-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YADDA AKE TUWON MASARA

YADDA AKE TUWON MASARA

YADDA AKE TUWON MASARA

Da Farko Za'a Debo masara a cire duk wani datti da take Dashi sai a fyace ta akai wurin surfe, bayan an surfe sai a wanke masarat ta fita da kyau daga nan sai a shanya masarat idan aka bata lokaci kamar mintuna ashirin haka ko talatin sai a sakata a bokiti ko Kuma buhun jikka na bagco aje akai nika bayan an nike sai asamu tukunya a wanke sai a Dora ta saman murhu a zuba ruwa gwargwado garin da ake dashi sai ka Jira ruwan idan aka fahimci ruwan ya tafasa sai a saka garin amma ba duka ba. Sai a rufe tukunyar abada lokaci bayan Wasu yan mintuna sai adawo a bude sai a dauko wannan sauran Garin da aka rage akama motsa na cikin tukunyar ana karawa da wannan ana yin dauri Dashi bayan an kammala haka sai a rufe tukunyar akoma bada wani lokacin sai idan aka Fahimci yayi sai azo a tuka tuwon daga baya idan aka gane ya hade yayi tsauri sai a nemo roba karama ana amfani da ita ana kwashe tuwon

0 Response to "YADDA AKE TUWON MASARA"

Post a Comment