Kalaman soyayya masu dadi da ratsa zuciya
Kalaman soyayya masu dadi da ratsa zuciya
Soyayyar da ke raina akanki bazan taba canza ra'ayi ba duk da cewa nayi lullubi kamar ango da amarya. Kin zama gagari gasa Kuma uwar Zuma abiki da gayya amma matan da suka kaiki kyawu zaki gansu halinsu ya banbanta da nasu Domin naki hali yana gaban nasu ba nan Acikin jaha ba hadda makwaftan jaha Domin babu irinki acikin matan duniya.
Kinada karamci na tausayi kin Riga kin gama da sauran mata duniya tunda gida gida mata duk suna son suyi kwaikwayon ki amma sun kasa wace macece zata ja dake sai wawuya ko mahaukaciya ina wuni ina kwana Domin dake nika alfahari yanzu babu wata mai ja dake. Yadda kika kulawa dani kema Allah ya kula dake sannan banda macen da Nike alfahari dake kinada karamci na tausayi shiyasa na kara amincewar dake Domin soyayya dake tana kara sakani nishadi. Ni nasan kin kula dani banda wata diya mace da zata iya yimin irin yadda kikemin irin yadda kike nunamin so Nima dole in kula dake sannan bazan taba bari kiyi kuka sabida ni ba Domin babu tamkar ki a wurina sannan Aikin ki yana kyau a koda yaushe dawisu kike ko a wajen ado. Ruhin jikina kin zamto jinin jikina ki yadda dani ki zauna Har abada kece a zuciyata na baki rayuwa ta yadda kibani taki rayuwa kema na baki ragwama ta yadda ki kaini inda zaki kwana nayi kewarki kin zama kundin ajiyar da bani baiwa kowa kin kai matakin da duk Wasu makiyanki zan iya maida su gawa na baki makullin soyayya Kema kibani naki Mu taru Mu kulle. Na baki naki so nema kiyi Hakuri kizo Mu zauna idan babu ke ya zanyi in rayu? Gashi ana yi muna gani ina matan dake cewa ke ba kowa bace yau gaki a Filin dagar masoya da yake ke dogaron ki Allah a gaya musu ke baki San wasa a soyayya ba sannan kin rike kaunar manzo saw. Lalle Hakim sama sai rakumi hakin kasa sai kwaki sannan yawan Sara da sassaka bazai taba kashe gamji Domin ruwan sanyi yau da Gobe zai iya dafa ganda Mutane na ta yokuwa Domin a ganki sabida a Garin Mu kowa ya ji labarin Mu.
Lalle shimfidar fuska ta wuce ta tabarma sabida haka ki tallafamin kada so yasani hauka idan nai fushi ya kamata ki rarrasheni Domin so yana zame mini tsani lalle nayi dacen masoyiyar dake saka ni dariya mai kunya ga ladabi da biyayya Domin baki biyema kawayen banza inasonki masoyita na kasa Samun tamkar ki burina inganki acikin gidana Kuma in tarairayeki sosai fiye da yadda zan yima kaina yadda ce tasa na baki ajiyar kaina yadda ce da amana. Lalle duk Wanda yasamu kulawa a soyayya lalle ya Samu so na gaskiyar kamar yadda kikemin duk da cewa akwai Mutanen dake tunanin wannan zamanin soyayya ta canza babu amana acikinta wannan ya saba ma dokar soyayya.
Na Riga na fara kauna tunda soyayyar ki tayi kira zo taho yar baba lokacin da na hango ki na tabbatar da duka soyayya makauniyar Abu ce Domin ganinki na Riga nayimai shiri akanki na shirya fara so a rayuwa yake gimbiyata mai son fara'a ta yau na fara soyayya dake Kuma zan kasance Har abada lalle so ya shigoni babu shiri na kasa inda zan fake dare da rana fitilar soyayyar ki ke haskani yau gashi akan soyayyar ki bana karba kiran kowa ba tunda na Riga nayi miki alkawali Bazan taba nisa dake ba. Kuma soyayya baa son fushi aciiinsa saidai dangana dakai zuciya nesa ya muradin raina. So ruwan Zuma ne Kuma ya Riga ya shigemin zuciya.
Ko zuciya ta Sheri bazata ce ita bata San so ba. Duk masoyin kwarai zai jure karan tsana akan wadda yakeso shiyasa ko yaushe na shirya duk wani fada da makiya. Nine ke shirin tanadar miki da madarar soyayya a rayuwa yake habibiyata murmushinki ya sace zuciya sai yawan ambaton ki nake a ko ina irin yadda kyawun ki ya ratsa Al'ummar Yankin Mu hakan yasa sauran mata idan suka ganki komawa hanyar gida suke Domin kin Riga kinyi musu rata kin zama jaruma a Fagen so. Ke budurwa tace ke Kuma nake kauna Kuma haka na ganki na kyasa Kuma bazan taba rayuwa ba tare dake ba so ya Riga yayimin ginin da aka kafa a tubali acikin zuciyata koda kallo na kikayi zanji sanyi ga zuciyata agareki rayuwata ta nace Har naji na zauce na tabbatar da dake na dace. Abin alfahari gareni gareki ki zama kusa dani Domin al kunyar ki ta wuce tunani duk Wasu masoya masu son suyi koyi da soyayyar Mu.
