-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

99 Kalaman Soyayya Masu Ratsa Jiki

99 Kalaman Soyayya Masu Ratsa Jiki

99 Kalaman Soyayya Masu Ratsa Jiki





Masoyiyata ki dawo gareni Domin bani iya jure ko minti goma banganki ba yake fadamar da nake amfani da ita Domin shuka lambu na na soyayya da kauna ya abar kauna ta mai kamar Zuma da galla a farar saka. Banyi bacci ba jiya lokacin da aka kirani aka gayamin kinyi tafiya zuwa kasuwa da na biki a baya banganki ba Kuma na kira wayarki ban Samu ba tun wannan lokacin ban sake samun sukuni ba Domin ina fargaba da jin tsoron kada wani yashiga tsakanina dake yake masoyiyata. Babu wata tazara da zan iya samu a yanzu wadda zan Samu sassaucin dannar da soyayyar ki tayimin a birnin zuciya ta. Anyi ruwa a dauke naji murya mai kama da muryar ki koda na fito a gurguje talababiya ta kwashe ni amma duk da haka na kasa gane na fadi kasa kasancewar kinada Muhimmanci a wurina tare da tsaremin duk wata muruba ta da mutunci na wannan dalilin yasa ban tsoron fadawa kowane kalubale akan soyayyar ki yake habibiyata. Babu shakka kin Samu gurbi wanda bai misaltuwa Kuma baza a iya kwatanta shi acikin zuciya ta ba, kin mamaye duk Wasu sassan jikina masu Isar da jinin jikina tun daga zuciya ta har zuwa jijiyoyin jikina, kin zama tantabara uwar alkawali kasancewar komai tsawon wuni idan lokacin dare yayi dole zuciyar ki zata baro jikin ki ta dawo jikina ta hade da tawa zuciyar su gudanar da soyayya tun daga farkon dare tsakiyar dare Har karshen dare. Sallolin Da muke dasu a wuni babu wata sallah da zata gudana banyi miki roko daban daban ba. Kuma kowace sallah da tata kalar rokon da nake miki yake masoyiyata. Idan na kammala sallar asuba zanyi miki rokon Allah yabaki jin dadin duniya da lahira Kuma yasa ki kasance acikin mata yantattu na ranar lahira masu Samun ceton annabi Muhammad SAW. Idan nayi sallar azahar na kasance ina yimiki addua gameda karatun da kike Allah yabaki kyakkyawan sakamako Wanda yafi na kowa acikin Saar ki da kuke karatun a tare. Idan na kammala sallar la'asar na kasance mai yimiki adduar gamawa da iyayenki makwaftan ki tare da sauran yan uwanki lafiya. Idan na kammala sallar magriba na kasance ina yimiki addu'ar Samun lafiya tare da Samun kuzari a kowane sasssa na gabobin jikin ki. Idan Kuma na kammala sallar isha'i na kasance mai roka miki aljanna fildausi tare da haduwar Mu acikin ta ni dake Domin muci gaba da soyayyar da muke yi acikin duniya sannan Mu raya sauran Mutanen dake cikinta. Kinji irin rokon da nake miki dare da rana a kullun yaumin Domin in nuna miki irin Matukar soyayya da kauna tare da kulawa da nake miki yake aminiya habibiya tauraruwar dake haske duniya Mutane suga hasken da zai amfanesu a fannin gudanar da soyayya da kaunar juna. Banida wani buri Wanda ya wuce naganki a kusa dani koda cikin mafarki ne. Ina ma ace duk inda zaki je koda bai kai tsawon kilomita guda ba sai kin kirani nazo wajen ki Domin inyi miki rakkiya muje tare mudawo tare. Yake abokiyar raya zuciya ta inasonki ina kaunar ki ina muradinki ina begen ki a koda yaushe nasamu kaina cikin halin farin ciki na tabbatar da cewa ba komi ne ya sakani cikin wannan halin farin ciki ba face soyayyar zuciyar ki da wannan zuciyar tawa mai albarka ke dauke da ita to itace ummul haba'isin farin cikina kullun a koda yaushe dare da rana Safiya Kuma da wuni Kuma nayi nazari iya nazari na kasa fahimtar yaya zanyi in Samu zuciyar ki ta kasance wuri daya da tawa zuciyar Domin insamu sukuni na rayuwa amma kash! Duk likitan da na gayyato Domin shiyimin wannan aikin bazai iyaba kasancewar babu wani Mutum Wanda zai iya rayuwa babu zuciya acikin jikinsa wannan dalilin shi yasa na kasa hade zuciyata da taki awuri daya koda nine zan mallaka miki tawa zuciyar ta isa a wajen ki Domin ki hadasu guda biyu a wuri daya yake masoyiyata aminiyar rayuwa ta.


