-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Sanarwa ga masu sha’awar neman aiki a kamfanin Dangote Sinotruk West Africa Limited

Sanarwa ga masu sha’awar neman aiki a kamfanin Dangote Sinotruk West Africa Limited

Sanarwa ga masu sha’awar neman aiki a kamfanin Dangote Sinotruk West Africa Limited

Sanarwa ga masu sha’awar neman aiki a kamfanin Dangote Sinotruk West Africa Limited. Kamfanin ya sanar da aniyar sake bude bangarorin ayyukansa kuma yana neman ma’aikata a mukamai daban-daban. Wadannan mukamai sun hada da: 

- Kwararrun Masu Gyaran Injinan Mota (Mechanical Technicians)

- Kwararrun Masu Gyaran Wutar Lantarki (Electrical Technicians)

- Injiniyoyin Injinan Mota (Mechanical Engineers)

- Injiniyoyin Wutar Lantarki (Electrical Engineers)

- Injiniyoyin Kayayyaki (Instrumentation Engineers)

- Shugabannin Layin Tara Motoci (Assembly Line Supervisors)

Hakazalika, akwai bukatar ma’aikata a wasu sassan kamfanin kamar: 

- Gudanar da Ma’aikata (Human Asset Management)

- Gudanar da Kayayyaki (Inventory Management)

- Talla da Kasuwanci (Sales & Marketing Management)

- Sabis ga Abokan Hulda (Customer Service)

- Gudanar da Kudi (Finance Management)

- Kula da Inganci da Tabbatar da Ayyuka (Quality Control and Assurance)

Masu sha’awar neman aiki su tura takardun neman aikin su, cikakken CV da shaidunsu zuwa ga:

The Head (Human Asset Management), Dangote Sinotruk West Africa Limited, 3, Oba Akran Avenue, Ikeja, Lagos.

Hakanan za a iya aika takardun neman aikin ta hanyar imel zuwa: hr.sinotruk@dangoteprojects.com

Ana maraba da duk masu sha’awa su gabatar da takardun neman aikin su cikin kwanaki bakwai (7) daga ranar da aka fitar da wannan sanarwa.

5 Responses to "Sanarwa ga masu sha’awar neman aiki a kamfanin Dangote Sinotruk West Africa Limited"