-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman love

Kalaman love

kalaman love



Rashin ganin ki na rame bana iya cin komai. Hakika na takura sosai irin yadda na shiga wani mawuyacin hali kasancewar rashin ki a kusa dani ya habibiyata. 

Hakika na Samu sukuni kasancewar zamana dake ya habibiyata nayi rashin farin ciki a duk lokacin da ban Samu ganinki ba. Da Yawa Mutane na tambaya na gameda ta yaya muke gudanar da soyayyar Mu dalilin shine irin yadda muke rayuwa a tare babu wani sabani dake afkuwa a tsakanin Mu dake Kuma na tabbata hakan ya samo asali ne sabida kowane Mu daga ni Har ke mun rike amanar juna da amana ta gaskiya.

Nayi kwana acikin duhu kala kala amma a yanzu da na Samu kulla alaka ta soyayya dake a koda yaushe idan na shiga bacci koda acikin tsananin duhu Nike zanga ga baki daya jikina ya haskaka dakin da Nike bacci sabida zuciya ta na dauke da soyayyar ki Kuma ke mace ce wadda Allah yayima muujiza ta kyawun hali da Kuma kausassar zuciya. Ni na jima ina jiran wannan damar dama irin wada Nike a tare da ita a yanzu ta dalilin Samun soyayyar ki cikin sauki tare da kauda kai da kike yi zuwa ga Mutanen dake so su kawomin farmaki a soyayyar da muke a tsakanina dake. Akwai wani sirri da Har yanzu baki sanshi ba game da soyayyar Mu Mutanen gari da Yawa suna son suyi mana kutse Domin Samun shiga a gareki Domin Kuma kyawun halayenki kowa ke son shiga ya shiga Kuma ya fita ko ta yaya Kuma a kowane hali shiga ya mallake ki amma kash! Ke ba soyayyar kudi ce ko kyawu ko kyalkyalin Mutum ne a gaban ki ba ke soyayya kike ta amana. Sannan ni nan kaina mata sunyi ta nuna ra'ayin su akaina amma na kasa basu dama suyi soyayya dani sabida soyayya ki ta Samu bagire acikin birnin zuciya ta Kuma inada tabbacin babu wata diya mace da zata Samu damar mallaka ta indai a Bangaren soyayya ne da kauna Hadi da amana ya ke masoyiyata abar alfahari na.

Banjin dadi idan kikayi Tafiyar wuni guda wadda zaki bar gari Domin a koda yaushe nafi son in kasance a kusa ga bugun numfashin ki. Na Samu bayyanar Fuskar ki a gaban idona akan haka fuskata ke dauke da wani hasken annuri Wanda a duniya kece mace ta farko da nasamu kasancewar ta a kusa dani wannan Kusanci naki da na Samu shine Silar Samun farin cikina na rayuwar duniya. Farin cikin ki babbar Garkuwa ce a gareni ya ke sahibata. Ban San yadda za'ayi a kwana a tashi kowane rana tunaninki Bai ratsa zuciyata da dukan gangar jikina ba ya ke farin cikina kin kasance mai zakin murya kamar Zuma Wanda baida sarkin suga a tare Dashi. Na Riga na fawwala ma Allah komi da duka ikonsa akan soyayyar da ke tsakanin Mu dake kasancewar ke ta daban ce a zuciyata

Banda wata mace tamkar ki dake iya gittawa a gaban idona naga ta burge ni a rayuwata ya ke muhimmiyar zuciyata banda yadda zanyi ban Samu amincewar ki daga gareni ba.

Ke nan da kike gani kin kasance ke fitilar mata ce idan kika yada kowane mace mai rayuwa a fadin duniya zata Samu alfarma wannan yadiyar ta dalilin kyakkyawan halaye ni da mutuncin ki zuwa ga Mutane duniya baki daya. Na tabbatar da tsananin karya da gaskiya akwai tazara sosai ko ince miki bazaa taba hadasu ba to wannan babban dalilin yasa na kaiki gaba a koda yaushe sabida kece babbar nasara ta a rayuwa wadda idan na sameta inada tabbacin bazan sake Neman amincewar wata diya mace acikin zuciyata ba

0 Response to "Kalaman love"

Post a Comment