Mutuwa ma idan tazo daukar wani daga cikin Mu zata ji wani shakku irin yadda zata rabamu Kuma ta wuce da ruhin Mutum daya ta dauki na daya, haka koda mutuwa tazo daukar waninmu zamuyi Kokarin bata zabi Domin ta kwashe rayukanmu a tare Kuma ta hadasu a wuri daya ta game ruhin awuri daya Domin ranar lahira mutashi tare muci gaba da soyayyar Mu inda ta tsaya. Ya ke masoyiyata Abin alfahari na shin kina jin irin radadin da nake ji idan kika gayamin yau bakida lafiya? Shin kema kina jin haka a lokacin da zan sanar dake banida lafiya ko banjin dadin jikina? Wannan dalilin yasa babu cutur da zata kawo min ziyara ajikina in kuskura in gaya miki banda lafiya Domin inajin tsoron irin halin da zaki shiga kasancewar Muhimmanci na gareki Kuma kinada Muhimmanci Wanda banson inganki acikin damuwa a kowane lokaci. Kin zamo damo sarkin hakuri wannan dalilin yasa nake kara sauke kayana acikin babbar jihar zuciyarki yake mai bani ruwa a lokacin da kishi ya riske ni na soyayyar ki da kaunar ki. Kaunar ki a raina ba kamarki a fadin duniya nine na jaraba haka Kuma na Samu tabbaci Acikin zuciyata. Ke tauraruwar da ke Bawa duk masoya duniya haske ce abar kauna ta. Na shiga Birni na shiga kauye domin inga mace mai kyawonki amma na kasa Samun irinki. Dole in maida Hankali wajen rike ki da Muhimmanci haka Kuma ban taba tunanin inyima zuciyata shamaki da isa lungun zuciyar ki ba. Na shiga na fita lungu da sako domin inyi awon gaba da duk wani mai son ya kawo mana cikas a soyayyar mu nida ke. Banga dalilin da zaisa in baiwa zuciyata tazara ta minti biyu batayi tunaninki ba yake yabibiyar raya birni da karkarar zuciyata. Banda yakinin rayuwa ta zata kai Gobe amma tun daga lokacin Da na tashi daga baccin yau na fara yadda zan tunkari shirin baki Gudummuwa soyayya a Gobe, Gobe Kuma tayiwa jibi ita Kuma jibi tayiwa gata shiri itama gata tayima citta shirin yadda zasu cimmata Domin kowace rana tazama cikin shiri na soyayyar ki da kaunarki. Soyayyar da ke raina gareki bazan taba gajiya ba, nayi lullubin soyayyar ki kamar ango da amarya kin San so idan ya bace hadda alakar gida yake tabawa. Ke nikason kiyo tuwo na kauna kizo kibani, ki dafa miya ta kauna kibani ni masoyinki haka Kuma kidama hura ta kauna ki zo kibani. Allah mamallaki na ya taimakeni in rika gwagwarmayar sonki koda babu rikon makami a hannuna in tsallake duk wani dafin damana da rani. Ke zanyima alkawalin hadin kudin aurenki Domin dake Nike alfahari a zuciyata. Zafin sukar zuciyata na tallafin soyayyar ki nikeyi kamar indaina sonki Kuma na jure sabida babu wata Mace kamarki a fadin wannan duniya da muke ciki yake masoyiyata. Inaji dake ni bazan barki ba ni kullun a fata na yaushe ne zamuyo aure, idan lokaci yayi ni angonki ne sannan ba wani namiji dazai fini jin dadin aure idan na aure ki, ke kika ban kauna wadda kudi basa saye, ki zo muyi batu amma batun zuciya. Zan iya rantsuwa ba wadda takkaiki ba wai kyau ba ko wanka a fannin soyayya da kauna, na San zaki zama karfina kibani wurin kwana Kuma kizama sarkin a fada ta Da nake mulki ta soyayya da kauna da amana. Zan baki lokacina inzo Mu zauna dake muyi soyayya da nuna kauna Tsakaninmu. Ni rayuwata na Riga na mallaka ta gareki shiyasa koda yaushe nake farin cikin idan muna zaune dake. Kaunarki ta shigemin cikin jiki jini da zuciya idaniya na sune Abin tambaya Domin sune sheda. Ina son ko a mafarkin ki in kasance nine Abin mafarkin ki Domin bazan rayuba sai dake, shi lamarin so tsakanina dake mujaddadi ne, na yadda da rabona nawa ne koda ina cikin kasar waje wannan dalilin shiyasa Allah ya hadani dake Domin wannan yazama wa'azi. Nayi tanadin da baida adadi gameda soyayyar ki duk da cewa ba lalle bane duk Wanda kakeso dole shiyima yadda kake sonshi Allah shibani ke ba don halina ba Allah shi Kareni da nuna zamba zuwa gareki. Da haka Wasu mazajen zasu soki Kuma Wasu su rasaki amma na tabbatar ni kadai ne duk Wanda zai shigo a kofar zuciyar ki na tabbbata nine gaba Dashi duk da cewa babu komi gareni da zan iya baki ya karkatomin da hankalinki. Alkawalin Mu dake Allah yasa ya zauna a zuciyar ki Domin ko yaushe zuciya ta begen ki take a Safiya da marece Domin kuwa banda kamar ki Kuma bazan taba tunin akwai ranar da zuciya ta zata nasa min inyi nesa dakeba, acikin zuciyata kekadai kika tare cikinta, kin rufe ko ina acikin jikina kin mamaye nifa kisani soyayya gadon ta niyyi Kuma komi ki rasa a duniya bazanji kin fita raina ba habibiya ta zo kisani sahun farko na cikin zuciyar ki kada kibari aji kukana a rayuwa yake masoyiyata Abin alfahari na inason kibani kulawa wadda akaso a tsakanin masoyan juna idan Har akwai so da yadda ya kamata amana tazo ta tsaya wuri guda cak Domin soyayya tasamu tsayawa mai kyau. Ina Matukar farin ciki da nayi gamo dake shiyasa na kara bata lokaci Domin kara kasancewa a tare dake. Akanki na jure zafi na jure sanyi a kowane hali na rayuwata Har Mutane suka Fahimci cewa na zauce. Kibani ruwa masu dauke da sinadarin so da kauna Domin nasha na Samu karfin sarrafa miki kalmomin so na hakika. 



