Kalaman Soyayya Masu Sanyaya Zuciya
Kalaman Soyayya Masu Sanyaya Zuciya
Bakida tamka a zuciya ta da zaki zama toka ni Na kasance sabulu da Mu hadu mun zama masu wanke duk wani dattin soyayyar duk Wasu masoya masu numfashi a doron kasa Domin idan mukayi haka zamu zama Abin misali ga Al'ummar duniya a Bangaren so da kauna. Da zaki zama zare ni na zama allura da mun taru mun dinke duk wata soyayyar dake rawa ta wannan duniyar tare da yimata garambawul mafi inganci wadda bazata sake yagewa ba. Da zaki zama siminti ni Kuma in zamo yashi da mun hadu munyi gini a kowace zuciya ta masoya tare da yimata kankare na dakin irin Wanda ko Shikara Dari da talatin da bakwai za'ayi bazai taba tashi ba daga kowace zuciyar namiji da mace. Da zaki zama toka ni Kuma in kasance lemon tsami Da mun hadu wuri daya mun shiga acikin cikin masoya domin yimusu maganin duk wata cuta mai hana so Samun sukuni. Na Dade ina ta jure soyayyar ki tun ina Yaro karami. Ina ajin farko a firamare nake karatun darasi Wanda ya shafi soyayyar zuciyar ki, ina karatu a aji na biyu a firamare na hadu da darasin soyayyar ki, ina karatu a aji na uku firamare na hadu da darasin soyayyar ki, ina karatu a matakin aji na biyar Na hadu da darasi mai dauke da soyyarrki, ina karatu a aji na shida na firamare haka na hadu da darasin soyayyar ki a nan Na gane yana cikin jadawalin kowane karatu da zan tunkara na zamani. Nayi zaton da na kammala firamare na gama da wannan darasin sai gashi Na isa a sakandiri a matakin aji daya na sakandiri a Matsayin darasin karatu na gameda ke, haka sai gani a matakin aji biyu na sakandiri na hadu da darasin soyayyar ki, ina kai matakin aji uku a sakandiri sai gashi Kuma na hadu da darasin soyayyar ki, ai kuwa koda aka saka mana ranar jarabawa ta junior leaving sai gashi anyi mana tambaya gameda darasin soyayyar ki ai kuwa nine Mutum mafi Samun sakamako a wannan shekat da aka rubuta jarabawar kasancewar kaina da ya Riga ya bude na zama Dan baiwa ta dalilin karatun darasin soyayyar ki yake muhibbatina na Riga da na zama majanuni game dake, sai gashi na taka matakin senior section sai gashi ina matakin aji na daya still(Har yanzu) na hadu da darasin soyayyar ki, ina gama wannan matakin sai gashi na isa aji na biyu na Kuma hadu da darasin soyayyar ki, hakama na isa matakin aji na uku a Matsayin siniya sai gashi na hadu da darasin soyayyar ki, ana cikin wannan yanayin nazo rubuta jarabawar zuwa babbar makaranta kamin isa kwaleji sai ga tambayoyi gameda darasin soyayyar ki nan take na amsa kowace tambaya Domin duk lokacin da aka yimin tambaya ta darasin da ya shafe ki kaina ya kasance budewa shike sabida kirishma da nasibi irin naki yake taliyar da nake ci Domin insamu inzali Wanda Zai taimakin wajen gudanar da aiki na kowane iri na yau da kullun
Ke ce kika kasance famfo Wanda ke janyo ruwa ya dauke su ya Isar dasu a gidajen masoya da kauna da Lumana tare da Bawa kowane lambun dake cikin gidan Domin yabashi ya girma a debeshi a baiwa masoya Gudummuwa Dashi Domin Samun girma da daukaka hadda nasibi na rayuwa ta kowane fannin rayuwa ta duniya. Banida wanta hanya da nake bi takaini masauki face igiyar soyayyar ki ita kadaice zata yiman garkuwa dakuma ninzami zuwa wajen da muke so Mu isa. Babu hayakin da zai taso ya turnukewa a sansanin wuri da zai hana idanuwa na su hango fuskar ki yake abar bege na. Kin Kai matakin da idan za'a iya amfani da bindiga a halbo harsashi ya zama dole inyi Kokarin gitta ma wannan harsashe Domin in Kareki daga afkuwa daga musibar wannan harsashi
0 Response to "Kalaman Soyayya Masu Sanyaya Zuciya"
Post a Comment