Yadda ake Tuwon Dawa
Wednesday, September 11, 2024
Comment
Yadda ake Tuwon Dawa
Nikeken garin dawa
Kanwa
Ruwa
Yanda ake hadawa
Da farko zaa dora tukunyarki a wuta sai a sa ruwa daidai misali
Idan ya tafasa sai a debo garin dawa da aka tankade a sa ruwa sai a dama shi a zuba a kan tafasasshen ruwan.
Sai a saka mucciya a juya don kar ya yi gudaje. Sai a kawo ruwan kanwa kadan a zuba a barshi yayi ta dahuwa.
Idan yayi sai a tuka zaaga har yauki yake yi. Idan an kare tukawa sai a rufe ya dan turara, zaa ji yana kamshi sai ki sauke ayi malmala malmala.aci lafiya.
0 Response to "Yadda ake Tuwon Dawa"
Post a Comment