100 Kalaman Soyayya Ga Budurwa
100 Kalaman Soyayya Ga Budurwa
Na kasa Samun dogon lokaci idan ina bacci kasancewar a kullun dake nake bacci haka Kuma dake nake tashi a rayuwa ta babu shakka ke Abin ayaba ce Domin kece makasudin duk wani farin ciki nawa dake wanzuwa a fadin kasar nan. Banida tamkar ki a zuciya ta ta fannin nunamin soyayya Da kauna tare Da amana da amincewar juna da kulawa a tsakanin Mu na Kuma Zamantakewar Mu.
Nayi ta sambatu a duk inda zanje banda wata diya mace mai irin saukar angulu tayimin dafifi a zuciyata face irin kyakkyawan fuskar nan taki Hadi Da tunanin ki ya abar yabo Da kaunata mace mai yawan annushuwa da sakewar fuska Abin biyan bukatar rayuwa a kullu yaumin musamma a lokacin Safiya da marece idan Mutum yayi yunkurin daukar gajiya irin wacce ke ajiyeshi a gida barjat ya habibiyata mai raya birni da karkarar zuciyata ta sanyaya kalbi na a matakin da babu wani namiji Wanda zai kaima babban matakin Da na taka na ribar rayuwa Da amanar juna Da nake akanki ya mashahuriya zukfatan ainihil mashinunin kalbi na.
Babin da na bude Domin fayyace soyayya ta a kalbinki ba karamin shiri nayi ba don inga na kare mutunci Da kauna dakuma amana da yarjejeniyar kaunar juna ta gaskiya ya kurratul aini na abar alfarina ruwan zumata Kuma agwalimar kaunar kirkirar raya ruhin rayuwata da sanadin girgizar farin cikin yanayin rayuwata da Kuma duk Wasu masun dake tare bugawar kirjina ta dalilin duk wani iftila'in so da hamayyar Rukunin tafarkin dake girgiza sanyin muradin zuciyata ya Abin sona da ambatona.
Babu shakka ta dalilin soyayyar da nake miki na hadu da wani farin ciki na duniya Wanda bai misaltuwa ya ke Bakadamisar karkatar da duk wata akala Da fannin Yankin yunkurin kasafin da zai iya riftawa ya ruguje ya rakube tattakar duk wani datti da kwarkwatar Da aka roshe Domin yima zuciya ta makusanciya mai amana da karamnci tare da nuna yaddar juna zuwa gareki ya ke ma'abociyar sarrafa idanuwana, ya ke bakin Dake furta kalmomin dake kara yaduwar so da shakuwa da amana a tafarkin kauna acikin kalbin zuciyata.
Na yadda dake Kuma soyayyyar da nake miki nafi son kidauki zare kibar duk wata auduga Domin akwai Wasu mata masu tamkar kaza idan sunci sai su manta, muryarki ta Kawaye ko ina ta fannin zaki idan kinyi musun haka sai kinemi yan Garin Mu su gaya miki hakan Domin da masu gari ake cin gari amma duk Wasu masu son suga sun rabamu bazasu taba Samun wannan damar ba Domin na Riga nayi musu rata ta kowane fanni acikin harabar birnin fadamar soyayyar gaskiya a fakaice a Kuma a bayyane
Na tabbatar da duk wani dandazon taron Da za'ayi dole sai kinbi kin haska wurinan ki haskaka wannan katafaren wurin. Kuma na tabbatar da kowane mace ta sami kanta a wurin taron Da kika hakarta na tabbatar da sai ta kasance Abin tausai Domin na tabbata Kuma inada yakinin babu wata rawa da zata taka kasancewar kina wannan wurin dole duk ki dambala duk wani lissafin duk wata mace mai ganin cewa tanada kyau na jiki ta fannin farin jiki, idanuwanki kamar madara, tsayin ki mai kama da dirin macen doki fatar ki mai lafiya kamar kadar auduga ya ke tauraruwar da idan dare ya tsala babu wata tauraruwar dake haske gari kamar ke ya gimbiyar duniyata mai takama da ikon Allah.
Yan mata miya faru miyafaru yau dai bakimin zance ba, Kuma duk Wanda ya tabaki idan Har kika nuna min shi to dole zaiga fushina Domin ke ka goyani kiyimin bambu dole ko in tarairayeki musha kauna Domin duniya labari ce idan Kaine yau takan yuyu Gobe bamu bane. Na zama surikin baba surikin mama Domin sune suka kawomin ke a duniya Domin Mu saita zaman lafiya da nuna soyayyata zuwa gareki ya a bar gwada muwafakata Domin sakin fuskat kalbina.
Na sunkuyadda kaina tare da rike tunani na Domin gurfanar da duk wata niimar dausayin lausasa harshe na don ganin yadda zan fara fafutika ta Bangaren soyayyar ki Da amana dakuma kaunar juna tare da yarjejeniyar bazan taba cutar dakeba dakuma alkawalin kasancewa a tare dake muna kaunar juna a bisa amana da tallar juna
0 Response to "100 Kalaman Soyayya Ga Budurwa"
Post a Comment