-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

200+ Kalaman Yabon Budurwa Masu Dadi

200+ Kalaman Yabon Budurwa Masu Dadi

200+ Kalaman Yabon Budurwa Masu Dadi 

Ko wace mace idan tazomin sai inga bata gabana duk da cewa turmi na musu da tukunya. Sannan kowa zaiyi shuka yana raayin kyawun iri ko ya kasance Kore ko fari shiyasa nake ta muradin in sameki in saka acikin kalbin zuciyata duk da cewa akwai su kanwa uwar gami sune wadanda idan sukaga soyayyar masoya na ta kara yaduwa akoda yaushe basuda wani buri Wanda yafi musu su raba wannan soyayyar to idan ma sun manta ki tuna musu cewa babu mai iya dakatar da wannan soyayyar tamu, Babu wani acikin wannan nahiyar ta duniya Wanda zai iya dakatar dani acikin soyayyar Mu face mutuwa. Nayi kewarki masoyiyata fiye da tunaninki. Lalle da kunu Da kunama gwara kunu sannan Da bala Da bala'i gwara bala Domin ko banza balai Abin a gujeshi ne yake sahibata ina ta dirikowar inga kin tsayu ga kafafunki a fannin soyayya Mu da kaunar da nake miki yake Rabin raina mai sanyaya zuciyata acikin kowane hali idan nasamu kaina acikin. Kece mai yar sarkar wuya wadda idan kaganta babu wani tambaya ansan ke ce ya ke sarauniya mai dauke Da masarautar gabas, yamma, kudu da arewa a fannin soyayya Da kaunar juna tare Da amana ta girmamawa ya muhibbata ni baza a rabani dake ba yake zinariya mai kyalkyalin Da Bai gushewa koda zan Samu kaina na kasance acikin duhun da babu ko alamar haske a tare Dashi. Ko ina cikin fadama zan iya cire rigata da sauran sutura ta Domin inji sarari Domin soyayyar ki ta hanani jin sarari acikin dukkan sassan jikina ya sararuniya ta Abin akfarharin rayuwata.


Na Gayama samarin Garinmu duk wani mai son katarar Giwa a gaya mata tayi masa nauyi, turmi a saman murhu Ku gaya masa yayi masa zafin dauka Domin ke ba ajinshi bace Domin kinada hali biyu sannan gaki da gida biyu na masoya akan haka koda yaushe idan na ganki sai in damu banyi kyauta koda sau Hamsin aka kira sunanki banda yadda zanyi dole sai na saka aljihuna nayi kyauta Domin kyautata ma soyayyar dake tsakaninmu dake ya ke Abin alfahari na da fitilar da Nike haskakawa in je Kuma in dawo acikin babban birnin soyayya. Kin Riga kin zama korama mai dauke Da Wasu manyan ruwa masu dausayin sanyi mai ni'ima Wanda idan ya ratsa ta jikinka zaka ji ka tamkar Wanda yasamu wata muhimmiyar kyauta ta Rahama musamman idan akwai yanayin zafi zakaji komai yayima garau kaji kanka tamkar lokacin hunturun sanyi ake ciki Kuma gashi cikin yanayin zafi ake ciki. Babu shakka soyayyar ki ta Riga ta ratsa jinin jikina ga baki daya na zauce ban iya Samun bacci isasshe Wanda sai na Samu kaina a zauce komai kurfin dare zanga koda zanje inyi kwanciya sai inga kwanciyar bazata yuyuba kasancewar Mashin soyayyar ki yayi tsaye cak acikin tsakiyar zuciyata sannan duk inda jini ke gudana daga jijiyoyin jiki zuwa zuciyata na tabbatar Da babu yadda zanyi insamu sukuni sai na hadu dake Domin ganinki shi zai kara karamin Kwarin guiwa tare Da Samun sukuni na zucciya Da kazazzaben sashen ruhin rayuwata ya shiga ya fita shiyimin tsayi mai taurin gaske shi kama dukkan ruhina ya sakashi sukuni Kuma asamu nutsuwa. Lalle kin wuce a kushe ki acikin kowace mata na nahiyar duniya da muke ciki mai dauke da manyan mata.


Lalle na tabbatar da kyauta ta wuce Tsintuwa a kowane lokaci. Kaunar Da nake miki ta sa koda na gudu na tabbatar da ban tsiraba sabida soyayyar ki na cikin jikina tayimin katutu sannan gaki saman kainuwa saidai aganki saman kainuwa Domin kin wuce nutsewa acikin kowane ruwa a nahiyar duniyar nan da muke ciki. Kin zama mai gira a goshi sannan ga yan kwalo a fuskar ki masu kyau hakan yasa kowa ya iso a wajenki Domin Neman soyayyar ki bazaki bashi dama ba kinsan kan koyarwar kwarai to dole ya kamata a zama gwani Domin kowane dakin bazai tabbata a Matsayin dakin ba dole saida yashi. Soyayyar Mu ni dake saidai masu fushi suyi ta fushi yan bakin gida suja daga baya Domin ke ce shugaban kasar zuciyata gwamnan zuciya ta yar majalisar tarayya ta zuciya ta ciyaman zuciyar yar majalisar jaha ta zuciyata sannan uwa Uba ma kansila kika zamo ta zuciyata. Burin zuciya ba abinda takeso tasamu rayuwa mai iya haska mata zuciya. Yabonki inayi Kuma duk sakan nutsuwa nikai in babu ke wa zan rike Kuma inason kisa yadda a soyayyar Mu Domin nine naki Kuma mallakin ki so nake kizamo mata in zamo miji idan hakan ta Samu to dole inyi hamdala kin zama idona a gari koda na ganki sai inji na kara Samun kwarjini acikin Mutane.


