Kalaman soyayya masu dadi da ratsa zuciya harda nishadantarwa 2025
Kalaman soyayya masu dadi da ratsa zuciya harda nishadantarwa 2025
Inason ki kwatanta mini yadda tasiri a zuciyar Mutum da Kuma yadda yake karuwa tare da yaduwa ga fuskar Mutane biyu. Yabonki ya Riga ya zama wajibi agareni ya kamata Ku koyar dani yadda zanyi in alkinta ki Matsayinki da nawa bazai taba banbanta ba. Tunda Har kin tabbatar da kaunace ta hadamu to kada ki biyema masu adawa sabida soyayya da akwai wuyar misali a gareta baby na. Akwai zanyi batun abinda yake canzamini ruhi gareki abar sona kin zama tauraro idan zuciya ta bata hadu da takiba banda sauran wani sukuni a rayuwata yake masoyiyata. Kibar zance makiya a soyayyar Mu Domin bazasu iya tasiri agaremu ba, idan wani ya kuskura ya aikata Sheri akanmu sai muyi Kokarin maida musu da alheri. Matan duniya suna suka Tara amma Acikin Ku ke ce Zara tauraruwa da ta tsallake samaniya a fannin so da kauna, kukana ya Riga ya kare tunda na sameki wadda Hankali na ya Riga ya kwanta gareta. Kin fi duk wata mace wadda ta gaji sarauta agidansu Domin ke taki sarautar ba gada kikayi ba a jikin ki take Domin kalarki Kawai idan Mutum ya kalla zaiji Kuma yaga cewa ya sameki koda ta hanyar maula sai yayi yadda zaiyi ya sameki. Kaddara ta kece, kece jinina damuwata Samun wurina murmushi na Kuma kece gado na mai idanu kamar madara hancinki kamar kara kizo muyi hira Domin na tabbatar da rabuwar saidai kushewa kin Samu wuri a zuciyata tunda baki makaroba ya zama dole soyayyar ki ya tabbata acikin zuciya. Ki zo ga gidana ni dake kizo muyi aure kece ta fari kece Kuma ta karshe na rufe kofa kada kisani kukan da bazan iya zubarda hawayeba sabida tsananin radadin soyayyar da nake miki. Sauko tsuntsun so sauko, wayyo Allah sauko tsuntsun so sauko wayyo Allah dawo mai sona dawo. Dawo idan kinason naci gaba da numfashi kece nafiso ke nafiso aurenki nakeso inyi kauna bishiya ce Domin idan suka sauko yayanta suna son raino to haka soyayyar da nake miki take tasiri agareki Domin babu wata diya da akeso sai ana ganin ta kai Kuma. Inason ki a yanzu da nake da numfashi Kuma ya zama dole in so ki ko banda numfashi a jikina. Na Riga na sha madaci acikin Zuma a shekarun da suka wuce amma yanzu da na sameki kinaimin maganin duk abinda ke damuna. A duniya ke kika zan farincikina idan bake wa zan Bawa kauna. Ni ke nikaima kallon sarauniya ta Domin kece cikar muradina. Idan na zauna ke nake tunani ko cikin bazara damana da rani idan na soki kema ki soni kamar yadda nake sonki. A gidan duniya rashin masoyi akwai dadi Domin idan babu masoyi babu nishadi hakan yasa a koda yaushe na sakaki a raina. Darajar soyayya bata kwatantuwa Domin masoya Kawai zasu gane haka, akoda yaushe hoton ki yana kan hannu na Domin abinda kake so dole ya zama a ranka koda yaushe ya ke masoyiyata a bar kauna ta. Komi kika ga na fada ba bakina Kawai ya furtashi ba hadda cikin zuciyata. Kiyi Gaggawar dorani kan hanya Domin in isa gidanki na soyayya. Rashin ki ya kasance kaddara ko Kuma fansar da zata kai ga zuciya kuka, kin halaka duk Wasu masu soyayya Domin kaunarki da zuciyar ki na a hannuna Kuma kinsan rashin Samun ki yakan iya saka kowane namiji kuka, duk da cewa sai an jajirce ake Samun babban rabo mai amfani irinki. Soyayyar ki ta jima tanaimin yawo acikin zuciya ta Domin dukkan babban da baya rike girman soyayya kice Dashi Yaro, shin ya kikqsan na tashi bacci dazu da safe? Domin ko yaushe sai na tashi sai nayi tunaninki bani tantamar fitowa dake a ko ina Domin kin kai mace Kuma ke kin kasance kadarata ce. Bini da kauna ni Kuma sai in raka ki da soyayya Domin soyayyar ki akaina na Riga na dauka. Zuciya ta bani sako ki zo ki karba gani ina Dakon tunaninki a kullun, Duba kiga tarin wasikun da na rubuta akanki amma Har yanzu na kasa Samun amsarki.