Ki Sani cewa sai da ido ake ganin hanya kamin a iso ga sansanin hanya amma duk runtsi idan naji kiranki dole in juya, Kuma idan nayi nesa dake sai inji tamkar anyimin kisan gillah. Kina a raina hubby farin cikina kece zan baiwa kauna idan babu ki babu ni Kuma inaso idan bani ya kasance kema babu ki da kaunar ki nakeson in rufe duk wata kofa Amma idan na isa acikin lambun kauna. Kuma ke zanyi ma adon shadda Domin kece farin cikina rabuwa dake tamkar kuskure ne Wanda bazai taba gyaruwa ba. Idan soyayyar ki ce banma fara ba a yanzu Kuma ba dani farauba haka Kuma ba dani karauba kasancewar so da kauna tun banzo duniya ba. Inji dake dole sai nayi amo a rayuwa. Ke ce zuciyata mai buga numfashi na kece amanar zuciya ta. Zuciyata da rabinta suna gareki gabadai dole in baki kyautar tagullah sabida baki sakani kwallah ba. Na kurbi sonki a kofin lu'ulu'u Domin na dace dake dole insamu kaina cikin masu shanye ruwan kalkausarar birnin soyayyar ki. Kauna ce ta hadamu ni dake don haka kada ki biyema masu adawa kin San so da wuyar Sani. Ya zama dole inyi yabo gareki abar sona. Kin zama tauraro acikin zuciya ta. Akwai wani labari zo kusa in saka miki shi a kunne Domin ki taushe bakin duk Wasu makiya. Idan ki hadu da mai Sheri kiyi maza ki maida mishi da alheri ya ke masoyiyata, kinsan rama Sheri da alheri Yanada kyau ga Mutum mai Hankali. Na baki dama ki zamto kamar malama ta Domin ki kwatanta mini yadda so yake a zuciya. Yabonki ko yaushe aiki na ne bai sauyuwa ki zama malama agareni ki nunamin yadda so yake da babban matsayi a zuciyar masoya

0 Response to "99 Kalaman Soyayya Masu Ratsa Jiki"

Post a Comment