-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Zafafan Kalaman Soyayya Masu Dadi

Zafafan Kalaman Soyayya Masu Dadi

Zafafan Kalaman Soyayya Masu Dadi 

Assalamu alaiki farin cikin rayuwata. Kina Dauke da soyayyar zuciya ta Kuma kin sakata a lokon da bazan iya hangota a zuciyar ki ba koda an fasa tsagin cikin zuciyarki.


Tun ranar da muka hadu dake Na shiga wani kyakkyawan yanayin jin dadi da annushuwa ta dalilin haduwa da farin cikin zuciya ta wato ke saurauniya ta Abin alfahari na.


Na jima a rayuwata tun lokacin da nazo duniya banga kyakkyawar halitta irinki ba. Kin mamaye duk Wasu sinadaran da nake numfashi dasu acikin zuciya ta ta dalilin so da kaunar ki sunyi dafifi akowane kusurwa na zuciya ta.


Kash! Ash! Wash! Kibiyar sonki ta kama ni a maimakon in jiyo inga jini daga nan sai Na hango tuwon so, miyar so, aka kwashe ni aka kaini asibitin so likitan so ya zo ya auna ni yace inada ciwon son ki Kuma ke kadai ce magani a wurina.


Ina cikin juriya tare da fargabar rasa ki a kusa dani sabida Muhimmanci ki a wurina masoyiyata. Kina burgeni, kalaman ki Na burgeni yar dagwas-dagwas. Rashin ki a kusa dani tamkar fura ce wacce batada nono, tamkar makaranta ce wacce babu dalibai acikinta, tamkar makaranta ce babu malamai Acikin ta, tamkar masallaci ne Wanda babu masallata acikin sa, tamkar gida ne wanda babu kowa acikin as, tamkar office ne wanda babu mai shi acikin as. Tamkar fitila ce wace babu haske agareta, tamkar ruwa ne Wanda babu fidda kishi acikin su, tamkar shayi ne wanda ba ruwa ba shuga acikin sa, tamkar gari ne wanda babu kowa acikin sa, tamkar fadama ce wacce babu lambu Acikin ta, tamkar salula ce wacce baa kiran kowa Kuma kowa bai kiranta, kamar kofa ce wadda babu mai wuce wa a gareta, tamkar titi ne ko godabe wanda babu mota ko Babur ko keke mai wucewa agareshi. Wannan shine misalin rashin ki a kusa dani ya ke Abin alfahari na, agwalima ta, zaki na.


Na fuskanci farin cikin rayuwa yayin da Na hadu dake yake abar bege na. Da inada dama da Na dauke ki mun shiga kogi da koramu masu dauke da gagarumin sanyin soyayya domin mu kwashe lokaci aciki muna gudanar da so da kauna cikin aminci da soyayyar juna a tsakanin mu... Na shirya bada lokacina, dama ta da duk wani abinda nake Dashi Domin saki cikin hasken farin ciki da walwala yake masoyiyata Abin kauna ta.


Na yafe ci da sha da sutura da sauran ababen more rayuwa domin in samu Karin yaddar ki da samun karbuwa daga wajen ki ya ke wadda aka halitta domin ni annurin rayuwata sanadin jin dadi na, rijiyar da nake debo ruwan kauna domin nasha naji dadin so zuwa gareki.


A kanki na jure duk wata gwagwarmaya ga sauran mazaje masoyanki domin in samu yaddarki cikin sauki kasancewar kece lailatil kadari na idan na ganki na san na Riga na dace. Babu wata diya a doron kasa wacce zan so kamar ki Kuma ke kadai ce aka yo Domin inso ta Kuma ke kadai zanci gaba da so babu ragi babu kari yake aminiya Kuma muradin zuciya ta.


Mutane na soyayya amma banga soyayyar jini kamar irin soyayyarmu ba Domin ita tamu ta kunshi amana, yadda, Mika wuya, aminci tare da kaunar juna tsakanin Mu sabanin sauran abokaina da nake tare dasu. Idan naji wani na labarin soyayyar sa tsakanin su da budurwa sa sai inga yana bani dariya dalili shine ko ansamu namiji kamar Irina mai irin hali na, mai irin siffa ta, mai irin tunani na, mai irin sutura ta, mai kama da yanayi na to ba za'a taba samun mace kamar ki ba wannan shine ke tayarma Al'ummar garinmu Hankali tare da sauya tunin su.


Inason ki zama Zuma ni Kuma in zama madi domin mutaru mu hada Mu saka acikin fura ta kauna mu baiwa masoya kowa yasha domin suyi kwaikwayon soyayyar Mu. Na so in samu lokaci acikin lokutan da muke dasu a duniya daga ciki hadda lokacin dare sai naci gaba da baki lokacin na irin yadda bazaki ganni nesa dake ba. Kinada Matukar Muhimmanci a wurina, kaunarki ta zamo min ciwo ta sakani hauka yanayi na da hankali duka sun gushe ta dalilin ki. Don Allah idan har kinyi min kafi ko sihiri kiyi Kokarin neman hanyar sassauci sabida na riga na zautu ban ganin kowa sai ke. Idan ina aiki ke nake gani, idan ina bacci ke nake gani, idan nashiga toilet ke nake gani, idan ina wanka ke ce nake gani ya ke mai sanyaya raina aminiyar ruhina Kuma Garkuwa ajikina

0 Response to "Zafafan Kalaman Soyayya Masu Dadi"

Post a Comment