kalaman soyayya masu dadi da ratsa zuciya 2025
kalaman soyayya masu dadi da ratsa zuciya 2025
Soyayyar dake tsakanin Mu ta Riga ta wuce tunanin kowa duk wani mai tunanin soyayyar su zata iya kai ga tamu soyayyar to ya yaudari zuciyar sa Kuma shinada gajeren tunani na dambala da rashin kan gado na rayuwa Domin ke idan ana soyayya dake dole ta banbanta irin yadda kike gudanar da soyyyarki acikin hasken zuciya da mutuntawa tare da karamci irin Wanda ake baiwa masoya sunajin shauki a zuciyar su.
Kibiyar ajali ma ta kasa isowa a Garemu Domin tana jin tsoron yadda muka hada kawunan Mu muna baiwa junan Mu kulawa shine take gudun kada ta sauko tayi batan bakatatan Kuma bata Samu yadda takeso ba a fannin sukar Mu a Matsayin Mu na masoya na tabbatar da zata yi tsoron tunkarar Mu a rayuwata Domin ba karamin kalubale bane gareta taji cewa zata iya dauke daya daga cikinmu Domin ta rabamu a rayuwa.
Kibiyar sonki ta soke ni akan haka nake Neman waraka amma kash! Abin yaci tura a rayuwa babu dalilin da zaisa inyi juriya akan wannan face sai kin bani maganin soyayyar da kika sakamin Kuma kibani alluran soyayyar da kika saka min Taimakon Gaggawar soyayyar da kika sakamun sannan zanyi tunanin in mike Kuma na tabbatar da bazan taba warkewa ga wannan tabon da kika sakamin ba kasancewar ke kibiyar kaunarki idan ta soki Mutum yana jinya amma yana morema so da kauna da amana tare da kaunar juna yake habibiyata gimbiyar rayuwata Abin alfahari na dare da rana zuciyata na mararinki Kuma bazata taba daina sonki a rayuwa ba.
Soyayyar ki bazata taba gushewa ba face sai juma'a da batada alhamis ta zo, assabar dinda batada Juma'a tazo, lahadin da batada assabar tazo, litinin dinda batada lahadi ta zo, talatar da batada litinin tazo, larabar da batada talata ta zo, alhamis din da batada larba tazo. Ma'ana ranar da babu wani sarki sai Allah subhanahu wataala zai yi ikonsa Domin kowa na duniya zai kau to wannan lokacin ne nake tunanin a dakatar da soyayyar mu.
Babu shakka ni nayi dace dacen da ba wani namiji Wanda zanyi tunanin zai iya Samun kalarki yake muradin zuciyata da kalbina, baturen da yayi mota yayi mashin yayi keke hadda ma jirgi amma ya kasa Samun Matsayin da nake Dashi a yanzu kasancewar na fishi Samun sa'ar rayuwa ta dalilin Samun ki.
Hakurin soyayyar ki sanadari ne agareni Kuma na San komi Daren dadewa wannan tunanin zai amfane ni yake abokiyar rayuwata sanadin Samun farin cikin kalbi na aminiyar kasafin raya birni da karkarar kara fahintar hasken taurarin zuciya ta.
Mun wayi gari tun jiya ana yimana ruwan soyayya da kauna tare da kulawa ta fannin soyayyaya da kauna amma ina tunanin idan na fito akan wannan ruwan bazanji komai ba face damshin sare sarin sassaken annushuwa da Karin hasken da zai gudana a zuciyata ta dalilin haiba da maruba irin taki yake mai sanyaya shukar da na saka ni Kuma dasa Domin Samun ta girma tayi yado acikin zuciya ta na fara farraka tunanin duk Wasu masu tunanin zasu iya shige da fice Domin wargaza soyayyar mu.
Nayi alwashin duk wata diya mace wadda ba ajinki ba bazan bari ta ko kusanto hanyar da nake bi ba a rayuwa Domin kada ma inyi tunanin zan iya kulla wata alaka da ita koda ta mutunci ce anan take Domin duk matan duka wannan duniyar banga wadda ko a misali da zata shiga rayuwata ba ta fannin soyayyar juna da rikon amana da haduwar jini a fannin soyayya yake aminiyar kara haske da daukaka ta isa ta fannin raayi da kaunar nuna kulawa akan so ya masoyiyata abar shiga da fice na Zuma da nake sha inyi annuri a fannin gabban rayuwa ta.
Babu dole in kalli wata diya mace a fadin duniya face idan na zo wajen ki Domin Neman nuna goyon bayanki kasancewar ke diya mace ce tilo a kasar nan da muke ciki wadda soyayyar juna da amana sukayi karamci amma na tabbatar da cewa irin yadda tamu soyayyar da kaunar juna take ba take ake Samun mace mai sukuni irinki ba yake kurratul aini abinda nake kallo inji zuciyata ta faranta, tunani na ya canza ta dalilin yadda soyayyar ki tayimin katutu acikin nahiyar zuciya ta da ruhina Hadi da gangar kalbi na
0 Response to "kalaman soyayya masu dadi da ratsa zuciya 2025"
Post a Comment