SOYAYYA RUWAN ZUMA - Kalaman Soyayya Masu Ratsa Jiki
SOYAYYA RUWAN ZUMA - Kalaman Soyayya Masu Ratsa Jiki
Hakika ke Jan zaki ce acikin birnin zuciyata kin zama maliya badda na kogo. Inason Allah ya nunamin ranar da zan zama ango ke ko kizama amarya in zama anginki banda tamkar ki acikin mata. Da farin na fara sallama inda zuciyarki tasa nazan Tunga. Kalma taso za na bayyana miki naki ne tasa naja damba yarda dani kada ki sakeni ya ke masoyiyata. Daga kauna aminci ke faruwa dama zaki bani damar yin ambato kalmomin da kike gayamin idan ina tunasu sai inji Hankali na ya fita daga gareni. Na shirya yakar zuciyata tare da yimata duk wata barazana Domin kada ta kuskura ta kasa tunaninki duk bayan mintuna. A koda yaushe ban iya jure mafarkin ki Domin babu wani Dare da zan kwanta mafarkin ki baizo minba. Akoda yaushe idan nayi sallah banda abinda nake rokawa kaina sai kasancewa tare da sonki da kaunar ki. Babu shakka kin ratsa jikina kin shiga zuciyata ruhina dakuma kalbina yake abinso na muradin zuciyata. Zuciya ta da taki ta kasance tamkar hasan da Hussaini kasancewar soyayyar Mu da shakuwa Da muka jima munayi ni dake a tare yake masoyiyata. Kareki manta dani masoyiyata Garin masoyiyata baya nisa akanki ba abinda zani kasa, idan na furta labarinda ke zuciyata na tabbatar zaki gasgata soyayayyar da nake miki nafi son ki sakani aranki koda babu raina bazaki iya mantawa daniba, idan Har uwa tana iya mantawa da yaronta to tabbas zan iya mantawa dake a rayuwa. Ba Domin mutuwa ba dani dake bazamu rabeba, kasancewar ke ta dabance a zuciyata masoyiyata Abin alfaharin rayuwata, kin sacemin zuciya ta gaba daya. Babu Shakka na gamu da barauniyar zuciya ta wadda ta tafi da zuciyata nayi yunkurin shiga duniya Domin nemanki babu Inda naji labarinki. Kin sace zuciyata ba yadda zanyi in ganta na Riga na zamto Mutum Wanda bai iya tabuka komai sabida sonki ya shige zuciyata ya narkarda ita koda yaushe kinaimin gizo a fuska yake masoyiyata. Abokanai na sukace in hakura dake amma na kasa hakura Domin ba karamin kalubale bane agareni, wata rana sai in dinga tafiya ina waiwaya sai naji tamkar muryarki ce a bayana. Masoyiyata juyo ki ganni gani a bayanki na tabbatar da idan kika rikeni a zuciya dole kisamu kulawa uwar Yarana. Inason duk rintsi ki rike alkawalin Mu. Ki amshi zuciyata ki ajemin ita na San zaki iya yimata gata duk cikin matan duniya ni dake Bama rayuwa muzama tamkar uwa da yayanta sabida haka alkawalin Mu nakeso komai wuya ki rikeshi. Duk inda zaki jani ki kaini ga hannuna ki rike Domin zan iya share miki hawaye bazan dauki zugar Kawaye ba duk girman zuciyata ta kasa daukar komai acikinta Wanda bai shafi soyayyar kiba ya habibiyata. Lalle kinmin satar da bazan taba iya Maye gurbin abinda kika rabani da ita ba wannan Abin da kika sacemin ba komai bace face zuciyar tawa. Da zaki ji abinda nake ji acikin zuciyata da kin Tausamin Mutane sai cewa suke banida Hankali sai wata rana idan na jiyo Da in wauwaya koda zan ganki Ashe zuciyar tawa ce ta zauce aranki. Wata rana ina kan hanya ina tuka motata nan take na fara sambatu akanki kadan da na afka acikin daji sai zuciyar da ke dauke da sonki itace ta ankaraddani. Zan rayu dake zan mutu dake tabbas dani dake zamu zauna, kece na hango na biyo ta bango Domin Samun haduwa dake ya ke habibiyata Abin alfahari na. Zuciya ta da taki abokan juna don basu rabuwa ko a hanya. Da akwai Wanda zai tsaga jinin jikina da yaga yadda naka yake gudana acikinsa. Idan nace ni ina nufin ke haka Kuma idan nace ke ina nufin ni. Lalle ni dake mun dace ya ke abar sona makamashin rike hura wutar zuciyata wacce ita nake bege akoda yaushe. Na yadda dake Kuma ke na baiwa sirrin zuciyata idan na sameki na dace. Koda magani indai soyayya ce taki bazan bartaba koda baturiya tazo agaban idona bazan kalleta ba, ina alfahari indai soyyace ce baza a fini ba indai ruwan idanuwa nane babu mai sakasu face ke. Sanin sirri Yanada kyau amma idan aka bayyana shi, kasancewar rikon sirrin da kikemin shiyasa ake ganin zamana dake mun dace. Ashe soyayya haka take da zafi? Ashe zafinta yafi garwashin wuta zafi. Ina kike masoyiyata na Duba gabas na Duba yamma kudu da arewa amma banganki ba. Nayi ta soyayya kala_kala Amma Har yanzu banga irin tawa da taki ba haka Kuma naga yan mata kala kala iri daban daban Amma banga irinki ba, soyayya sa'a ce haka Kuma ni na dace. Babu abinda zanyi babu ke Domin kin iya kwalliya ga kyau ga kunya ga haiba sannan ga kwalliya da kike yi ko yaushe hadda mata suke zuwa a wajenki Domin suyi koyi da irin kwalliyar ki Domin suyiwa masoya. Dani dake soyayya ce tsakanin Mu Kuma mutuwa ce kadai zata raba babu sukuni idan banganki a kusa daniba alkawalinmu na nan kamar yadda muka dauka. Na San kin kula dani a soyayya Wanda kushe da hassada baisa kika rabu dani ba Kuma idan ga halicci ba yadda za'ayi inyi tunanin in rabu dake ya habibiyata aljannar duniya ta. Yau ni gane soyayya ba kudi bane Kuma ba wuta bace sannan soyayya ba mulki bane ba sarauta bane idan kudi ne na San bazaki soni ba Kuma idan kyawo ne bazaki soni ba amma Allah ne Kawai yayi nashi tsari a wannan nahiyar duniya
0 Response to "SOYAYYA RUWAN ZUMA - Kalaman Soyayya Masu Ratsa Jiki"
Post a Comment