-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman Soyayya 2025 Masu Dadi

Kalaman Soyayya 2025 Masu Dadi

Kalaman Soyayya 2025 Masu Dadi 



Masoyiyata nine naki Har kullun mai baki zallar so koda ke jinin sarauta ce ya zama dole Mu kasance tare dake Duba Da irin yadda kike faranta min. Kece na kama Kuma banda wani buri Wanda ya wuce na kasance a tare dake Domin banda wata kyara ko isa Da zan nuna miki Domin soyayyar ki batada misali a fadin duniya kizo Rabin raina muradina kada kiyi watsi da soyayyar da Nike miki shin mi zai saka na baki rata Domin na tabbatar da kaunar ki bazata taba warware wa ba sonki yasa Har na kasa baci banda wani buri face in ganki kada ki yada ni Domin ina ganinki naji na aminta dake Kuma na tabbatar da na Riga na rabauta indai Har jini da fata suna tsayawa na tabbatar da cewa kaunar Mu dake bazata bar jikin junan Mu ba sabida haka ki saurara kiji zance na idan kikayi biris da zance na ruwan soyayyar da nake miki babu shakka zasu kafe. Sannu sannu idan Har ana tafiya wata rana jariri zai zama ango Kuma ya kasance a Fagen daga amatsayin jarumi


Alkawalinmu dake ki rike kar kiyi wasa kada kisake zuciya begen ki take tunda Har soyayya ce ta hadamu na tabbatar da rabuwarmu dake akwai Matukar wahala daga nesa na fara ganinki kinyi kyau a fannin Tafiyar tun daga nan kika Tara mazan gari a bayyane kowa ya iso Domin ganin kyakkyawan furkarki nan take nazo na bayyana musu cewa soyayya ce ta hadamu ni dake Kuma ko mutuwa bazata iya rabamu ba da ita zanje wajen dangina Domin ita na zaba muyi rayuwa ta Har abada yar doguwa kike mai kyauwo kamar zinariya kin Riga kin fidda ni acikin damuwa lalle ina cikin sahun Samun manyan mace irinki ya ke aminiya Kuma gimbiyar rayuwa ta. Mai sona ki rikeni amana Domin duk inda naga mace mai karamci ban taba ganin wadda takai ki ba wato kin gane ke din ta gaban ce don haka na zauce Kuma na maida Hankali Domin Samun ki


Ga sakon da zan baki na soyayya Domin ki aje mini shi kin sanyani nayi gudu Har nayi gumi soyayyar da kike mini na Riga nayi fice akan ki soyayyar ki farin cikin take Sani ta sanyani farin ciki ke kadai Kuma nake gani Acikin matan duka duniya kin sakani ina ta zuba koda muryarki na jiya sai inji na damu da sai na gareki indan zan iya fasani na tabbatar da babu bakin halin Da zan shiga face sai kinzo kin bani ceto. Ya masoyiyata ki tsaya ki saurareni Domin idan kika gujeni ni kaina bansan ina zan kwana ba kasancewar ke ta musamman ce acikin matan zamani so Kawai nake bukata agareki Domin kaunar ki ta shigemin jini da tsoka irin yadda bazan iya tsayawa lissafi ba tunda na Riga na sauce nayi canjin rigar mahaukaci tun a baya ke ce ya kamata. A labarina na soyayya ke ce nayiwa rakiyar so lalle nayima so bauta Har ta kai idan na shiga gidan Ku da nayi magana zasu gane muryata sabida Sun San yadda na jima inasonki ina ganinki a take gabobin jikina zanji sun canza Domin ke ce kalar matar da kowane na miji yake nema nidai yau na gode Allah dukan matan gari sai kallona suke irin yadda nakai matakin Samun irinki a Matsayin mata. Wata rana ina kirarki ta waya Domin insamu inji muryarki kirarki na shiga sai naji waya ta yanke sabida na Riga na damu sabida sonki yayimin kamun da Har ana tunanin inada aljanu bazan kusheki ba Kuma koda yaushe cikin gyaran murya Nike Domin kara birgeki ya ke gimbiya tawa bazan taba kushe soyayyar ta a gareki. Tambaya ta akeyi acikin Garin Mu wai ke wacece a wurina Kawai sai nace musu ai ke sarauniya ce mai dauke da birni zuciya ta ta fannin soyayya.


Bari kiji soyayya dake tana da dadi Domin ni na yadda na tabbatar da hakan ke ce karfin idanuwa na Kuma gaki dole ke ce sauran Duba da yadda naga kina tare Dani a koda yaushe ina tare dake yanzu haka banda yadda zanyi acikin zuciya ta ta fannin Taimakon da bazan iya alfahari ba Domin Allah ne ya bayyanami soyayyar ki acikin zuciyata da zaran na kasa runtsawa ke ce idan na tunaki zanji wani Sabin tunani ya ratsa ruhina idan bake ba banida wani buri face in kaiki gidana yake yar Fulani ke nake so soyayyar ki tayi data Acikin zuciyar yake kurratul aini ina soyayya amma banda wacce nake soyayya da ita wadda ta fiki kyawun halin haiba Kuma farin ki ya bayyana siffarki Kuma yadda zuciyar ki take fara haka Kuma furkarki take fara shiyasa kowa ke son ya sameki ki tabbatar da zuciya daya kizama matarsa Domin Samun ribar rayuwa biyu a lokacin guda. Gida gida kowane namiji sai bashi shawarar iyayenshi keyi Domin zuwa ya sameki ta kowane hali

0 Response to "Kalaman Soyayya 2025 Masu Dadi"

Post a Comment