100+ Kalaman Soyayya 2025
100+ Kalaman Soyayya 2025
Ya masoyiyata ki rike mini alkawalin da nabaki Domin dake zanyi cikon burina sabida haka ki rikemin amana a rayuwa Domin na Riga nayi Mutum dake, Ashe dake acikin tarihina da labari zani baki Domin kauna magaucinmu bansan lokacin Da zaiyi nasara ba Domin bazamu taba bashi dama ba kidaina tunanin wani zai iya kutsawa shiyi tasiri cikin alakar mu. Kizo Mu doshi lambu kauna muje daki a tare dake Domin Samun tattaunawa Domin kauna da amincewar juna da yake akwai maganganu wadanda ya kamata Mu tattauna na soyayya tsakanina dake Domin na yadda dake masoyiyar gaske ce ki rikemin alkawali Domin raina Da jikina duka ya Riga ya kasance naki yake masoyiyata kin zama aminiyar rayuwa ta. Tun ranar da sonki ya sarkafe zuciyata lalle na tabbatar da zafin dafin so na ratsa zuciya mai gaddamar haka zai gane amma idan ya taka matakin soyayya da mace mai burge kowa irinki Domin ke na kama ki yadda da burina na zama a kusa dake zo rabi raina muradina kada kiyi watsi dani.
Kin zamo babban burina Kuma ke kadai zan Adana acikin zuciyata Kuma ko a ina zan iya bayyana haka sabida kece Rabin raina Kuma muradina ya abokiyar rayuwata masoyiyata Abin alfahari na. Dawo dawo haba masoyiyata mi zaisa nabaki rata. Idan akace akwai jini da fata na tabbatar da babu ranar Da kauna zatayi rata duk Tsakani kada Mu yada juna ke ce tauraruwa ta mata wadda ke haska kowane diya mace kaunar da nake miki bata da karshe Kuma alkawali Yanada rana Kuma ki tabbatar da mai shi baza shi fadi kasa ba idan Kuma munyi biris da haka na tabbatar da ruwan soyayya ba zasu ratsa muba ni nazo ne da maganat aure buri na ki Isar da magana ta duk Da na San akwai masu Sara da shuka acikin wannan Tafiyar ta soyayyar Mu. Alkawalinmu dake ki rike kada kiyi wasa ki sake soyayya ta ta hadamu Domin rabuwar Mu akwai wahala.
Ya ke masoyiyata alkawali ki rike da gaske sonki nake kiji bada wai ba. Daga nesa na fara kula ki jininki ya bayyana a idon alumna na tabbatar da idan akwai rayuwa wata rana zamuyi aure ni dake Mu isa a dakinmu ba Domin Mu gudanar da soyayyar Mu tare da kauna soyayya ce ta hadamu na tabbatar da baa rabamu Domin shi so baida farashi da za'a tayashi ke na Riga na zaba Domin muyo rayuwa a tare don kyawun ki na kallafa ma rayuwata dole sai dake Domin ke kamar rayuwa ta ce ke yarinya ce mai farin jini mai kyau da siffar fuska gaki tafiya kike amma kowa kallo yake yana shauki maisona zo ki rike hannuna juyo ki kalle ni kiyimin kalma ta soyayya Kuma mai dadi wada baa taba yin irinta ba ke kyakkyawan mace ce wadda na jima ina jiran irinta Domin muyi soyayya.
Ga sako aje mini ni zani tafi nayi rubutu ga dawwada soyayya ki rika mini babu laifin da kike mini tarkon ki ya Riga ya rikeni soyayyar ki farin ciki take sakani ta koremin bakin ciki kin Kore farin tufa kin sanya ina ta tsuma murya ta tanai miki kyakkyawan fata ba kowane mace a zuciyata Domin soyayyar zuciyata ke kadai ta rika lalle karshen so idan yazo za'a ji wuya. Da ganinki sai naji na kamu da sonki soyayyar ki ta daban ce acikin zuciyata ke ta musammman ce na rantse ya habibiyata da ace zaki soni lalle zaki gane ke ta musammam ce irin yadda soyayyar ki ta ratsa jini na da fata na Riga na tsaya akanki Domin na San baa yimin kwace kasancewar ke macece mai alkawali. Naga banda dabara sai Abinda Allah ya tsara amma tunanina duka yana kanki. Kinsa min yaggiyar so akan haka sai na zautu idan haka nasso a baya lalle a soyayya da ban moreba da ganki na juya naji kinaimin sallama zakin muryar ki yasa na koma gefe inajin sauti mai ratsa zuciya Domin na kasa fahimtar zancenki. Lalle za'ayi min Kuka Kuma ayimin jaje Domin idan na rasaki a kusa dani sabida na Riga na Gayama yan uwana cewa idan na rayu ba dake ba bazan Samu kai lokacin mutuwana ba sai na bar wannan duniya
Soyayyar ki tilas ne akanki ko gasa aka Dora nine zan zama a sahun farko Domin shigar wannan gasar Domin banida wani buri a rayuwa face inganki a gidana Domin kowa zaifi son ganin sarauniya irinki Acikin gidanshi sannan zanyi yaki Da kowa mai son kusanto ki babu dalilin da zaisa inga ranar da zata sa na rabu dake Domin na Riga na kamu da kaunar ki a rayuwa.
Bari kiji kece karfin ganin idona dani dake ba zancen yin fada da juna, kinada kyau musamman idan kin saka hijabi saida ke na tabbatar da zan tsaida lamura na naki ne ni koda acikin damana da rani. In rabu dake Sam ni bazan iyaba. Murmushin fuskar ki ta isarda komi acikin zuciyata, ke ta daban ce acikin birnin zuciyata kibani dama in bude zuciyata sabida idan ban Samu amincewar ki ba zan shiga wani hali na garari.
Ya ke yar Fulani ke nakeso sonki ba dai shiyi iyaka acikin zuciyata ba Domin hakan kuskure ne a soyayyar da nake miki. Na Riga nayi Tafiyar da banso ko waiwaye inyo gameda soyayyar ki kin zama tamkar fadama Da karamar ruwan dake ratsa geben Da zai kwaso jinin jikina ya shiga ta jijiya ya isar Da sakon zuciya ta ta fannin kauna da kulawar juna yake fadamar dake sanyaya zuciyata da kalbina a fili da boye. Kin zamo mai niyyar rikon gaskiya a soyayyar Mu
0 Response to "100+ Kalaman Soyayya 2025"
Post a Comment