Shirin Tallafin Keke Napep Masu Amfani da Iskar Gas (CNG) Domin Matasa a Najeriya
Shirin Tallafin Keke Napep Masu Amfani da Iskar Gas (CNG) Domin Matasa a Najeriya
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin rabon kekuna masu amfani da iskar gas guda 2,000 domin tallafawa matasan Najeriya su shiga harkar sufuri mai tsada. Wannan shiri na musamman, wanda aka fi sani da Presidential CNG Initiative (Pi-CNG), na nufin rage radadin tsadar sufuri tare da bunkasa tattalin arzikin kasa ta hanyar samar da ayyukan yi da kuma amfani da makamashi mai tsafta wanda ba ya gurbata muhalli.
Shirin ya kunshi rabon kekunan napep masu amfani da iskar gas ga matasa domin su samu damar gudanar da harkokin sufuri cikin sauki da kuma araha. Wannan mataki yana da nufin rage yawan kudin sufuri, bunkasa kasuwanci, da kuma samar da hanyoyin dogaro da kai ga matasa a fadin Najeriya.
Matasan da za su ci gajiyar wannan shiri za su fara da samun horo na musamman kan yadda ake gudanar da kekunan CNG da kuma kula da su. Bayan wannan horo, za a hada su da masu tarawa (aggregators), wadanda za su taimaka wajen saita tsarin mallakar kekunan ta yadda kowanne mahalarta shirin zai samu cikakken mallaka idan aka cika sharuddan da aka gindaya.
Abubuwan Da Shirin Ke Nufa
- Rage Tsadar Sufuri: Samar da wani tsari na sufuri wanda zai rage radadin tsadar sufuri ga jama’a ta hanyar amfani da CNG.
- Kara Yawan Kekuna a Tituna: Kara yawan kekunan CNG a fadin Najeriya domin kara saukaka sufuri.
- Jawo Jari: Kawo masu zuba jari cikin harkar CNG da kuma bunkasa tsare-tsaren ci gaba mai dorewa a bangaren sufuri.
- Samar da Ayyukan Yi: Samar da dama ga matasa su samu sana'ar sufuri da zai inganta rayuwarsu.
- Kare Muhalli: Inganta muhalli ta hanyar rage hayaki da sauran gurbatattun abubuwa daga tsoffin kekunan mai.
Yadda Zaku Cike
Wannan tsari zai bai wa matasa damar shiga harkokin kasuwanci da kuma samun hanyar dogaro da kai cikin gaggawa. Duk wani matashi mai sha’awar shiga wannan shiri zai iya yin rajista ta tashar yanar gizo ta
domin samun cikakkun bayanai kan yadda za a shiga tsarin. Tashar ta kasance hanya mai sauki ga matasa su yi rijistar shiga shirin kuma su samu damar mallakar kekuna cikin sauki da tsari mai kyau. Hakan zai taimaka wajen samar da sana’o’in dogaro da kai da kuma rage radadin rashin aikin yi a tsakanin matasa a fadin Najeriya.
Ta wannan shiri, ana sa ran inganta tsarin sufuri tare da samar da wata hanyar samun kudin shiga ga matasa, sannan a lokaci guda a rage tasirin gurbatar muhalli ta hanyar amfani da iskar gas mai tsafta fiye da man fetur.
Allah yasa mu dace baki daya
0 Response to "Shirin Tallafin Keke Napep Masu Amfani da Iskar Gas (CNG) Domin Matasa a Najeriya"
Post a Comment