-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YADDA AKE TUWON MASARA

YADDA AKE TUWON MASARA

YADDA AKE TUWON MASARA

Da Farko Shi tuwon masara tuwo ne Wanda Mutanen kabilar Hausa suka fi tu'ammali dashi sannan ga yadda ake yin shi kamar haka:


A Samu masara wacce ta bushe sai a kaita wajen masu surfe, bayan an surfe tsabar masarat sai a wanke ta fes a shanya tsabar masaran tasha iska abata lokaci. Daga baya sai akaita wajen nika. Bayan an nika sai azo da garin masarat a tankade shi shiyi laushi sosai, Sai a aza ruwa saman wuta a cikin tukunya sai a jefa kanwa kadan a ciki a rufe tukunyar, idan ya tafasa sai a samu wuri daban a dibi garin masara a kwaba da ruwa kar yayi kauri sosai Kuma kar yayi ruwa sosai. Sai a dauko hadin garin a zuba acikin ruwan masu tafasa ana juyawa da muciya kar yayi gudaji Amma Za'a rage wutar idan yayi kauri sai a rufe abashi lokaci ya dahu.

Idan ya dahu, sai a raba biyu, a zuba Rabin a wani wuri a ruhe a kuma bar Rabin a tukunya a tuqa ana zuba gari kadan kadan ana tuqawa har kaurinshi yayi  sai a yayyafa ruwa a sama a ruhe ya qara dahuwa, idan ya dahu sai ki dauko wancan Rabin talgen da Kika aje ki zuba acikin ki tuqa sosai sai ya hade ki qara mintoci kadan ki sauke Amma kar ki Bari yayi qarhi a Yishi da laushi, sai a kwashe aci da miyar da akeso 


Wannan shine bayanin yadda ake tuwon masara

0 Response to "YADDA AKE TUWON MASARA"

Post a Comment