-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda ake tuwon masara

Yadda ake tuwon masara

Yadda ake tuwon masara

Kayan hadi

Masara

Da farko zaa surfa masara idan aka surfa sai a wanke ta domin cire wannan dussa dake jikinta sai a jika masarar for like 3hours haka kuma zaa iya bari ta kwana a jike .

Idan ta jika sa a tsane ruwan aje a markada a inji daga nan sai  azo a tankade garin masarar sai a Dora ruwa a tukunya su tafasa sannan azo a debi kadan dafa cikin garin a sa mishi ruwa kadan ayi talge  wannan talgen shi zaa zuba a cikin tafasashen ruwan zafin idan talgen ya fara tafasa sai a dauko sauran garin kadan kadan ana zubawa a tukunya har ya hade jikinsa sai a rufe tukunyar tuwon ya turara for 10 minutes sai a sauke a zuba a mazubi.  Aci dadi lafiya

0 Response to "Yadda ake tuwon masara"

Post a Comment