-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Idan Kana Da Takardar Sakandare, Ga Yadda Zaka Cike Aiki a Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS)

Idan Kana Da Takardar Sakandare, Ga Yadda Zaka Cike Aiki a Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS)

Idan Kana Da Takardar Sakandare, Ga Yadda Zaka Cike Aiki a Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS)

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta sanar da guraben aiki na Customs Assistant Cadre ga ƴan Najeriya masu sha’awa, tare da kammala rajista kafin 2 ga Janairu, 2025.  


Sharuɗɗan Cancanta  

1. Dole ne mai nema ya kasance haifaffen ɗan Najeriya.  

2. Ya mallaki Lambar Shaidar Ɗan Kasa (NIN).  

3. Bai da tarihin aikata laifi ko bincike akansa.  

4. Ya kammala makarantar firamare tare da samun takardar First School Leaving Certificate.  

5. Ya mallaki sakamakon O’Level (WAEC ko NECO) mai inganci.  


Lafiya da Jiki  

- Dole ne mai nema ya kasance yana da cikakkiyar lafiya ta jiki da kwakwalwa.  

- A bayar da takardar shaida daga asibitin gwamnati.  


Sharuɗɗa na Gabaɗaya  

1. Tsawon maza bai gaza 1.7m ba, mata kuma 1.64m.  

2. Ba za su kasance da nakasa ko cuta mai tsanani ba.  

3. Ba za su kasance mambobin kungiyoyin asiri ko masu amfani da miyagun ƙwayoyi ba.  

4. Su kawo takardar asalin jiharsu ko ƙaramar hukumar haihuwarsu.  


Yadda Ake Nema  

A ziyarci shafin yanar gizo: http://recruitment.customs.gov.ng/apply

A tabbatar da cikakken bayani kuma kada a yi rijista fiye da sau ɗaya don guje wa haramcin shiga takarar.

0 Response to "Idan Kana Da Takardar Sakandare, Ga Yadda Zaka Cike Aiki a Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS)"

Post a Comment