-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

200+ Kalaman Soyayya

200+ Kalaman Soyayya

200+ Kalaman Soyayya



Ke budurwa ta ce ke nika kauna Kuma haka na ganki na kyasa Samun ki na Riga nayi riba ga dukkan wani Da namiji Domin na Riga na zauce akanki na aminta muyo aure Kuma kauna ce tasa na makkale zuciyata akanki kinada alkunya dake na aminta gimbiyata. Sarauniya ki juyo gareni Domin da kudiri guda nikayin fama ki taimakeni Domin insamu sururi yabonki zuciyata ta aminta yake gimbiyata ki aminta Domin kizo gareni koda kaina akace in bada sabida ke zanyi, ni kinga na daina sonki tun randa kikkace bakin sona ke kika lurasheni komi zanyi inkare mutuncina kada inbari so yakaini Garin da bazan iya jure zamaba. To Ashe Wanda zucciya takeso bashi yake sonta ba kituna ba dare ba dara duk rakiyar sonki babu wacce banyi ba


Akanki na jure zafi na jure sanyi Kuma bani gajiya akanki Har yaumal tanadi, kiran waya sai inkira ki sau goma ko kira daya bazaki daga ba yan uwana suna gayamin in daina sonki Niko bazan iya bariba, zafin zuciyar da na rika akan sonki ba zaki iya ba amma Ashe so Yanada rana tunda gashi kin dawo. Kukan da duk zakiyi akaina Bazan taba koma miki ba, indai ana batun soyayya a nahiyar kasar Nigeria na tabbatar da ke jigo ce acikin mata don haka nake muradinki akoda yaushe, Allahu Rabbana Abin bauta shi na hannantama soyayyar ki, salati nakeyi ga rasulu saw Domin kowa ya ki shi yayi hasara amma akoda yaushe ina tawassali Dashi. Shi goro bashi maganin yunwa amma na tabbatar idan gaki to zan koshi, tilas ne na dinga darawa indai akwai ki a doron kasa. Komi kika bani na tabbatar Da arzukin kaunar da nake miki nicci, bari ganin reza karama a halitta Domin jarin Dan sane ce haka soyayyar Da nake miki ta wuce matakin tunanin kowa Domin duk mai ganin zogale yabashi shawa dole ya hadashi Da karago Kuma yaji indai na arziki ne dole akwai citta acikinsa. Son alumma da yawan fara'a sai ke masoyiyata.


Tafi in biki ya ke masoyiyata Mata masu soyayyar kauna suna rusunawa su gaida ke Domin haka balango shi ka burgeni ba wai kuli da yajiba kowa ya saki rumbun hatsin soyayyar ki na tabbatar da sai yayi rama sabida yunwa. Tashoshin motar Da za'a dauki wani namiji Domin isa babban birnin soyayyar ki sunyi wuya kasancewar ke mace ce wadda batada arha ga kowane namiji nidai ke ka burgeni ba wai wata diya mace ba, kece kihi sarkin wanka Domin ita Tsafta ibace Kuma kina yinta ne bawai don burga ba.


Idan naji an kirarki dole sai nayi kyauta koda kalilan ba soyayyar ki na tabbatar da ko ina zaune naji ankira ki dole da naji ki na tabbatar da akwai kauna saidai mata su fiki katon hijabi amma ba kwalliya Da Tsafta ba Domin ke ta daban ce acikin manyan mata. Gani dai acikin gonar zuciyar ki ko in mutu ko in rayu, Allah da yayi balbela yayi shamuwa yayi maiki shine ya hadani Dake Har nasamu soyayyar ki, sabida haka kiyi Kokarin daukar zare kibar auduga Domin kaddara tafi fata, muryarki Da kyawunki ya zagaye ko ina acikin nahiyar duniya koda wa zumunci ni nafi karfin in fadi ta dalilin ki ko mai kushe sonki gareni yayi kuskure. Bude kunnayenki Domin idan na fada miki Kalmar soyayya ki dauka yake masoyiyata. Zallar farin cikin kasancewa tare dake banma fara ba

0 Response to "200+ Kalaman Soyayya"

Post a Comment