-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Sabin Kalaman Soyayya Masu Dadi

Sabin Kalaman Soyayya Masu Dadi

Sabin Kalaman Soyayya Masu Dadi 

Soyayyar Mu ni dake ta kasance Abin misali a kowace nahiyar duniya Duba da yadda muke saffara soyayyar Mu ni dake kamar laila da majanun wani sa'ilin ma muna gudanar da ita kamar tamkar nine romio ke ko juliyat. Na tabbatar da cewa babu wata rana da zata wayemin acikin kwanakin rayuwa ta ba tare da zuciyata tayi bugu Har sau Hamsin ba a dalilin so da kaunarki da take dauke Dashi yake tauraruwa mai haskaka ruhi tare da kalbin zuciyata. Kin zama mazurari wanda ake amfani Dashi a sakamin soyayyar ki a kullun kamar yadda ake amfani Dashi wajen awon mayuka, ke ce lalurar da akemin a kowane wuni Domin Samun saukin daukar soyyarki da tayi dafifi ta mamaye kwalakkwason zuciya ta tare da hana ma zuciya ta Samun isasshen jini Wanda zai taimaka mata ta fannin bugun da takeyi tana Isar da sako ga jijiyoyi na Domin Samun motsi da kuzari mai kyau. Kece farin cikina, natsuwa ta, kirishma ta a idon Mutanen da ke zagaye a doron kasa ta fannin kyalkyalin fuskar ki da kyawawan halayenki zuwa ga Al'ummar duniya. Kece ta farin Kuma kece ta karshe ga Manyan matan duka duniyar nan yake aminiyar raya koramar ruwan zuciya ta. Ban taba tashi da wata mace a zuciyata face ke ba.


Kin hana ni bacci kin hana ni sukuni kin yimin katutu akan makwallaton zuciya ta, idan na tuna ranar da zata fito a kullun sai inga kamar akwai gizon ki Acikin wannan ranar ta kowane wuni ko kinsan miyasa nake ganin haka a kullun? Kasancewar ke haske ce Kuma ke fara ce wannan dalilin yasa nake tunanin dake ake amfani Kuma da hasken fuskarki rana ke Samu tana haskawa Al'ummar duniya a kowace rana idan Garin Allah ya Waye haka Kuma idan dare yazo sai in tsaya a tsakiyar wurin Da ba kowa Domin hangen kowace tauraruwar dake a sama koda zanga hazonki Acikin wannan taurarin amma kash! Ashe zuciya ta Kawai ke raya min hakan sai gangar jikina ta kwashe ni zuwa wannan tunanin da baya karewa a gareni. Ban taba gardama da kowaba sai ta dalilin ki. Wani ya gayamin cewa babu wata mace tamkar wacce yake so a wannan doron kasa ta duniya da muke ciki a wannan zamani da muke ciki a yanzu duk da yawan kyawawan matan da suka mamaye duniya amma shi a nan ya nuna son kai zuwa ga gimbiyar sa. Nan take nayi musu tare da nuna rashin yadda da akwai wata mace a fadin duniyar nan mai dauke da irin kyakkyawar siffar ki, Da fuskar ki, da bakin ki, da hancin ki, da kunnayen ki, da hannuwan ki da leben ki, Da kafafuwanki da faratunan ki Na yatsar kafar ki da hannayenki zai yi wuya a Samu wata ya mace mai irin wadannan abubuwan da Na lissafa game dake Domin ke mace ce wacce Allah yayima tata halitta ta daban wadda ba Wani Na miji a duniya Wanda bazai ji son yaga ya kasance tare dake ba. Ta dalilin haka Na kara Samun abokanai masoya da Kuma Karin son a kusance ni sabida babu wani sarkin dake Saman sarautar da yafini sarauta a yanzu Kuma kece kika jamin wannan girma Da kima ba bainan nasi.


A lokacin da nake tashi daga bacci Na a kowace Safiya, banida wani buri a sassan zuciya ta face inyi ido biyu dake in ganki, Domin cutur sonki ta Riga da ta kamani Kuma banida wani magani da zan sha Domin Neman waraka face Samun kulawar ki zuwa gareni. Kulawar ki a wurina tamkar gidan sama ne Wanda akayi shekara sama Da goma ana Gina shi Domin a inganta shi, Samun kulawarki a wurina tamkar wani bango ne Wanda ya tsake Kuma wannan tsagewar bai fi girman yatsa ba amma aka tanadi Jikkunan siminti kwara Dari da arba'in da biyar da yashi Tifa Hamsin da Tsakuwa Tifa Hamsin, mesin Mutum goma sha biyar, leborori Mutum Hamsin da biyu Domin a taru a rufe wannan bangon da ya tsage don a kara inganta shi, Samun ki a kusa dani tamkar Mutum ne Wanda yana jin yunwa Har tsawon kwana da wuni bai ci Abinci ba sai a tanadar masa da ruwan zafin Lipton masu Dimi tare da saka madara laya kwara Hamsin tare da yimasa farfesun gurayen kaji a aje a kusa Dashi idan ya gama shan ruwan shayi sai ya fara afka wannan farfesun Acikin cikin sa wannan ba karamin cetonsa akayi ba kuma bai ki gobe haka ta sake faruwa ba to haka kusancin ki yake Da Matukar Muhimmanci a gareni yake kasar da nake takawa Domin inje in Isar da sakon zuciyata zuwa ga lailatil Qadrin zuciyata Da ruhina.