Har cikin zuciyata tunani na ya rabu dani Domin Hankali na ya Riga ya karkata a gareki, hausawa sunce komi Nisan jifa kasa zata sauka hakan yasa na sakama zuciyar tawa hakurin jiran amsarki ya ke masoyiyata. Ga samarin gari sunyi rashin Samun irinki sunyi Jira a Haifa mace irinki amma Har sun tsufa basu samuba amma nine Wanda Allah yayima gyadar dogo da nasamu irinki. Shi so makaho ne shiyasa yake da bukatar kulawa Domin dani dake babu batun muyi rabewa sabida akwai bakin ciki kaso Mutum ya gujeka, bana ganin wata diya mace tamkar ki Samun ki Har yakan sanyani marari ke na baiwa ji na da ganina Kuma lafazinki rudani yake a duk lokacin da kika zo a wajena Domin mugaisa, inason kibani zumar so insha wadda batada kissa acikinta. Yadda da amana sukan sanya soyayya tayi karko sabida ya ki kula dani ki lura dani ki Taimaka kada kibari sonki ya rikitamin lissafi. Ke kika zama ginshikina Kuma Garkuwan rayuwata, soyayyar ki Bazan bariba koda za'a kaini inda bazan dawoba. Ke na baiwa zuciyata Kuma bazan taba cewa kidawo da itaba. Duba kiga yadda sonki yayi mini duk da na San kina sane da yadda yayimin kibani maganin da bazan iya manta ki a rayuwata ba Domin tunaninki bazai taba fita a tsagin zuciya ta ba sannan duk abinda bakiso zanyi Kokarin hana kaina aikatashi, wata rana ina ni kadai sai in rinka tambayar kaina ya za'ayi in wadata wacce ke sona a soyayya. Ina sonki yake masoyiyata, tauraruwa ta Abin alfahari na so na gaskiyar gaskiya Wanda babu yaudara acikin gashi nauyi na kaunarki ya Riga ya rinjaye ni. Zuciya ta ta kamu da soyayyar ki Har ta gansu dake. Masoyiyata kinga nidai kinyimin kema ki zayyana mini idan nayi miki.
Sinadarin soyayyar ki yayimin Garkuwa ga dukkan gabobin jikina. Kin kasance mace wadda babu irin mai sukuninta da saka maza farin ciki a soyayya, hakika tun ranar da zuciyar ki ta yadda dani tun a wannan ranar nasan na ribatu a fannin soyayya da kauna Hadi da kulawa. Nayi Nisan da bani waiwaya gameda soyayyar ki ya ke ma'abociyar raya birni da karkarar zuciya ta. Ta kowane fanni na Rabin zuciya ta babu wata masokar tsintsiya wadda zan Samu sukuni Domin soyayya Da kaunarki sun kasance a daskare ga sassan duka zuciya ta. Na nuna miki soyayya wadda a duniya bani tunanin wata diya mace ta Samu irin soyayyar da kike Samu daga gareni. Wasu lokutan sai na tambayi kaina wai yanzu idan na rasaki wane hali zan shiga Domin na San tabbas bazan iya jure kalubalen rashinki ba. Babu zamanin Da zai zo Har ya wuce Wanda za'a iya Samun macce mai kyakkyawar sura da haiba irinki ko Kuma ince bazaa taba Samun tamkar ki ba a wannan nahiyar afrika kai hadda ma duniya baki daya. Banyi tunanin akwai ciwon Da zai iya kaini kasa war was ba amma sai gashi ciwon sonki ya kaini kasa hadda amai da gudanawa na soyayya da kauna.
Randa duk idona bai gankiba bazan iya cin Abinci ba kasancewar jini na da naki a tare suke zagayawa suna gudanar da so da kaunar juna ya ke habibiyata Abin juyin yanayin rayuwa ta. Masoyiyata banda tamkar ki a wurina jikina yana bani zakiyi nisa dani Amma na tabbatar da zuciyata ce shedan ke son shiyi galaba akaina Domin ni na jima da shiga fadama tare da afkawa koramar soyayyar ki yake muradin rayuwar zuciyata. Na shiga lungu Da sako Domin in Samu damar Samun Maye gurbinki da wata amma sai gashi na kasa kasancewar ke babbar yarinya ce mai kashe dukkan shawar samarin duniya.
0 Response to "Kalaman soyayya masu dadi da ratsa zuciya harda nishadantarwa 2025"
Post a Comment