Kalaman Soyayya - Kalaman Yabon Budurwa
Kalaman Soyayya - Kalaman Yabon Budurwa
Masoyiyata abar kauna ta tun ranar da nayi tozali dake na kasa zama na kasa tsayuwa kasancewar babu irin kyakkyawar furkarki a duk fadin nahiyar duniyar nan da muke ciki. Na jima inason inga mace mai surah da Haifa irin taki amma kash! Duk Garin da naje Domin Samun wannan bukatar mai Muhimmanci sai Abin yaci tura sabida ke ta daban ce ko cikin Dubu guda ake samu sai Kuma dace da mai irin siffar ki amma ba maganar kama da juna a tsakaninku ba. Nayi nisa Kuma Nisan da bani jin kira na soyayyar ki, na zagaye duka duniya tun daga Saudi Arabia, shina, Mali, France, indiya, indunusia, burkinafaso, Iran, Iraq, america, ingila, Spain, kodibowa, Holland, jamani dadai sauran su Domin insamu mace mai siga irin taki amma na kasa samun ta daga baya na dawo kasa ta najeriya tun daga abuja, legas, abia, potakul, bayelsa, kogi, Adamawa kebbi, sokoto, zamfara, katsina, Kano, jigawa, bauchi, gombe, Adamawa, taraba, yobe, Borno, Niger, Oyo Ibadan da lampai duk na kasa Samun mace mai irin kirarki Domin koda babu ki idan na kalleta zan iya rage kewa amma na kasa Samun biyan buka ta a rayuwa amma ba komai nine nafi kowa farin ciki akan haka tunda na tabbatar da babu yadda za'ayi asamu wani Mutum namiji Irina mai irin sa'ar rayuwar da na Samu dalilin Samun wacce tafi kowa kyauwo da nasaba da nasibi tubarraki baiwa tare da fasaha irin ta diya mace zuwa ga kowane da namiji. Ban fara sonki ba sai da ni Fahimci kin San rayuwa Kuma gaki da kamun kai da nasaba sannan bugu da kari gaki da asali na kwarai Wanda kowane namiji na son ya kulla alaka dake Domin neman iri a gidanshi wanda sai ya kasance uwa hadda riba acikin gidansa sannan ya zama yadon irin Wanda kowa zai iya zuwa ta gefen ka domin samun nagartaccen iri mai asali. Shin kin gane nufi na ko na saka ki a duhu? Maganata tana nufin idan na kasance a Matsayin mijinki ke Kuma kika kasance mata a gareni ya zama wajibi ga samarin da zasu tasowa bayan mun tsufa mun aje iyali su garzayo gidanmu Domin Neman diyan Da muka Haifa ni dake ta dalilin kirishma ki, laulayin ki, asalinki, kyawon ki, kudinki tare da kimar ki hakan zaisa kowa yaji yanason kulla zuria damu ta dalilin na tsaya nayi zabe mai kyau Wanda zai zama Garkuwa a gareni duniya da lahira. Da zaki iya taimako Nima in Taimaka Mu hada karfi da karfe in zama murhu ke kizama itace Mu dauki tukunyar so tare da kauna Mu Dora ta akai Domin mutaru Mu hada tuwon masoya, miya ta masoya, kulolin masoya Abin kwasar masoya gwagwar masoya Mu hada dukkanin abubuwan da suka dace Mu kwalhe tuwon da muka girka na soyayyar gaskiya da amana tare da mutunci mukaima masoyan juna suma su more Da wannan gagarumar soyayya irin tamu wadda ba kowane saurayi da budurwa zaka Samu suna gudanar da ita a wannan duniyar, a wannan kasar, a wannan jaha haka ma a wannan karamar hukumar wannan lokacin da muke ciki da amana tayi karamci in ba ga irinmu masoya asali ba. Na shirya zama toka wacce ake amfani Da ita ga bindigar masoya Domin Mu hada ta muyi duri Mu halbata ga makiya masu son suga sun bata soyayyar