-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

100+ Sabbin Kalaman Soyayya Masu Janyo Hankali Masoya

100+ Sabbin Kalaman Soyayya Masu Janyo Hankali Masoya

100+ Sabbin Kalaman Soyayya Masu Janyo Hankali Masoya



Masoyiyata a bar kauna ta Kuma Abin alfahari na magana ta gaskiya inada burin inga na kasance tare dake a wannan nahiyar duniya, ko a wajen Kalmar sunanki ya tabbatar min dake macece wadda kowane Mutum yayi Kokarin Samun ta a rayuwa yayi babban dace. Babu shakka ban makara ba Domin tarko na ya Riga da ya kama ki kasancewar duka fadin inda kike Mu'amala dasu babu namiji guda dake iya Samun lokacin Da zaki iya waremai acikin dubban lokutanki masu Muhimmanci Domin wata tattaunawa dake bale ayi maganar so a Tsakaninku Dashi. Babu shakka ke kyakkyawar macece wadda duk namiji ya ganki yanason ya kasance tare dake amma kash! Ba kowane namiji ke iya jure fargabar tunkararki ba Duba Da irin kwarjininki idan Mutum ya kusanto a kusa dake zai ji tamkar ya isa wajen fadar shugaban kasa ya tarar da shugaban sojojin tsaro Kuma abunda ya kawo shi a wannan fadar ba komai bane face ayi masa iso ya gana da shugaban kasar Nigeria Wanda wannan Abin zaisa yaji bai iya jure wannan firgici Da faduwar gaba Domin bai San irin yadda zata kaya ba kamin shi Samu haduwa Da shugaban kasar Har su tattauna Dashi wannan zai Sa shi rashin nutsuwa tare Da rashin Samun sukuni aransa to ina mai tabbatar miki cewa kwarjininki Da kike Dashi tamkar wannan misalin ne Da na baki na haduwa da shugaban sojoji kamin isa fadar shugaban kasa.


Nayi mubaya'a acikin birnin zuciyar ki sannan na tabbatar Da banida wani karfi ko dabara wadda zata iya dakatar dani daga rage irin soyayyar da nake miki ballantana ace in daina sonki, To hakan na iya haifar Da wata cuta ta kamani wadda in za'a dauke ni akaini babbar asibitin garinmu bazan tashi ba, Kuma idan za'a dauke ni akaini asibiti karamar hukumar Mu to bazan tashi ba idan Kuma za'a kwasheni akaini babbar asibiti Jahar Mu bazan tashi ba. Baya ga haka ma idan za'a kwasheni akaini babbar asibitin kasarmu ga baki daya na tabbatar bazan tashi ba sai an kaini asibitin duniyar soyayya tare Da kauna da amana da yarjejeniyar rike juna da aminci Da alkawalin rike juna Da amana daga nan na tabbatar da Za'a Samu maganin waraka ta Duba Da yadda soyayyar ki da kauna da muradinki sukayi tasiri da galaba ajikina

0 Response to "100+ Sabbin Kalaman Soyayya Masu Janyo Hankali Masoya"

Post a Comment