Zuciyata ta Riga ta gansu da kyawun ki. Kinga nidai kin mini kema ki zayyana mini matakina a wurinki burina ni dake zaman lafiya gashi kalamai na na soyayya sai sauka suke Domin babu wani mahassadi da zai kusantomu ya cimu da yaki akan soyayyar Mu nidai burina kada ki gujeni Domin sonki tayimin mamaya akanki na koyi karfin halin yin yaki da soyayyar kowane daya mace a fadin duniya Domin babu mai iya tunkaro ni gameda maganar soyayya kasancewar ke kikayi nisa acikin zuciyata
Duba kika yadda soyayyar ki tayimin a jiki duk da na San kina sane kinga yadda tunani na ya canza ko na waiwaya Kuma na juya Kuma amsa ta guda ce babu abunda zai canza na so kizo ki tafi dani kada so shiyimin lahani ya za'ayi na kara so tare da kara lullube ki da kauna ni naso kisoni son da babu guru babu laya ba don kwalliyar da Nike ba Kuma ba don abina ba inasonki so na gaskiya ba na yaudara ba masoyiyata abin alfahari na. Yau na tashi banda wani sukuni shiyasa nakeson inga na ganki koda ina Samun salama acikin rayuwa ta.
Ko baru basu gwada mana yadda ake zama da juna ba Kuma koda tsotsayi ya rabamu dake bazan kara tunanin yin aure ba ki kula dani ki soni kin zama ji na da gani na Kuma uwar yaya na mai dakina. Zuciya ta ta nunamin cewa kece cikar muradin rayuwa ta koda yaushe ya habibiyata ke naba zuciyata Kuma bazance kikawo ba ya habibiyata. Kada ki tafi kiyi nisa gareni Domin yakan iya zama sanadiyayar mutuwa ta banda yadda zanyi tunda ko iyayyenkii sun tabbatar da zuciyata tana akanki ya aminiyata.
So na tabbatar da gaskiya ne tunda naga yadda ya shiga jikina ya mamaye ni. Duk yadda kaga so idan Har na gaskiyar ne zaka ga ya zo da kishi amma na gode Allah da ya hadani da mace mai fahimta Kuma maison gaskiya Kuma nata bata zamiya. Na San zaki bani yadda sannan ga soyayyar ki nata yaduwa Kuma idan Kuma zaki Bini ni na Riga na shirya naga kinada alkunya Kuma komai zanyi in shirya don Allah kibani soyayya kamar yadda Nima na baki soyayya duk mai sonki ni inason shi. Na yadda so makaho ne irin yadda a baya wata ta yaudareni nine komai nata a rayuwa na dauka cewa koda wata rana ta gayamin zata canza tabbas zan karkata Domin nayi Matukar yadda da ita Domin na saba da ita amma idan yanzu na ganta sai inji ma banda sukuni Ashe bayanin ta bayanin banza ne babu komai face yaudara.
Kullun sai daga ta zo wajen na Domin Mu gaisa Kuma tabani zuman soyayya na sha baida Hadi da komai face kaunar daga karshe ni inai mata soyayyar gaskiya amma ita bata gari ce na kauda so Domin ita tayimin hiyana a soyayya dani da ita banyi tunanin akwai rayuwa ba Domin akwai Matukar zafi kaso Mutum ya gujeka
To kinga na daina sonki tun ranar da kika nunamin baki sona ni na Sani babu mai sonki tamkar ni a duniyar nan Domin ni na baki makullin so da kauna kika kulle idan Har akwai abinda zai saka miki kauna ba yadda zanyi in rabauta. Na jure zagi da kyara akanki babu yadda zanyi duk da haka idan na kirarki a waya bazaki dauki kirana ba Har ta kai ina tunanin cewa babu yadda zanyi a fannin rayuwa. Zafin zuciyar da na jima ina dauke Dashi na tabbatar da babu wani na miji mai iya jure shi Anma haka na jure wahala a soyayar sabida ina son ki na Riga nayi ta jani talau duk da ni na dauka komai sai na dauki cewa babu abinda zanyi Daidai sai dake sai gashi farin ciki ya gagara.
Kaunar da nake miki ta ratsa jini da fata dole saidai kijani Mu taka a Hankali Domin yau da Gobe sai Allah shi keda mulki akan komai Kuma ni na tabbatar da cewa matsalar ki matsala ta ce ya ke sahiba. Bini da kauna Domin in gwadamiki soyayya idan naga wani a kusa dake zuciya ta tayimin ciwo. Gashi zuciyata ta bani sako zuwa ga zuciyar ki tashi gashi ina ta dakon ki safe da yamma. Idan kin Duba tarin wasikun Da na karanata Kuma na rubuta zaki ga cewa na Samu tabbacin babu yadda zakiyi a rabamu na Riga na gansu dake ya aminiyar zuciyata na tabbatar da cewa komai Nisan jifa wata rana kasa zata sauka babu yadda zanyi Domin ni ke nika ta dako safe da yamma sannan duk macen da bata fesa turare bayanki take Domin ke a kullun cikin Tsafta kike a kullu Yasmin ke kina ke ce rainin turare ya habibiyata
0 Response to "Kalaman soyayya masu dadi da ratsa zuciya"
Post a Comment