masoyan juna irin Mu Domin shine hukuncin da duk yafi dacewa dasu. Babu wata kasa ko jaha ko Kuma local government Da tarihin soyayyar Mu ya bayyana ko Kuma mai kama Dashi Sam hakan bata saba faruwa ba kasancewar ni dake na daban ne ko cikin miliyoyin Mutane dole idan angani an gaki ace ke mace ce mai fara'a mai cikakken aji haka Nima da an ganni ansan na iya takona. Bazan taba fatali da soyayyar ki ba Domin da na rasaki duk Nigeria babu asibitin da ke iya daukar dawainiyar kula dani kasancewar shiga halin ha'ulain da zanyi na rashin Samun sukuni da rashin gata na soyayyar ki. Idan ina tuna rayuwar ki sai inji wani irin a rayuwata inji tamkar duk fadin wannan duniyar babu wani sarki sai ni. Akan ki zan iya shiga ruwan da babu iyakar ganinka inyi nuta Domin inje in dauko miki tsibirin soyayya Wanda ba za'a sameshi ba dole sai tsakiyar wadannan ruwan duk da ni ba gwani bane a fannin ruwa amma zanyi kasadar isa in dauko wannan tsibiri so Domin kawo miki tare da yimasa ado don ya kara saka miki farin ciki yake masoyiyata Abin bege na
Masoyiyata Samun ki a kusa dani a koda yaushe tamkar yake kamar na tsinci dame a kala, inason idan mun kasance ma'aurata ki zama mai ishe ni turaka a koda yaushe Domin Mu gudanar da fira ta soyayya tare da yimin tsarabar fura tare da madarar nono don kara kauna da dankon soyayya. Da in rasaki a kusa dani gara abani takardar kama aiki Kuma akaini a maaikatar da babu kowa Acikin ta sai kadangaru. Rashin ki tamkar wata azaba ce da ake ji wadda misalin ta yafi ciwon nakuda ga diya mace lokacin da take haihuwa, rashin ki tamkar nayi Shekara goma ne inada burin inje kasa mai tsalki sai ga shekara goma sha daya na Samu ikon biyan kujerar Makkah nayi medical checkup nayi passport nayi Riga kafi, nayi kayan sakawa na uniform Amma ranar da zamu wucewa wani kwana na soyayyar ki ya nufe ni nan take na kwanta koda na tashi aka bincika jirgin da zai kaini Har ya isa Jidda. Akan soyayyar da nake miji zan iya kiwon shanu da rakuma da bisashe Har tsawon shekera biyu da wata uku da kwana biyu da wuni guda sai barawon soyayyar ki yazo ya kwashe duka dabbobin ga baki daya Kuma inji babu zaton su Kuma babu labarin inda suke bale a yanke shawarar ina za'a je a bincika koda zai kasance rabona ne. Nayi ta ci dasha akai akai Domin in Samu kuzari na daukar nauyin soyayyar ki a gangar jikina koda hakan zai zama dalilinki na tabbatar da so da kauna wacce nake miki a fili da boye sannan Acikin gida da wajen gida. Tarkon son ki ya Riga ya kama ni Kuma banida wata hanya wadda zanyi Kokarin kubuta face Neman mafita ta hanyar Samu da gayyato hadiman so suyi dafifi su riski kasa ta, su riski jaha ta Kuma su shigo cikin karamar hukuma ta Domin kawomin dauki don Samun salamar tarkon da ya sarkahe dani. Bayan hadimai na soyayya da kauna sunyi nasu kokari haka za'a kwashe ni akaini asibitin so mai dauke da taimako Kuma an ginata don Taimakon Mutane masu fama da ciwon so. Za'a yimaka awo kyauta, magani kyauta, a kaika gida kyauta Domin ka Morema shugabannin duniyar masoya da suka yi wannan yunkurin Domin Neman lafiya ga duk Wasu masoya.
