-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

ZAMAN BUDURCI

ZAMAN BUDURCI

ZAMAN BUDURCI

Da Farko Kalmar Budurci ta Diya Mace ce Kuma kowace 'Ya Mace ana son tayi Budurci mai kyau Kuma mai amfanin ta Ta hanyar Tsare mutuncin ta, Tsafta, Biyayya Ga iyayen ta, Dauke Ma Mamar ta Wasu Ayukkan Gida Kamar irin su Shara, Wanke-Wanken kayan Abinci, Girki, wanke ma mamar ta kayan ta Na sakawa tare da kwaikwayon Wasu Halaye masu kyau Na Zamantakewar Aure daga mahaifiyar ta a fannin mu'amalar ta da mahaifin ita budurwar. Daga nan zata fara sanin mi nene rayuwar auratayya tun gabanin tayi aure.


Fannin Neman Ilimi a wurin mace budurwa; Yanada Kyau ga budurwa ta nemi ilimin muhammadiyya da Na zamani Domin ta Samu Jin dadin Mu'amala Da Mutane Kuma Da gidan auren ta. Idan Zaki nemi kawaye a wajen neman ilimi kuma Kika Fahimci kin kai matakin zama budurwa Yanada kyau duk wace kika hadu Da ita ya kasance Kun San Gidajen junan Ku Kuma ki gabatar Da ita a wajen mahaifanki Domin su San Waye ita Kuma suwaye asalin iyayenta. Hakan Zai Kara kare Budurwa Daga shiga wani Halayyar banza Da ake dauka daga miyagun abokani. Da Yawa Akwai Yaran Da Zasu taso basuda Home training (Tarbiyyar da ake Samu daga gida) tun daga nan ake Samun mummunar Dabi'a wacce yarinya ta Dauko daga gidansu sai Kuma ke Ki biyema rayuwar ta. Wata Budurwa daga ganin irin yadda take mayar wa malami magana daga nan zaki Fahimci cewa bata Samu tarbiya daga gida ba. Irin wadannan Kuma idan kika biyema zama tare dasu a Matsayin Kawaye daga karshe kema Zaki Samu Kanki a Matsayin wacce Zata yi hasara ta Rayuwa Domin A wannan lokaci da kawayenki ake yi miki shaidar ke abar kwarai ce. Ko akasin Haka.


Ta Fannin Mu'amala Da Mazaje idan an hadu a makaranta; A Matsayinki Na Budurwa Yanada Kyau ki Kiyaye wadanda zaki yi Zamantakewar yau Da Gobe dasu Domin Tseratar Da mutuncin ki Sabida Da Yawa Wasu Dalibai ba karatu ke kawo su yi a makaranta ba bata gari ne Wasu Kuma A gidajen su an kasa yadda za'ayi dasu amma sun gagari iyayensu Sai a yanke shawarar kaisu makaranta Domin gyaran tarbiyyar su a makaranta. Irin wadannan mazaje idan kin lura zasu nemi shiga cikin rayuwarki ta hanyar kyautata miki Acikin makaranta Haka Kuma Babu wacce suke so suga sun batawa rayuwa kamar Kamilar budurwa. Zaki ga Suna Yi miki Wasu maganganu Na dadin baki tare da zolaya kamar haka: Hajiya An shigo Jiya karatun da aka yimana Ban gane abinda Malam ke koyar damu ba amma Na San ke kin Fimu ganewa sabida haka Na zo wajenki Domin Samun tubarraki wajenki tare da yimaki murmushi😄😄, Ko Kiji Sunce Aunty Hauwa ya gida kin San Ku manya ne dole muyi Kokarin kulla alaka daku daga nan Matsayin ki Na mace budurwa kiyi masa tambaya wace irin Alaka zata hadani dakai ina mace kana Na miji? Daga nan zaki Fahimci wani Abu a fuskar sa Domin baida wata gamsasshiyar amsar Da zai baki Na wannan tambayar daga karshe shine zai sanar Da sauran miyagun abokaninsa wacece ke Kuma kowa zaiyi Kokarin Shigowa Sabgar ki.


Bangaren Girmama Mutanen dake gaba dake A Matsayinki Na budurwa; Yanada kyau duk wani Wanda ke gaba gareki tun daga gidanku, Makwabtan Ki, Mutanen anguwar Ki kasance kinada kyakkyawar Mu'amala Dasu Hakan shi zai sa Idan wani ya zo Neman auren ki babu yadda za'ayi Wani Ya kawo suka a gareki saidai shi kawo gyaranki a gaban Wanda yazo Neman ki. Haka Kuma irin wadannan Mutanen su suka San waye ke sabida haka ba zasu bari wani mai muguwar Halayya Shi Samu Neman aurenki ba Kinga tun daga nan Halayyar ki tayi miki garkuwa ga rayuwar ki.


Rayuwar Mace budurwa tare Da kannenta a gida sai mace ta jure ta Saka hakuri Tsakaninta Da kannenta. Budurci Na da bukatar kauda kai ga kanne tare da hakuri dasu yayin Zamantakewa Acikin gida. Mace budurwa Na dauke Da jarabawa musamman lokacin Al'ada Yanada kyau mace ta kiyaye tun kamin Al'ada tazo Mata ta tanadi tsaftataccen Kyalle Mai Yawa Wanda ba'ayi amfani Dashi ba Domin kare kanta daga cututtuka a Gabanta.


Mace budurwa Na bukatar Samun biyan bukata daga wajen iyayenta gwargwadon Halin iyayenta Domin gujema fadawa wani hali. Budurwa Na bukatar kulawa daga wajen iyayenta ta fannin daukar mata mataki wajen cin ta, shan ta, sutura ta tare da Dawainiyar ta idan batada lafiya.


Haka Kuma budurwa Na da bukatar Kawaici tare da killace kan ta daga shiga gidajen makwafta Hakan zai iya haifar da canza tunanin ta Da tarbiyar ta da ta Samu a gidan idan akayi rashin sa'a kila wannan uwar dakinta Da take makwaftaka da ita batada halayya ta gari wannan Na janyo dalilin bata mata rayuwa.


Wannan shine takamammen bayani game da yadda mace ke zaman budurci.

0 Response to "ZAMAN BUDURCI"

Post a Comment