Kalaman kwantar da hankali
Kalaman kwantar da hankali
A lokacin da na fara soyayya dake ya ke masoyiyata babban farin cikina in ganki jikina yana bani ke tawa ce Kuma ta Har abada Domin na Riga da na Samu soyayyar ki da amincewar ki ta fannin soyayya kinga duk wani karnin sakon soyayyar amana ke zan baiwa shi kasancewar ke yar baiwa ce dake Nike alfahari. Rashin ganinki tabbas ba karamar illah yake mini ba acikin zuciyata banda yadda zanyi in jure soyayyar da nake miki dole sai ta bayyana a idon duniya banga yadda za'ayi kiyi Tafiyar kwana bakwai banyi ciwon kwana bakwai da wuni bakwai ba. Soyayyar ki ta kai idan kika saka ma kafar ki takalme koda makwafta zaki je Hankali na bazai kwanta ba Har sai kin dawo gida sabida kowane namiji idan ya ganki dole sai ya kyasa irin kyakkyawar Surat da Allah ya baki ya ke masoyiyata abar kaunata agwalima ta haske na.
Kaunar ki a rai na ta kasance Har Ina ganin babu kamar ki a fadin duniya. Duk da na tabbatar da cewa duk matashi wata rana sai ya kasance babu tsoho idan akwai yawan rayuwa Anma ni na dauki alwashin duk yadda kikayi tsufa zanci gaba da sonki kamar yadda nake sonki tun kina yarinya yar shila. Soyayyar ki ta zama albarka a gareni ya ke gimbiyar rayuwata, banda wani sukuni Wanda yafi inganki a kusa dani duk da cewa na San mutuwa batada sabo Kuma na tabbatar da batada Tausayin kowa Kuma ita kadai na San zata iya shigi da fice tayimin tasiri Domin ta rabamu dake ke nakeson in Bawa gata a rayuwa kasancewar ke gwanina ce. Da farin Allah shi ya kamata in gode masa Domin shi ya tsaramin in soyayya ki a rayuwata Kuma rayuwata ke nabaiwa dukkan rayuwata da kalbina da duk wani ruhin numfashi na. Kin kasance Rina Kuma abar taremin kowane irin fada gaki tamkar numfashi na Kuma gaki da zakin murya kamar Zuma farar saka sakamakon soyayyar da nake miki Har na fada wani kogin da ya kai zurfin Da koda zanyi Iwo na awa daya bazan iya fidda kaina acikinsa ba irin yadda na shiga babban kogin sonki zuciyata ta Riga tayimin diskandiridi Kuma naji babu yadda zanyi in rayu idan babu ke ya farin cikin rayuwata a bar alfari na na tabbatar da yau da Gobe sai labari Domin duniya ga batada tabbas shiyasa nakeso koda yaushe ya kasance na kawo kudin aurenki ya ke gimbiyata.
Ni Kuma na San abinda duk rabbana ya yadda ya tabbata dole ko ana a bakin daga babu Wanda zashi hanashi ya tabbata hakan yasa a koda yaushe koda makiya sunyi wani yunkurin rabani dake Hankali na bazai tashi ba kasancewar na Riga nayi kogo Kuma kogon Da babu mai iya Duba shi Har ya shiga acikin birnin zuciyar Mu Domin sanin sirrin soyayya ta tsaninkmu dake ya babbar sahiba ta amanar rayuwata aminiyar da babu tamkar ta acikin matan duniya ga baki daya. Na kasance Mutum mai Hakuri Domin inga na rike soyayyar ki bisa ga amana. Kizo kibani madarar kauna mai dauke da gari Hadi da ruwan cream Wanda zai iya zama Silar idan na sha shi zanyi iya tsayin daka in zauce a kanki. Kullun kuka nikai babu magani zafi kunci ga Kuna kuni da nake tayi amma na kasa Samun ki a koda yaushe a kusa dani kinsna akwai kalubalen rashin ki a kusa dani Domin Wasu mata ko suna so na na tabbatar da kissace sukeyi Domin babu mai iya yimin soyayyar zuciya daya tamkar ki yake masoyiyar ta aminiyar rayuwata Kuma kin Riga kin zama inuwa wadda nake shiga tana ratsan jikina Kuma tabani ni'ima wadda zata karamin lafiya ga dukkan gabobin jikina.
Zanyi amfani da wannan Damar Domin zayyana miki irin so da kaunar da nake miki a rayuwata. Ya ke masoyiyata kibani Aron zoben hannunki Domin in sanya shi a nawa yatsan hakan sai ya kara tabbatar min da cewa an Riga an zama dai. Koda zan mutu bazan daina sonki a rayuwata ba duk da kinga na daina sonki tun randa kikkace baki sona kuma ke kika luraddani komai zanyi idan babu ke tayaya zanyi rabauta yake gumbiyata
0 Response to "Kalaman kwantar da hankali"
Post a Comment