Idan na Tina ranar da mukaje bakin korama ni dake domin musamu wuri Wanda yake saka kowanenn mu shauki sai inyi ta Tina kalaman da kika ta yimin na kashe zuciya mai ratsa ruhi ya ke masoyiyata. Banjin akwai wata rana da gari zai Waye Har wuni ya kare ban Samu awa biyu ina tunanin ki ba kasancewar Muhimmanci ki awurina, na sha madarar soyayya hadi da kauna burina in kasance mutum mai tattausar Maurya mai kyau Domin inzo wurinki insamu lafazin Isar miki da kalamai masu ratsa zuciyar ko, korama da gulbi tare da rafin dake kauyen Mu koda zasu hade wuri daya Kuma su lugude waje daya sai a yanka ni a saka wuka a fasani acire kayan cikina daga ciki hadda zuciyata mai dauke da sonki da mararinki na tabbatar da koda an dauke wannan zuciyar tawa an jefa wannan ambaliyar cikowar ruwan tare da daukar abu mai nauyi a hada da zuciyar yadda zasu nutsewa daga karshe zuciyar ta isa ga karamin kifi shi hadeta baya ya gama hadiyeta shima wani babban kifin shi hadiye shi bayan wannan babban kifin ya hadiyeshi shima wannan babban kifin shi hadu da kada shi hadiyeshi, haka shima kadan shiyi ido biyu da dorina a bakin ganga su hadu da fushin juna kowanen su suhadu suyima junan su nugu_nugu na tabbatar da wannan zuciyar tawa da ta fita hannu na tana nan cikin aminci kasancewar tana dauke da Son ki da kaunar ki tare da mararinki dare da rana kai harma a nade duniya zuciya ta bazata dakatar da sonki ba koda bata cikin gangar jikina koda akwai tazarar kilometers Dubu daya da Dari bakwai da sittin da Hudu na tazarar zuciyar tawa da gangar jikina. Na kurbi zuman kauna kema inason inyi miki gayyata muhimmiya wacce take ta daban Domin kema kizo ki karbi naki ragowar zuman kisha. Akanki na kai matakin ko ciwo nake Kuma duk yadda ciwon nan ya tsananta da anzo dake kin kira sunan da kike min na masoya da na farga na gano lalle kece a kusa dani to na tabbatar da na Samu warakar ciwo na. Idan ina ciwon kai murmushin ki shine zai zama maganin waraka da tadda kafadu agareni, idan cikina ya ciwo lafazin ki da kyakkyawar muryarki mai tarin zaki kamar madi itace zata zame min garkuwa a wajen tashi na daga wannan ciwon. Idan idaniya na na ciwo Har takai babin ban iya ganin kowa to da naji samatar takin kafafuwanki ya zama lalle insamu waraka idanuwa na su bude tare da gane komi wanda ke a fadin kasa koda kuwa akwai tazarar kilometers Hamsin da bakwai da digo uku a Tsakanin Mu Dashi.