Babu shakka idan zan Samu kasacewa dake na har abada da dukkan samarin duniya zanfi kowa samun farin ciki da rayuwa mai kyau wacce take dawwamammiya ta Dalilin Babban rabon da nasamu daga wajen mahaliccina Kuma zanyi Kokarin tashi a kowane sulusin dare in gudanar da nafiloli masu Yawa tare da fadawa da zikirorin Ubangiji ta'ala Kuma in Isar da godiya ta ga rabbi samawati wal ardi da yabani babbar kyauta wadda tafi dacewa dani. Hakika kowane lokacin ina cikin Matukar farin ciki idan nayi wani nazari gameda kalam da kike min na Fatan alheri tare da yimin fadakarwa Domin inji tsoron Allah Kuma in kawar da kai ga duk wani Abin ki kamar su; Giba, chacha, gulma, rada, annamimanci, zina, girman kai da dai sauran duk wata alfasha da Allah ya hanemu da aikatawa. Hakan ke kara sakamin kaimi ta fannin kara saka soyayyar ki a zuciya ta Domin ta zama min Garkuwa agareni tun daga nan duniya Har lahira. Idan lokacin zafi(bazara) yazo koda Na shige bacci idan naji Na kasa kwana ta dalilin zafin da ya haddabe ni Da Na tuna da kyakkyawar fuskar ki sai inji yanayin sanyi mai ni'ima ya ratsa jikina nan take sai bacci ya kwashe ni, idan Na kwanta bacci a lokacin sanyi duk yadda sanyin nan ya haddabeni ya Hana ni sukuni Da na tuna da kyakkyawar fuskar ki sai inji wani Dibi na ni'ima ya ratsa ni sai wani baccin dadi ya kwashe ni a nan take, idan ina kan hanya ta a lokacin damana koda ruwan sama sun tsareni a wurin da ba gidanmu ba Dana tuna kyakkyawar fuskarki sai in kama hanyar zuwa gidanmu ba tare da naji bugun ruwan da ke sauka ba Har sai na isa gidanmu. Bazan daina sonki ba Har sai juma'ar da bata da assabar, bazan daina sonki ba daga nan Har assabar dinda batada lahadi, bazan daina sonki ba daga nan har lahadin da batada litinin, bazan daina sonki ba daga nan Har litinin da batada talata, bazan daina sonki ba daga har zuwa talatar da batada larba, bazan daina sonki ba daga nan har larbar da batada alhamis, bazan daina sonki ba daga nan Har zuwa alhamis dinda babu juma'a. Idan kikaga na daina sonki to numfashi Na ya tabbatar min da cewa ya daina bugawa ma'ana na mutu amma ko babu zuciya ajikina hanta ta zata rike soyayyar ki, idan ma babu hantar a jikina to huhu Na zai rike soyayyar ki, idan ma ba huhun kododi na zasu cigaba da rike soyayyar ki, idan ma sun daina Aikin akwai hanji na sune zasu rike soyayyar ki. Kai ina ma ace gangar jikin Mutum na iya rike soyayyar masoyiya ita kadai ai da na Mutum rike da soyayyar ki sarauniya Abin yabon zuciya ta. Ban taba yima wata budurwa tanadin kaina kamar yadda nayi miki ba na kurbin sonki a babban kofin Lu'u lu'u Kuma yayi tasiri a birnin zuciya ta, duk wata koramar Da nake da ita Domin jin sanyi Acikin zuciyata soyayyar ki ta cike wannan wurin Har takai yanzu zuciya ta bata Samun bugawa hundred percent (Dari bisa Dari) a kowace Safiya idan Na tashi tun safe Har shafewar wuni kai harma dare yazo safiyar Allah ta Waye.


Kin zamto mota ga wannan zuciya tawa domin tukawa tayi tafiya mai Nisan gaske takai sako zuwa ga zuciyar masoya Domin su amfani wannan soyayyar tamu, kin zamto Babur ga zuciyata Domin daukar buhuhuwan sakon masoya Domin su Isar Dashi zuwa Garesu tare da sauke nauyin da zuciyar ta daura masa zuwa ga duk masoyan juna guda biyu namiji Da mace. Kin zama keken zuciya ta Domin wana shi ayi zagayen gari ana zagayar zucciyoyin masoya daban daban Domin kara ma so da kauna tasiri ga zuciyar duk Wasu masoya masu kaunar juna. Ke takalmin zuciya ta ne wadanda take amfani dasu ta isa gari daji tare da zuwa ziyara gidajen duk Wasu masoya masu jin su masoya ne na gaske.

0 Response to "Sabin Kalaman Soyayya Masu Dadi"

Post a Comment