu a soyayya irin yadda na Samu yadda da amincewar yarinya mai kyakkyawan fuska da tattausan lafazi irin ki Wanda na tabbatar Da Duk Yankin kasar ga banga wani matashi Wanda zai kaini zabi mai kyau ba idan akayi la'akari da kyakkyawar fuskar Da Allah yayi miki Har Mutanen duniya suna tsananin tunin cewa ke balarabiyace Wasu Kuma na tunanin ke baturiya ce haka Kuma Wasu mazan abinda a tunanin su game dake wai ke yar India ce ko Kuma kinada alaka da indiyawa ko ta wajen dangin uwa ko Kuma ta wajen dankin mahaifin ki. Babu Shakka duk lokacin Da kika fito kan hanya Al'ummar garinmu kowa sai mararin Samun ki yake Domin yaga cewa kin kasance tare Dashi a Matsayin matar aure ko banza zai more iri Wanda idan kika Haifa masa 'Yaya zasu zama babban jari a wurin shi sabida ko shugaban kasa ya gansu sai ya ji Yanada ra'ayin aurensu ya ke sahibata muhibbatuna lailatil kadarin zamani na kin zama haske a rayuwa ta Wanda bazai taba gushewa ba Har sai ranar da mai zuwa ya dawo acikin wannan nahiyar duniya mai dauke da saman bakwai da kasan bakwai tare Da Al'ummar dake rayuwa akanta tun daga jinsin maza Har zuwa jinsin mata akan doron kasa.


Na kashe dukkanin ayukka na na tsaida duk wani tunani na akanki Domin kasancewa ta a tare dake ba karamar riba zai zame min ba sabida akanki duka kofofin Samu na da duk wata hanya tawa ta alheri sun Riga da sun bude tun daga nan na tabbatar da cewa lalle soyayya ta dake na Riga nayi awon gaba dake sosai tunda Al'ummar garinmu ma sun tabbatar ma duniya cewa ni na shiga da kafar dama acikin soyayyar ki Domin ke wata kyakkyawan halitta ce mai kwarjini a idon kowa wadda duk Wanda ya sameki dole ne ya zautu Kuma ya kara Samun farin jini ga idon Mutane kasancewar ya dauko sabuwar haja mai tsadar gaske irin wadda ba kowane Mutum ke iya tayawa shi kwashe ba koda kuwa shi mutumin jinin sarauta ne babu Shakka idan yace ya Samu hadin kan soyayyar ki tare Da amincewar ki lalle ya zama wajibi shi aje wadannan abubuwan kamar haka: girman kai, fifiko, izza tare da duk wani nau'in rayuwa ta diyan sarauta Domin ajinki ke ba don gidan sarauta aka yishi ba kin kasance Garkuwa ce akan kowa Kuma kowa ya sameki zai zama mai ribautar rayuwa tunda ke ce macen da duk matan Da suka ganki Har Rena Kansu suke Domin matakin Da kike Dashi ta fannin ko ina ya Riga ya haura nasu tun daga fannin ado, Sifa, kamala, iya Tafiyar ya mace, laushin murya, iya Jan aji, murmushin idanu Dadai sauransu wadannan abubuwan da na lissafa dukan su kin fi mata da Yawa more masu wannan dalilin Yasa ke kika zama ta daban acikin mata Kuma kika kasance mai aji ga kowane namiji Acikin nahiyar duniyar nan.


Na rattaba hannu akan kowace doka da aka shimfida amma banda wata dokar da zata dakatar dani akan Samun ki acikin kasar nan Domin tun ranar da muka hadu dake koda na iso a gida saida nayi tuntube Har sau ashirin da biyu akan na shiga tunanin ki Kuma ba kowane tunanin ki na shiga ba face irin yadda kika bani hadin kai kika yadda dani a fannin soyayya. Lalle tun daga ranar na riga na shirya damarar yaki da kowa Domin Samun ki a kusa dani a koda yaushe. Banida wani buri guda da nake Dashi a duniya kamar inga na Samu amincewar ki a fannin soyayya ta Kuma sai gashi na Samu to wannan dalilin ya sa na fara tunanin duk Wanda ya ganki zai iya Kokarin shigowa shi nemi soyayyar ki ko ta halin kaka amma na kasa ba kowa damar yin haka sabida na fara taririyar ki tare da kara janyo hankalinki zuwa gareni a koda yaushe duk da na San Wasu na iya tunkaro ki suyi miki barazana da kudi amma wannan ba gabana shike ba tunda na San ke kudi basu a gaban ki sabida idan Har kudi ne babbar matsala a gareki na tabbatar da cewa babu randa zan Samu lokacin tsayawa tare dake ballantana in samu aika sakona na soyayya da kauna zuwa gareki Har Kuma ki nunawa duniya ke amince dani Kuma ni na zama naki

0 Response to "Kalaman soyayya Masu Dadi da Ratsa Zuciya da Saka Nishadi 2025"

Post a Comment