Kash na so in zama injimin nika ke ki kasance hakuran injimin Domin muhadu Mu Nike duk Wata soyayya a fadin nahiyar duniya Mu maida ita tamkar gari muyi mata lukui_lukui bayan mun kammala sai muzo in zama kwarya ke ki kasance ko ki zamo matankadi mutaru Mu tankade wannan Garin na so da kaunar juna bayan munyi nasarar tankade sai kizo kizama itace nikuma inzama murhu Mu dauko tukunyar so da kauna Mu hana tuwon so da wannan tukunyar da akayita Domin so da kauna idan muka gama wannan tuwon sai Mu fara rarraba shi ga masoya masu kaunar juna Mu fara tun daga kasar China, Ghana, Spain, England, Germany, Burkina Faso, Togo, Dubai, Saudi Arabia, falasdine, Iraqi, Iran, itopiya, chadi, Mali, nijer, Cameron, america daga nan sai mudawo gida Nigeria lungu Da sako Mu nemi masoya masu kaunar juna tun daga Borno state, yobe state, taraba state, Adamawa state, gombe state, bauchi state, jigawa state, Kano state, katsina state, Zamfara state, sokoto state, kebbi state, Niger state, Oyo state, Lagos state, abia state, bayelsa state, akwa ibom state, nassarawa state, kogi state, abuja state kai harma da babban birnin potakot muje ko ina Mu rarrabama masoya tuwon so da miyar so Domin su amfana damu Mu masana soyayya da kaunar juna
Tabbas banida wata Garkuwa a yanzu wacce takai ki a fadin duniya. Banda wani sukuni a kowace rana a rayuwata bayan inshiga in fita insamu ganinki Domin zuciya ta tasamu sukuni tare da Samun salama ta rayuwa. A rayuwar soyayyar mu na shirya mata tsaf komi rintsi komi tsufa soyayyar da nake miki bazata taba raguwa a zuciyata ba ya ke aminiyar raya karkara fadama da koramun zuciya ta, bazan taba yin kasa a guiwa ba inhar akwaiki acikin duniyar nan. Na samu karramawa da daukaka ta dalilinki ya ke sarauniyar annurin zuciyata. Banda Hankali da tunani face in na Samu kula war ki da kyautar zuciyar ki da muradin yarjejeniyar kulawar ki yake aminiya mai dauke da ninzamin zuciyata abar faharin na. Inada yakinin idan na Samu karbuwa Kuma na sameki zan kasance cikin maza na duniya masu rike da inuwa mai damshin sanyi mai sanyaya zuciyar Dan adama yasa mata annushuwa na Har abada ko a karshen rayuwa. Banda yakinin zan kasance tare dake na Har abada ya ke masoyiyata amma inada tabbatacin ko banida rai zuciyata zata wuce da babban tabo a gareta Wanda bai warkewa wanda ta dalilin son ki ya addabi zuciyar tawa ya hanata duk wani motsi da sarrafa wa da bugun kudan jini Wanda yake zagayawa shiyi wani shillo muja daga irin wacce mafarauta ke yi su kama duk wani naman daji a dawa yayin da suka nufi babban birnin dajin bauchi wajen sa Rani. Babu wani da na Sani da zai riskeni kamar inga na baki tazara ta minti biyu da sakan biyu a rayuwata. Koda ance ke alluar ruwa ce mai rabo kan dauka to ya zamamin wajibi dakuma dole in mayar da Hankali tare da kure duk wata himma ta Domin in kasance Mutum Wanda zai mallake ki a wannan nahiyar duniya kai Har ma a ranar lahira inda matan huru'aini suke nafi son ace koda da wadannan dakwalen matan na cikin aljannah na kasance tare dake a rayuwa.
Tabbas ke kibiyar Ajali ce Kuma mai Kokarin tayar da Hankali tare da razana kowane namiji Kuma duk namijin ya ya kuskura kika shafe shi koda a gefen garkuwar jikinsa ne to ya zama wajibi ki shiga ta tsakiyar zuciyar sa kiyi Kuma tasiri Gareshi amana yaji babu wata mata a fadin duniyar nan da rabbi samawati walardi ya halitta wacce takai yake.