Nifa kaunar ki nake yan mata Kuma babu abinda zaisa wannan soyayyar taki ta rage a rayuwata Domin duniya ta sheda soyayyar da nake miki ba jabu bace Kuma duk Al'ummar gari shedane. Kinsan so makaho ne sannan idan babu ke ina zani. Ina sonki sahiba kada kibarni soyayyar ki ta zama sinadarin rayuwata a fannin Yankin kalbi na. Kinsan a duniya banda kowa a soyayya face ke ga labarin soyayya ta zan baki ni bansan ya so yake ba saida na hadu dake na Fahimci minene so. Wata rana ina kan hanyata daga makaranta zuwa gida Domin isa gida ana haka sai gaki kin iso kan hanya sai nayi gamo da abokiyar rayuwa mai iya raya dukkanin kalbi na tun daga nan na tabbatar Da zuciya ta tana rayamin ke ce abokiyar rayuwata dake Kuma zan zauna na more rayuwa a fannin gudanar Da rayuwa cikin nishadi tare da annushuwa. Lalle rayuwa kaddara ce Kuma kowa da irin tasa to haka soyayya ke rabuwa sashe sashe acikin jinin Mutane. Kibari in gaya miki rayuwata idan Har bake to tamkar mutuwa ce a gareni shaanin so na rabuwa ta kowane fanni ke ce masoyiyata Kuma ta gaske Wasu masoya basu Duba nasabar so amma ke kina yimin adalci a Bangaren soyayya kulawa fara'a tare da kauna. Na jima banga mace mai diri ko akan hanya ta wuce irinkiba ya ke masoyiyata Abin alfahari na akanki na kasa ciki na kasa sha Domin babu wani sukunin da ya rage wata tazara acikin zuciyata. Nayi lale nayi marhabin Da sallamar zuciyar ki zuwa tawa zuciya hakika nayi Matukar farin ciki Da irin kulawar Da nake Samu ta soyayya daga wajen ki ya aminyata mai son fara'a tare dani akoda yaushe dare da rana Safiya sannan Kuma da maraice. Na kasa Samun sukuni dole sai na Samu soyayyar ki gabaki daya irin yadda ko wani ke son ya shigo acikinta bazai iya tasiri acikin Zuciyar ki ba kasancewar nayi mata babban gini na Karin tubalin Da ba yadda za'ayi a ratsa ta ba ya ke jakadiyar sarkin dake aika sakon duk wata soyayya zuwa ga masoya guda biyu ta fannin kaunar juna.


Hakika rashin ki a kusa dani zai kasance babbar illah acikin rayuwata Domin banda wani nishadi Wanda zaisa in zautu acikin tunani na na yau da kullun Wanda ya wuce in sameki a kusa Dani numfashi ki na hadewa da nawa numfashi daga nan zan Samu babban sukuni a rayuwata Wanda sai nayi kwanakin Da idan naci karo da Abinci koda ban sakashi acikin baki na ba sai inji gaba ki daya na koshi Domin tasirin Da soyayyar ki tayi acikin zuciyata ba karamin tasiri bane haka Kuma dalilin da yasa na kasa ko rage soyayyar ki acikin zuciyata shine; kinada kamala, kinada haiba, kinada kwarjini, kinada muruba a idonki Kuma ga jamaar garinmu, sannan kinada karamci, kinada amana sannan ga kyakkyawar zuciya Da haiba mai kyau ya ke masoyiyata abar alfaharin rayuwata wacce a kullun dake nake kwana Kuma dake nake tashi a rayuwata. Hakika alherin Allah ya tunkaro ni ta dalilin kulla wannan kyakkyawar Alaka tsakani na dake, kin zama fannin Da idan babu shi tamkar na rasa wata gaba ne acikin gabban jikina amma kash babu wata diya mace wadda zata iya kusantoni inji na zauce Domin duka yan matan duniya banga kalarki ba a wannan nahiyar duniya Domin babu loko Da sakon Da ban shigaba Domin inga mace mai kala irin taki Amma kash ko makamanciyar ki ankasa Samu a nahiyar duniya baki daya. Ban taba tunanin akwai wata rana wadda zata zo in kasa tunanniki ba yake wace ta sacemin zuciya Kuma bayan kin sace kika kaita a wani jeji mai tsananin nisa daga bisani kare yaje ya cinye zuciyar bayan shekaru goma sha biyu da wata biyu da kwana Hudu da minti goma da sakan Hamsin haka aka Samu dakari ya Samu Karen ya yanke ya cinye Karen ga baki daya daga nan shima bayan wani lokacin shima badakaren ya mutu aka kaishi aka rufe amma duk Da haka zuciya ta bata daina amfani acikin jikina ba kasancewar soyayyar ki ba karamin rawa ta taka a fannin zuciyata ba

0 Response to "200+ Kalaman Yabon Budurwa Masu Dadi"

Post a Comment