Nayi Nisan da bani kamuwa Kuma na zauce na kasance tamkar wani Mutum mahaukaci ta dalilin ki yake annuriya Kuma tauraruwa mai haskaka kwalakkwason kirjin makwarin zuciya ta da ruhina
Duk wata gidauniyar raya masoya da za'a bude a fadin kasar duniya ina baki tabbacin mune zamu zama Silar budewar wannan gidauniyar kungiyar Kuma mune zamu more mata a wannan takamammen lokaci. Har wa yau ina kara jajantama zuciya ta irin tunanin da takeyi tare da nashe_nashen da takeyi na tunanin Samun tazara a tsakaninmu wannan dalilin Yasa na kasa yafewa kaina Kuma da zuciyata na kafe kai Domin inyi Gaggawar daukar ma zuciya ta mataki ta dalilin wannan mummunan tunani da ta jima tana kawo min hakan Kuma ba Daidai bane gareni ace haka na faruwa Domin babu wani kalubalen da zan shiga a doron kasa Wanda yafi rashinki a kusa dani. Soyayyar kowa dake zaune a duniya tamu nida ke idan aka hadeta zata kai ta Al'ummar duniya duka a baki daya Domin ni na daban ne Acikin maza sa'a ta Kuma kema ta daban ce acikin matan duniya sa'ar ki, ki shirya zama da tsayuwa tare da damarar daukar kowane mataki mummuna ga duk Wanda ke tunanin ya shigo Acikin alakar Mu Domin shiyi mata illah Domin idan bamu hada karfi da karfe ba Al'ummar garin da muke zasu iya yin komai Domin suga sun bata alakarmu tsakanin ni dake yake susu wacce nake sakama sabulun soyayya inyi Kokarin wanke duk wani datti tun daga kaina, wuya na kafada na, kirji na, cikina, Mara ta, guiyoyina, Hadi da kwabro na da kafafuwana Wanda zai zama barazana ga lafiyar soyayyar mu ta yau da kullun Domin shine mataki Wanda yakamata ni dake mutaru Mu dauka don gyara soyayyar Mu, muyi mata ado tare Da kwaskwarima mai saka mata daraja a ko ina. Banga wata yarinya da zatayi tasiri a zuciya ta ba idan Har gaki banda wani shawarar idan ba taki ba sarautar da duk za'a iya bani ta kowane gari koda an Riga da an nadamin rawani zan iya murabus in barmiki sarauta ta duk da cewa mata basu sarauta a Yankin arewa dake dauke da dimbin hausawa amma ke ya zama wajibi in bayar da kujera ko in sadaukar da ita akanki. Na shiga yanayin da ban saba samun kaina acikinsa ba ta dalilin samun ki yanayin Kuma ba abinda ya sakani face farin ciki farin cikin tare da annushawa ta fannin jin dadina da walwala ta. Na tabbatar da babu mace mai ratsa mazajen gari ta Bangaren soyayya kulawa da Kuma kauna kamarki yake sahiba ta mai kamar Zuma farar saka mai kamar galla idan ta kasance acikin iccen mangwaro. Banida wani salama a rayuwata idan Har dare zai tsala tun daga faron dare tsakiyar sa har zuwa karshensa ban Samun runtsa ido inyi kwana sabida zurfin tunanin ki da yake zomin kwatsam idan na kwanta.
Ke tamkar fitila ce wacce idan duhu ya bayyana akan iya amfani dake a haska Acikin garin masoya Domin kowa ya Fahimci so, yasan Kuma minene so, yasan minene amfanin so, Kuma ya amfana daso yake tauraruwar da ke haske samaniya da wata da rana duk suna bayan ki Domin baza a taba kwatanta hasken ki da na wata ba bale rana mai saukar da zafi yana sukar Mutane salihan bayin Allah musamman yayin da suke neman abinci. Idan na wuni banyi kukan rashin jin muryarki ba sai inji ga baki duka numfashi na ya dauke Domin kece ke kula da sassan dake dauke da generator Wanda ke bada wuta Kuma ya haska numfashi na yake baturiya nuriya kyakkyawar da idan ta fito kowace mace zata Rena kanta Domin ajin ki da shigar ki da kasaitar ki da annushuwar ki da sukunin ki sun baiwa na kowane budurwa rata a fadin kasar Nigeria. Bance kinfi kowace mace a duniya ba Domin duniya Yawa gareta amma duk Inda za'a je gasa ta mata masu kyau a fuska da dukkanin gangar jiki tun daga kai, wuya, kirji, ciki, Mara Hadi da kafafuwanki na tabbatar da yakan zama Abu mafi wuya asamu mai irin siggar ki ko Kuma kama dake. Kai Har rantsuwa zan iya yi wacce babu kaffara agareta babu wata mace mai diri da siffa ta kamala a fuska tamkar ke sahibata
A koda yaushe ina mai rokon Allah Domin kada shi baiwa kunci da damuwa damar shiga zuciyar ki kasancewar idan kika shiga wani hali nine na shiga a wannan halin da Kuma yanayin damuwa Domin gangar jikina da naki sun hade da jini tare da jijiya suna gudanar da Aikin busa numfashi a tare, kinga kuwa tunda wannan ta faru Dole ne inji tsoron afkawa acikin damuwar ki Domin damuwar ki itace babbar barazana agareni. Na Dade ina alfahari tare da jin dadin ganin duk wani Yaro ko yarinyar dake cikin gidannan naku domin akoda yaushe na kalli yaran gidanku sai inji wani shauki na jin dadi tare da kyakkyawar muryar su zaka ga ta ratsa jikina da fannin zuciya ta ko Kuma ince shimfidar taskar Rukunin kalbi na na fili Dana boye kasancewar kasantuwar ki mace mai kyau mai kima mai lafazi tare da karramawa Hadi da biyayya ga kowane da namiji da Mutanen duniya da na Yankin area Ku da sauran sassan wurare daban_daban nusamman idan kin zo wucewa ta majalisa mai dauke da tarin samarin gari masu Yawa a wannan wurin sai kaga kowa hankalin shi da tunanin shi ya karkata ya koma a Bangaren ki ta dalilin sura ki dakuma haiba wacce Allah ya albarkace ki da ita na a Matsayinki na diya mace. Rijiya, tafki da korama sun cika fafil sai ga igiyar sonki ta zo ta haura wurin amma ta tsinke ta fada duk jaruman gari kowa na Duba ta yadda zai dauko wannan igiyar soyayyar ki Domin tayi masa amfani ta hanyar yunkurin amfani da ita Domin ta zame masa makamin yakar soyayyar ki amma kash! Sai ga baki daya samarin wurin da na Garin dukanau sunyi kasa a guiwa Kuma sunyi ragon azanci haka Kuma sun nuna kasawar su a Bangaren jarumta irin ta masoya budar bakin wani keda wuya yace inda ace wane na nan cewa dani da yanzu na zo na afka gangar jikina acikin wannan ruwan tare da nutsewa Domin nemo wannan igiyar soyayyar ki dakuma kaunar ki nan take wani daga cikin manyan samarin anguwar ya tuntubeni Har majalisar da nake zama ya karanta min abinda ke faruwa sai gashi ban tsaya wata wata ba sai muka isa a kusa da ruwan ina zuwa sai na hangeki muna hada idona ni dake ban tsaya wata wata ba sai gashi na afka acikin wannan ruwan ba tare da shawarar kowaba ina shiga ina nutsewa Domin inyi Kokarin kamo igiya mai dauke da Ninzamin soyayyar ki sai gashi na kwana na wuni acikin ruwa kwatsan sai ga igiyar so a hannu na koda na iso ganga sai ga ayarin Mutane sukai mutun Dubu daya Dari shida da Hamsin da takwas sunyi tsaye suna kallon ikon Allah. Nan take na mayar mata shike nan sai gaki tare dani Kuma tare da yabama jarumta ta
Na tabbatar da idan soyayyar ki ibada ce da nine Mutum na farko a duniya Wanda idan yaje lahira ake kyautata masa zaton zai dace da rahamar Ubangiji. Da soyayyar ki taliya ce da na ci ta koda babu mai Domin ke babu abinda aka nema a gurunki duniya a rasa shi, kina tsorata ni a duk lokacin da kike gayamin wata rana zamu rabu hakan yana saka zuciya ta tana tafarfasa na jima ina jin haka daga cikin zuciya ta da rayuwa ta.
0 Response to "Kalaman Soyayya - Kalaman Yabon Budurwa"
Post a Comment